Waɗanne ƙasashe ne ke samar wa Rasha makamai a yaƙin Ukraine?

Iranian Shahed-136 drone in flight

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jirgin Shahed-136 maras matuƙi na Iran
    • Marubuci, Jeremy Howell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 6

Rasha na harba miliyoyin makamai duk shekara zuwa Ukraine, sannan tana kai hare-hare ta sama a akai-akai kan wuraren farar hula - galibi da makaman da ake cewa wasu ƙawayenta ne ke ba ta.

Yayin da ƙasashen Yamma ke ƙoƙarin rage ƙarfin Rasha na ƙera makamai ta hanyar ƙaƙaba mata takunkumai, China da Iran da Koriya ta Arewa suna taimaka mata ta bayan fage kamar yadda ake zargi.

Makami maras matuƙi da masu linzami daga Iran

A baya-bayan nan, an zargi Iran da ƙulla yarjejeniya da Rasha ta samar mata da makamai masu cin gajeran zango - kilomita 200 ko fiye.

Makaman da aka kira Fath-360, na iya tafiyar kilomita 120 kuma suna da ƙarfin ɗaukan abubuwan fashewa masu nauyin kilo 150.

Hukumar leƙen asirin Amurka ta ce sojojin Rasha da dama sun samu horo a Iran game da yadda za su harba makaman. Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya ce ana iya harba makaman kan Ukraine nan gaba.

Makaman ƙirar Fath-360 za su taimaka wa Rasha ta kai hare-hare kan biranen Ukraine da kuma cibiyoyin lantarki da ke kusa da iyakokinta, abin da zai bai wa makamai masu cin dogon zango damar nausawa cikin ƙasar.

"Makaman Fath-360 na da kyau wajen kai hari a wuri da ke kusa," in ji Dakta Marina Miron ta sashen nazarin harkar yaƙi a kwalejin Kings da ke London. "Rasha ba ta da makamancin makamin na karon kanta."

A ɓangarenta, Rasha na iya bai wa Iran fasahar ƙera makaman soji, wataƙila har da fasahar ƙera nukiliya, in ji ta.

Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus sun ƙaƙaba sabbin takunkumai kan Iran saboda samar wa Rasha makamai.

Takunkuman sun hada da haramta jiragen Iran zuwa Birtaniya da Turai har da haramcin tafiye-tafiye da kuma ƙwace dukiyar wasu Iraniyawa da ake tunanin suna da hannu a yarjejeniyar.

Iran dai ta sha musanta bai wa Rasha makamai.

Gwamnatin Ukraine da hukumomin leƙen asirin ƙasashen yamma suma sun ce Iran ta daɗe tana samar wa Rasha makamai ƙirar Shahed-136 tun 2022.

Sojojin Rasha suna tura da yawansu a ƙoƙarin samun galaba kan Ukraine. Ana amfani da irin jiragen marasa matuƙi domin hana Ukraine daƙile harin makami mai linzami da ke ya fi daukan abubuwan fashewa kuma yake iya yin ɓarna sosai.

Gwamnatin Iran ta ce ta bai wa Rasha jirage mas matuƙi ƙalilan ne kafin soma yaƙin.

Sai dai Amurka da Tarayyar Turai sun zargi Iran da tura makamai zuwa Rasha sannan EU ta ƙaƙaba takunkumai kan mutane da kuma kamfanonin da ke da hannu.

A cat perches in the wreckage of a Shahed drone shot down by Ukrainian air defences in a residential area of Kharkiv

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi amfani da jirage marasa matuƙa ƙirar Shahed wajen kai hari kan gidajen Ukraine

Makamai da rokoki daga Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa, a cewar rahotanni ta tura wa Rasha miliyoyin makaman atilare domin yaƙar Ukraine

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Koriya ta Arewa, a cewar rahotanni ta tura wa Rasha miliyoyin makaman atilare domin yaƙar Ukraine
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A rahotonta na Mayun 2024, hukumar leƙen asiri ta Amurka ta ce Koriya ta Arewa ta tura wa Rasha da miliyoyin rokoki.

Makaman artilari shi ne muhimmin makamin da duka ɓangarorin biyu ke amfani da shi a fagen dagar Ukraine. Yana kare hare-haren maƙiya daga yin tasiri.

Cibiyar nazarin tsaro a Birtaniya, Rusi ta ce a watannin baya-bayan nan sojojin Rasha sun samu nasara fiye da Ukraine a yawan makaman da suke da shi na harbawa.

Rusi ta ce wannan ne babban dalilin da ya sa Rasha ta ƙwace iko da yankuna da dama a gabashin Ukraine tun 2023.

A Janairun 2024, jami'an leƙen asirin Ukraine sun ce sun gano tarkacen wasu makamai masu cin gajeren zango nau'i biyu waɗanda Koriya ta Arewa ta ƙera kuma aka yi amfani da su wajen kai hari kan Kharkiv.

Hukumomin Ukraine sun ce a cikin makaman akwai ƙirar Hwasong-11 da ake kira KN-23.

