Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Godswill Akpabio, sabon Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya?
An haifi Godswill Obot Akpabio a Ukana cikin Ikot Ntuen a jihar Akwa Ibom, ranar 19 ga watan Disamban 1962.
Akpabio dai ya kammala karatunsa na firamare ne a makarantar firamare ta Methodist da ke Ukana, sannan ya yi sakandare a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Fatakwal cikin jihar Ribas.
Ya kammala karatunsa na Lauya a Jami’ar Kalaba da ke jihar Kuros Riba. Daga nan ya tafi Kwalejin Horas da Lauyoyi ta Najeriya da ke Legas a 1988, kafin ya zama cikakken lauya a Najeriya.
A shekarar 2002, an naɗa Godswill Akpabio matsayin kwamishinan albarkatun man fetur da ma'adanai na jihar Akwa Ibom, daga bisani kuma ya zama kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu.
A 2006, an ƙara naɗa shi muƙamin kwamishinan ƙasa da gidaje.
Godswill Akpabio ya tsaya takarar gwamnan jihar Akwa Ibom a ƙarƙashin jam'iyyar PDP cikin watan Afrilun 2007, inda ya yi nasara.
Ya sake tsayawa takara a zaɓen shekara ta 2011 kuma ya samu nasarar sake zama gwamnan jihar Akwa Ibom.
A ranar 28 ga watan Yulin 2015 ne, jam'iyyar PDP ta tsayar da Akpabio a matsayin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, bayan ya ci zaɓe zuwa babbar Majalisar Dokoki ta Tarayya.
A watan Agustan 2018 ne, ya yi murabus daga matsayin shugaban marasa rinjayen, bayan ya bayyana sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.
A watan Yulin 2019 ne kuma shugaban wancan lokaci, Muhammadu Buhari ya miƙa sunansa ga majalisar dattawan Najeriya wadda ta tantance shi don nada shi muƙamin minista.
Daga bisani an rantsar da shi matsayin ministan Neja Delta ranar 21 ga watan Agustan 2019.
Akpabio ya yi murabus a watan Yunin 2022 domin shiga zaɓen fidda gwani na takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, amma ya janye wa Bola Ahmed Tinubu a daren da aka gudanar da zaɓen.
Kwanaki kaɗan bayan zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasar ne, sai ya koma inda ya tsaya takarar sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.
Akpabio ya kayar da abokin hamayyarsa Emmanuel Enoidem na jam’iyyar PDP inda ya zama zaɓaɓɓen ɗan majalisar dattijai bayan zaɓen watan Fabrairu.
A halin yanzu kuma shi ne ya ci zaɓen Shugaban Majalisar Dattijai.