Tambayoyin da har yanzu ba a san amsarsu ba game da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Asalin hoton, Anadolu / Getty Images
Isra'ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan shafe wata 15 ana gwabza faɗa a Gaza.
Firaiministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdul Rahman Al Thani ya ce yarjejeniyar za ta fara aiki ne a ranar L;ahadi, matuƙar ta samu amincewar majalisar zartaswar Isra'ila.
An cimma wannan matsaya ce bayan watanni da dama da aka kwashe ana tattaunawa sanadiyyar rashin yarda da juna tsakanin Hamas da Isra'ila.

Asalin hoton, Mohammed Saber / EPA
Tun farko Hamas ta buƙaci dole a kawo ƙarshen yaƙin kafin ta saki ƴan Isra'ila da take garkuwa da su, sai dai Isra'ila ba za ta amince da hakan ba.
Yarjejeniyar ta ƙunshi batun tsagaita wuta, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan sauran batutuwa.
Sai dai abin da babu tabbas shi ne ko hakan zai kawo ƙarshen yaƙin, domin kowa ya huta.
Ɗaya daga cikin alwashin da Isra'ila ta sha game da yaƙin shi ne lalata ƙarfin soji da na jagorancin ƙungiyar Hamas.
Duk da cewa Isra'ila ta yi wa Hamas gagarumar illa, har yanzu Hamas na da sauran ƙarfin sake curewa da ci gaba da ayyukanta.
Sakin waɗanda ake garkuwa da su da kuma fursunoni

Asalin hoton, EPA
Babu tabbas kan yawan sauran waɗanda ake garkuwa da su da suke raye a yanzu, da kuma waɗanda suka mutu, haka nan babu tabbas ko Hamas na da masaniya kan inda sauran mutanen da ba a san halin da suke ciki ba suke.
A ɗaya ɓangaren, akwai wasu fursunoni da Hamas ta buƙaci Isra'ila ta saki amma Isra'ilar ta ce ba za ta sake su ba.
An haƙiƙance cewa mutanen da Isra'ila ta ce ba za ta saki ba su ne waɗanda ke da hannu a harin da ƙungiyar ta kai na ranar 7 ga watan Oktoba.
Haka nan babu tabbas ko Isra'ila za ta amince ta janye daga wurare masu muhimmanci wurin hana kai mata hari da ta jibge dakarunta, a lokacin da aka ayyana.

Asalin hoton, Bashar Taleb / AFP / Getty Images
Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin biyu ba ta da tabbas.
Yarjeniyoyin tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Isra'ila da Hamas a baya sun samu cikas sanadiyyar rikice-rikice, waɗanda daga baya kan wargaje.
Sarƙaƙiya da kuma lokutan da aka tsara na aiwatar da wannan yarjejeniya na nuna cewa duk wani rashin jituwa, komai ƙanƙantarsa zai iya zama barazana ga zaman lafiyar.

Asalin hoton, Mahmoud Issa / Reuters
Ko Trump zai iya samun yabo kan yarjejeniyar?

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya yi iƙirarin cin nasara kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas. A cewarsa, ''cimma yarjejeniyar tsagaita wutar mai muhimmanci ya faru ne sakamakon nasarar da muka yi mai cike da tarihi a watan Nuwamba.''
A birnin Doha, firaministan Qatar Sheikh Mohammed Bin Abdulrahman al-Thani ya amsa tambayoyi daga manema labarai bayan sanar da yarjejeniyar.
Tambaya ta farko ita ce me yasa sai a yanzu aka cimma yarjejeniyar, kuma shin matsi ne daga shugaban Amurka mai jiran gado ta sa aka cimma yarjejeniyar.
Al Thani ya ce Qatar ta fuskanci wasu abubuwa da suka faru a watannin baya-bayan nan.
''Mun ga matakai da Amurka ke ɗauka a baya-bayan nan da suka taimaka wajen kaiwa ga wannan lokaci,'' in ji shi.
Ya ƙara da cewa abin da suka gani daga Amurka a baya-bayan nan haɗin gwiwa ne da ya zarce na gwamnatocin biyu, wanda ya bayyana a matsayin sadaukarwa domin cimma yarjejeniya.
Ta yaya za a aiwatar da yarjejeniyar?

Asalin hoton, Getty Images
Akwai buƙatar majalisar tsaron Isra'ila ta amince da yarjejeniyar ta hanyar kaɗa ƙuri'a, duk da ƙalubalantar matakin da wasu ministoci na ɓangaren gwamnati masu tsattsauran ra'ayi ke yi.
A yayin jawabi ga manema labarai, an tambayi Firministan Qatar din kan irin tabbaci ko yaƙinin da yake da shi cewa yarjejeniyar za ta yi nasara har a wuce mataki na farko.
Ya ce suna da yaƙini kan hakan kuma nasarar ta ta'allaƙa ne kan ɓangarorin biyu.
Da aka tambaye shi kan matakan da aka sanya domin tabbatar da ɓangarorin biyu sun bi sharuɗɗan yarjejeniyar, ya ce ƙasashe uku - Amurka, Masar da Qatar- za su sanya ido kan aiwatar da yarjejeniyar.
''Muna sa ran ɓangarorin biyu za su bi ƙa'idojin yarjejeniyar,'' in ji shi, sai dai ya kuma yi la'akari da cewa irin waɗannan yarjeniyoyin suna da sarƙaƙiya.
Wane ne zai mulki Gaza?

Asalin hoton, Reuters
Ko wane ɓangare ne zai jagoranci Gaza bayan yaƙin?
Wannan tambaya ta kasance ɗaya daga cikin manyan tambayoyin da ba a amsa su ba.
Dole ne hukumomin Falasɗinawa (Palestinian Authority PA) su zama su kaɗai ne gwamnatin da ke da iko a Gaza bayan yaƙin, in ji Firaministan Falasɗinawa, Mohammad Mustafa a ranar Laraba, gabanin sanar da yarjejeniyar tsagaita wutar.
Isra'ila ta ƙi amincewa da barin Hamas ta cigaba da iko da yankin. Ta kuma ƙi amincewa ta bar Gaza ƙarƙashin jagorancin PA, wadda ke jagorantar wani ɓangare na yankunan da Isra'ila ta mamaye a Gaɓar yamma da kogin Jordan.
Kuma Isra'ila na so ta cigaba da yin iko kan tsaron Gaza bayan yaƙin ya kawo ƙarshe.
Sai dai tana aiki tare da Amurka da kuma Haɗaɗɗiyar daular Larabawa domin shirya tsarin samar da gwamnatin riƙon ƙwarya da za ta jagoranci Gaza a yayin da ake sauye-sauye a PA.
Daga nan sai sabuwar gwamnatin ta amshi ragamar mulkin a matsayin gwamnatin dindindin.