Wannan makami mai cin gajeren zango ne da ke iya kai wa kilomita 400 da 690 kuma yake iya ɗaukan ɓangarorin makamai masu nauyin kilo 500.

Tun 2006 ne kuma Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaƙaba wa Koriya ta Arewa takunkumi kan harkokinta na kasuwanci da suka shafi makamai masu cin gajeren zango.

Hukumar leƙen asirin Ukraine ta ce Koriya ta Arewa ta tura makamai 50 zuwa Rasha kuma a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da aka yi Fabarairun 2024, Amurka ta zargi Rasha da yin amfani da makaman Koriya ta Arewa a aƙalla hare-hare tara da ta kai a Ukraine.

Tarkacen makami mai linzami a Kharkiv da hukumar leƙen asirin Ukraine ta ce makamin Koriya ta Arewa ne ƙirar Hwasong-11

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tarkacen makami mai linzami a Kharkiv da hukumar leƙen asirin Ukraine ta ce makamin Koriya ta Arewa ne ƙirar Hwasong-11

Hukumar leƙen asiri ta Amurka ta ce Rasha da Koriya ta Arewa sun fara cinikin makamai a 2022 kuma makaman farko an tura su Koriya ta Arewa zuwa Rasha a 2023 domin gwada su.

Ta ce Rasha ta soma amfani da makaman wajen kai hari kan Ukraine a Janairun 2024 daga tsallaken iyaka.

"Makaman Hwasong-11 sun fi arha ga Rasha wajen amfani da su a maimakon makamai masu cin ƙaramin zango kamar Iskander," in ji Dakta Milton. "Batu ne na lissafi.

"Haka nan ƙulla yarjejeniyar makamai da ƙasashe kamar Iran da Koriya ta Arewa ya nuna wa ƙasashen yamma cewa Rasha na da ƙawaye, kuma ba ita kaɗai ba ce."

Makamai irin su Hwasong-11 na da wuyar daƙilewa saboda gudunsu wajen isa inda aka tura su. Sai dai jami'an leƙen asirin Ukraine a cewar rahotanni sun ce akasarin jiragen daga Koriya ta Arewa sun gaza kai wa inda aka harba su saboda tangarɗar da suka fuskanta.

Koriya ta Arewa ta musanta tura wa Rasha makamai sannan ita ma Rashar ta musanta karɓar makami.

Jami'an leƙen asirin na Ukraine a cewar rahotanni sun hango sojojin Koriya ta Arewa tare da takwarorinsu na Rasha a kasar. Jaridun Ukraine sun ruwaito suna cewa a ranar 3 ga Oktoban 2024 ne aka kashe jami'an Koriya ta Arewa, uku kuma suka ji rauni a wani harin makami mai linzami na Rasha da ya faɗa kan sansanin horo a gabashin Ukraine.

Zarge-zargen sojojin Koriya ta Arewa a baya na cewa suna yaƙi a Ukraine an yi sune a 2023 kuma shugaban Rasha, Vladmir Putin ya ƙaryata.

China da kayan fasahar ƙera makamai

Shugabannin ƙasashen Nato sun zargi China da zama babbar mai bai wa Rasha tallafin tsaro.

Sun ce China na samar wa Ukraine wasu kayayyakin fasaha da ake iya amfani da su wajen ƙera makamai.

Nato ta ce ana amfani da na'urorin China sosai a Rasha wajen ƙera makamai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nato ta ce ana amfani da na'urorin China sosai a Rasha wajen ƙera makamai

Cibiyar nazarin tsaro ta CEIP ta ce a kowane wata China tana tura wa Rasha dala miliyan 300 na fasashohin da ke da amfani biyu da za a iya ƙera makamai da su kamar jirgi mara matuƙi da makamai masu linzami da kuma tankokin yaƙi.

Ta ce China tana sayar wa Rasha kashi 70 cikin 100 na dukkan kayan da ake iya amfani da su wajen ƙera murafan makamai da kashi 90 cikin 100 na kayayyakin da ake iya amfani da su don taimaka wa makaman su dira a inda aka harba.

CEIP ta ce a 2023, Rasha ta shigo da kashi 89 cikin 100 na kaya masu amfani biyu daga China. Ta ce kafin soma yaƙin., Jamus da Netherlands ne suka samar da galibinsu. Da aka ƙaƙaba takunkumi da ya shafi shigar da kayansu Rasha, sai China ta cike giɓin.

China ta musanta taimakon Rasha wajen ƙera makamai inda ta ce ita ta kasance ƴar baruwanta a yaƙin na Ukraine. Ta ce ba ta samar da wani makami ga Rasha ba sannan ta kasance mai taka tsan-tsan a kayan da take sayar wa Rasha.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce Rasha ta kafa masana'anta a China domin ƙera wani sabon jirgi mara matuƙi mai tafiyar dogon zango ƙirar Garpiya-3.

Gwamnatin China ta ce ba ta da masaniya game da hakan kuma tana da tsauraran dokoki game da fitar da jirage mara matuƙi zuwa wasu ƙasashen, in ji Reuters.