Hanya ɗaya da Arsenal za ta iya cin Premier

d

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Lahadi za ta zama rana ta karshe da za a rufe wasu daga cikin gasannin nahiyar Turai da wasu sassan duniya.

Tuni a wasa gasannin aka samu wadanda suka lashe su, kamar Bundesliga da La Liga da Serie A.

Amma Premier Ingila har yanzu akwai sauran runa a kaba, domin kuwa wasan da ya rage shi ne zai bayyana gwarzon gasar tsakanin Pep Guardiola da Arteta.

A yanzu haka teburin gasar ya nuna Manchester City ce ke jagorantar Premier da maki 88 tazarar maki biyu tsakaninta da Arsenal.

Arsenal na mataki na biyu da maki 86, kuma ta zarce Man City da kwallo guda, inda take da 61 ita kuma City na da 60.

Manchester City na da wasa da West Ham, yayin da Arsenal za ta fafata da Everton.

Wacce dama ko wacce kungiya ke da ita ta lashe wannan gasar.

Hakan ya sa BBC ta yi dalla-dalla kan ko wanne yanayi da za a iya tsintar kai a ranar Lahadi ga masu karatu domin su gane.

Idan Arsenal ta ci wasanta ita ma City ta ci nata, City ta ci Premier kenan da tazarar maki biyu.

Idan aka yi janjaras da City da West Ham da za su yi fafatarwar karshe, Arsenal ta ci to maki yazo ɗaya amma kwallaye ne za su raba.

Idan aka ci City Arsenal ta ci nata wasan to Arsenal ta zama gwarzuwar gasar Premier 2023/2024.

Idan kuwa aka ci Arsnal, City ta ci Premier. Ka zalika City za ta iya cin Premier da Arsenal ta yi canjaras.

A don haka yanayi guda Arsenal ke fatan gani a ranar Lahadi, a ci Man City ita kuma ta ci.

Wani abu mai kamar wuya inji masu iya magana.

Sai dai Hausawa na cewa ba a san maci tuwo ba sai miya ta karae.