Waiwaye: Janye yakin aikin ASUU, korar karar Nnamdi Kanu da soke takarar Binani

Asalin hoton, others
A karshen mako ne kungiyar malaman jami'a ta Najeriya, ASUU ta sanar da janye yajin aikin da mambobinta suka shafe wata takwas suna yi.
Dokta Chris Piwuna, mataimakin shugaban kungiyar ta ASUU ya tabbatar wa BBC labarin, inda ya ce an janye yajin aikin ne da sanyin safiyar Juma'a, bayan da shugabannin kungiyar suka gana jiya da daddare a Abuja babban birnin kasar.
Kazalika a sanarwar da shugaban ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke ya sanya wa hannu, ya ce sun janye yajin aikin ne duk da yake "ba a warware batutuwan da ake jayayya a kansu ba."
Kotun daukaka ƙara ta kori ƙarar gwamnatin Najeriya a kan Nnamdi Kanu

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Alhamis ne kuma Kotun daukaka ƙara ta Najeriya ta kori ƙarar gwamnati tarayya a kan jagoran ƙungiyar ƴan aware ta IPOB Nnamdi Kanu, ta hanyar yin watsi da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Tawagar alkalan ta mutum uku da Mai Shari'a Jummai Hanatu ta jagoranta ta ce Kanu ba shi da laifin amsawa saboda tun farko Babbar Kotu ba ta da hurumin yi masa shari'a tun farko.
Hukuncin kotun ya ce matakin kamo Kanu da aka yi da dawo da shi Najeriya daga Kenya ya kauce wa doka.
Sai dai a sanarwar da ofishin ministan shari’a na ƙasar ya fitar ta ce kotun ta yi watsi ne da ƙarar kawai, amma ba ta wanke shi daga laifukan da ake tuhumarsa ba.
Sannan kuma gwamnatin Najeriya ta ce tana duba hukuncin da kotu ta yanke na yin watsi da ƙarar da gwamnati ta shigar kan shugaban kungiyar IPOB, mai rajin ƴantar da yankin Biafra.
Gwamnatin Zamfara ta garƙame ƙananan hukumomi uku

Asalin hoton, TWITTER/@BELLOMATAWALLE
Sannan kuma a cikin makon da muke bankwana da shi din ne kuma gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta ɗauki matakin dakatar da kowace irin hada-hada a wasu yankunanta da ke fama da matsalar tsaro.
A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a ranar Juma’a, ta ce ta lura da yadda ake samun taɓarɓarewar tsaro ta hanyar sace-sacen al'umma a kauyuka da kuma kan wasu hanyoyin jihar.
A saboda haka sanarwar ta ce gwamnati ta kulle, ɗungurungum, ƙananan hukumomin Anka da Bukuyum da kuma Gummi.
Kotu ta soke zaɓen Aisha Binani

Asalin hoton, FACEBOOK/AISHA BINANI
Haka kuma a ranar Juma'ar da ta gabata ne babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Yola ta soke zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Adamawa, wanda Sanata A'isha Binani ta lashe.
Kotun ta ce zaɓen ya zama haramtacce saboda aringizon ƙuri’a da kuma kawo wakilai daga ƙaramar hukumar Lamurde, inda ba a gudanar da zaɓen cikin gida na jam’iyyar ba.
Jiragen yakin Najeriya sun kashe rikakken mai garkuwa da mutane Ali Dogo da yaransa

Asalin hoton, NIGERIAN AIRFORCE
Haka kuma a dai makon da muke bankwana da shi din ne rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana yadda jiragen yakinta suka yi luguden wuta kan rikakken mai garkuwa da mutanen nan Ali Dogo wanda aka fi sani da Yellow da wasu yaransa a Jihar Kaduna da ke arewacin kasar.
Air Commodore Gabkwet ya ce bayanan sirrin da suka samu sun nuna cewa Ali Dogo da yaransa sun taru a gidan wani fitaccen mutum da ke karamar hukumar Giwa a Jihar Kaduna domin kitsa yadda za su kai hare-haren ta'addanci da garkuwa da mutane a karshen makon jiya.










