Bayern Munich ta kammala daukar Kompany sabon kociyanta

Vicent Kompany

Asalin hoton, Getty Images

Bayern Munich ta kammala ɗaukar Vincent Kompany a matakin sabon kociyanta kan ƙwantiragin kaka uku.

Ɗan Belgium mai shekara 38 ya maye gurbin Thomas Tuchel, bayan da ya bar Burnley zuwa Bundesliga, inda ƙungiyoyi suka kai ga cimma matsaya.

Kompany ya lashe Championship da Burnley a 2022-23, amma ƙungiyar ta faɗi daga Premier League a bana, bayan da ta kare ta 19 a kasan teburi.

Kompany, wanda ya yi ritaya daga taka leda a 2020 ya karɓi aikin horar da Burnley daga Anderlecht a 2022, wanda ya tsawaita yarjejeniyarsa a bara zuwa kaka biyar.

Ana kammala kakar Premier League ranar 19 ga watan Mayu a wasa da Nottingham Forest, kociyan bai fayyace makomarsa ba a ƙungiyar.

Tun farko Burnley ta sanar cewar za ta ci gaba da aiki da Kompany a Turf Moor, amma yanzu ta hakura da kociyan ya koma Bayern Munich.

Tuchel ya bar Bayern Munich a watan nan, bayan da ta kare a mataki na uku ateburin Bunsdeliga - mataki mafi muni tun bayan 2010/11.

Bayern ta sha wahala, wajen neman wanda zai maye gurbin Tuchel, wanda tun cikin watan Fabrairu ya sanar da zai bar ƙungiyar.

Kociyan Bayer Leverkusen, Xabi Alonso da na tawagar Jamus, Julian Nagelsmann da na Austria, Ralf Rangnick, duk ba su yadda sun karɓi ragamar horar da Bayern Munich ba.

Bayern Munich ta yi kokari ta rarrashi Tuchel ya ci gaba da horar da ita, daga baya batun ya ci karo da cikas.

Kompany ya taka rawar gani a aikin kociyan Anderlecht da Burnley, wadda ya kai Premier League, koda yake ya ɗan ci karo da koma baya, sakamakon da ta koma Championship.

Tsohon ɗan wasan Manchester City da ya lashe kofin Premier League hudu ya zama mai horar da Anderlecht a 2020, wadda ya buga wa tamaual daga nan ya koma Turf Moor.

BBC ta famince cewar tsohon ɗan wasan Chelsea da Everton, Frank Lampard na son maye gurbin Kompany a Burnley.

Tsohon kociyan Nottingham Forest, Steve Cooper ya ce baya takarar karbar Burnley, bayan da yake sa ran aiki da wata ƙungiyar dake buga Premier League.