Uzbekistan ta alakanta mutuwar wasu yara da shan maganin tari na Indiya

Hotunan wakilai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Indiya ce ke samar da kashi uku na magungunan da ake amfani da su a duniya

Ma'aikatar lafiya a Uzbekistan, ta ce yara 18 ne suka mutu bayan sun sha maganin tari na ruwa da kamfanin Marion Biotech na Indiya ya ke samarwa.

Ma'aikatar ta ce gwajin farko da aka yi ya nuna maganin na dauke da sinadarin ethylene glycol, da ke janyo shidewa. An bai wa yaran maganin tari na ruwa samfurin Dok-1 Max syrup ba tare da izinin likita ba.

Sannan adadin maganin da aka bai wa yaran ya wuce ka'idar da ta dace.

Zargin na Uzbekistan na zuwa ne makonni bayan gwamnatin Gambia ta yi irin wannan zargin bayan mutuwar yara da dama da suka sha maganin tari na wani kamfanin Indiya.

Ma'aikatar lafiya ta Indiya ta fitar da sanarwa a hukumance, tare da nanata cewa jami'anta na tattaunawa da hukumar da ke sa ido kan ingancin magunguna ta Uzbekistan kan batun tun 27 ga watan Disamba.

Ta kara da cewa, jami'an lafiya na tuntuba da bincike a kamfanin Marion Biotech da ke Noida a jihar Uttar Pradesh.

"An dauki samfurin maganin tarin daga kamfanin da aka samar da shi, an tura dakin gwaji da ke Chandigarh domin a yi gwajin kwakwaf kan maganin,'' in ji ma'aikatar lafiya ta Indiya.

Sai dai kamfanin Marion Biotech, ya ƙi cewa uffan kan batun lokacin da BBC ta tuntube shi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kamfanin dillancin labarai na ANI ya ambato babban jami'i Marion Biotech, yana cewa kamfanin ya dakatar da hada maganin tarin na wucin gadi.

Ya kara da cewa, gwamnati na bincike da umartar kamfanin samar da magungunan ya dauki matakin gaggawa.

Shi dai kamfanin samar da magunguna na Marion Biotech mazauninsa ya na Noida, kusa da babban birnin kasar Delhi.

A yanzu shafin intanet na kamfanin an sauke shi, amma shafin LinkedIn na kamfanin ya ce a shekarar 1999 aka samar da shi.

Kuma magungunan da yake samarwa sanannu ne a gidajen jama'a musamman kasashen tsakiyar yankin Asiya, da tsakiyar Amurka har da yankin Latin, da Kudu maso yammacin Asiya da kuma Afirka.

Kasar Indiya ce ke samar da kashi uku na magungunan da ake amfani da su a duniya, yawanci kan tsarin generic drugs.

Daya daga kasar da kamfanonin harhada magunguna ke bunkasa cikin sauri, ana yi mata da lakabi da ''duniyar magunguna'', sannan ta kasance dillaliyar magunguna ga kasashe masu tasowa.

Sanarwar da ma'aikatar lafiya ta Uzbekinstan ta fitar ranar 27 ga watan Disamba, ta ce maganin Dok-1 Max nau'in na ruwa da kwaya an saida su a kasar tun shekarar 2012.

"Mun gano iyayen wadanda suka mutu sun ba su maganin tarin da kusan mako guda kafin a kwantar da yara a asibiti , kuma suna ba su babban cokali sau hudu a rana, wanda hakan ya zarta ka'idar likita,'' in ji ma'aikatar lafiyar.

Sai dai sanarwar ba ta fadi takamaimai lokacin da yaran suka mutu ba.

Sashen BBC Monitoring ya bada rahoton da ya samo daga shafin intanet din Gazeta.uz, kan cewa hukumomin Uzbekistan sun yi bincike tare da ikirarin yara 15 sun mutu a tsakiyar yankin Samarkand cikin watanni biyu, bayan sun sha maganin tari dan Indiyar.

A ranar 26 ga watan Disamba, shafin kamfanin dillancin labarai na odrobno.uz ya sake wallafa wani sabon rahoton yara 21 kuma 15 daga cikinsu 'yan kasa da shekara uku an yi musu magani ciwon ƙoda.

An kuma yi zargin maganin tari na ruwa da aka samar daga kamfanin na Indiya ne ya haddasa musu hakan, magani kuwa shi ne Dok-1 Max, kuma sun sha tsakanin watan Satumba zuwa Disamba.

Uku daga cikin yara masara lafiyar sun murmure an kuma sallame su daga asibiti.

A watan Oktoba Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gaggawar fidda sanarwa ga duniya ba ki daya, da gargadi kan magungunan har guda hudu da kamfani na Indiya ya samar, da kuma suka janyowa yara kamuwa da ciwon koda a kasar Gambia.

Ta kara da cewa gwajin da aka yi akan maganin ya nuna ya na dauke da wani sinadari da ke janyo kasawar koda da daukewar numfashi.

Gwamnatin Indiya da kamfanin magani na Maiden Pharmaceuticals, ya musanta wannan zargi.

A farkon watan Disamba Indiya ta ce gwaji da aka yi kan magungunan hudu sun cika dukkan ka'idojin da aka gindaya wajen samar da su.

Sai dai wani jami'in gwamnati ya shaidawa BBC cewa hukumar lafiya WHO na yi gaggawar zargin kamfanin da dora masa laifin samar da maganin.

Amma WHO ta kafe cewa ba za ta sauya matsaya ba saboda abin da bincike ya tabbatar da shi ta ke aiki.

A makon da ya wuce, kwamitin da gwamnatin Gambia ta kafa domin binciken lamarin ya bada shawarar gurfanar da shugabannin kamfanin gaban shari'a.

Sannan kwamitin ya ba da shawarar ya kamata a haramta amfani da duk magungunann da kamfanin ya ke samarwa ba wai maganin tarin yara kadai ba.