Mece ce gaskiyar yawan al'ummar duniya?

Asalin hoton, Getty Images
Sabbin alƙalumman Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi hasashen yawan al'ummar duniya zai ƙaru daga biliyan 8.2 zuwa kusan biliyan 10.3.
Alƙalumman na yawan al'ummar duniya da aka fitar a 11 ga watan Yuli da ake bikin ranar yawan al'umma ta duniya, sun yi hasashen yawan al'ummar duniya zai kai ƙololuwa a tsakiyar 2080 daga nan kuma a fara samun raguwa sannu a hankali.
Rahoton ya kuma yi hasashen cewa mutanen da aka haifa a yanzu za su yi kusan shekara 73, inda aka samu ƙarin shekara 8.4 tun 1995.
Kusan rabin ƙarni, Majalisar Ɗinkin Duniya na fitar da hasashe kan yawan al'umma ta hanyar amfani da alƙalumman ƙidayar jama'a da ƙasashe ke yi musamman alƙalumman ranar haihuwa da mutuwa.
Amma za mu iya yin imani da waɗannan alƙalumman?
“Alƙaluma marasa tabbas”
"Kiɗayar yawan al'umma a wannan duniyar, kimiya ce da ba tabbas," kamar yadda masanin tattara alƙalumman al'umma Jakub Bijak ya shaida wa BBC.
Farfesa Bijak daga Jami'ar Southampton ya amince cewa abu ɗaya da za a iya tabbatar wa kan hasashen yawan al'umma shi ne rashin tabbas.
"Ba mu da wani mizani," in ji Dr Toshiko Kaneda, masani hasashen yawan al'umma a wata cibiyar binciken yawan al'umma a Washington DC.
Amma hakan ba yana nufin masu hasashen na amfani da alƙalumman ba ne yadda suka ga dama domin yin hasashen.
"Tunani ne mai wahala, daga ƙwarewarmu da ilimi da duk bayanan da za mu iya samu. Babban aiki ne," a cewar Dr Kaneda.
Masu binciken yawan al'umma na sabunta alƙalummansu. Misali, a bana Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi hasashen cewa daga 2100 za a samu kashi shida na yawanmu saɓanin hasashen da ta yi shekara 10 can baya.
Duk da wannan sauyin, yawan al'umma na da matuƙar muhimmanci ga gwamnatoci da kuma masu ruwa da tsaki, waɗanda ke amfani da su wajen ɗaukar matakai da suka shafi makoma.
Don haka, sabbin alƙalumma na Majalisar Ɗinkin Duniya suka nuna muna?
Sabbin alƙaluma
Aƙalumman yawan al'ummar na duniya a 2024 sun ce "ɗaya cikin mutum huɗu a duniya na rayuwa ne a ƙasar da yawan al'ummar ya riga ya kai kololuwar mataki."
Sai dai, ƙasashe 126 da kuma yankunan za su samu ƙarin yawan jama'a a ƙarin wasu shekaru 30, kuma ƙasashen sun ƙunshi waɗanda suka fi yawan al'umma a duniya, kamar Indiya da Indonesia da Najeriya da Pakistan da kuma Amurka.
Wani abin da binciken ya gano a wannan rahoton shi ne samun ƙaruwar tsawon rai, bayan samun raguwa a lokacin annobar korona.
A dunbiya, mutanen da aka haifa a yau, za su iya rayuwa matsakaitan shekaru sama da 73, ƙarin shekara 8 da watanni huɗu tun 1995.
Kwararar baƙi na haifar da ƙaruwar jama'a
Yawan al'umma na da bambanci tsakanin sassan duniya.
Wasu ƙasashe kamar Angola da Jamhuriyyar Afirka ta tsakiya da Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo da Nijar da Somaliya za a samu ƙaruwa a jariran da ake haifa nan da shekara 30. Yawan al'ummarsu ana sa ran zai lunka.
Amma cewar sabon rahoton na Majalisar Ɗinkin Duniya, a wasu sassan duniya, kwararar baƙi ne babban dalilin ƙaruwar yawan al'ummarsu.
A ƙarni na 19, inda yawan al'umma ya kai ƙololuwa - musamman a ƙasashe kamar Jamus da Japan da Italiya da Rasha da Thailand - alƙalumman sun nuna cewa yawan al'umma zai raguwa idan har babu kwararar baƙi.
Rahoton ya ce kwararar baƙi zai zama silar ƙaruwar jama'a a ƙasashe da dama bayan 2054. Ƙasashen sun haɗa da Australia da Kanada da Qatar da Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Amurka.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Ƙaura na ƙaruwa kuma wani mataki ne da ke haifar da ƙaruwar jama'a a duniya," a cewar Farfesa Bijak, amma kuma "yawancin ƙasashe ba su ɗaukar matakai, ko suna ɗauka suna yi ne sau ɗaya a shekara 10, a lokacin ƙidayar al'umma, ba tare da wani tanadi ba,"
Farfesa Bijak ya ce wasu ƙasashen na amfani da alƙalumma yawan jama'a ko rijista "amma ƙasashen ba su da yawa - galibinsu ƙasashe ne da suka ci gaba kamar a Turai da Arewacin Amurka da Australia da New Zealand."
Amma ya ƙara da cewa wasu ƙasashen na ƙoƙarin yin amfani da wasu matakai na tattara alƙalumma, "kamar amfani da fasahar taswirar wayoyin salula, amma wannan tsarin na buƙatar ingantawa kafin zama madogara: ya kamata a fahimci waɗannan alƙalumman sosai."
Dr Kaneda ya ce ana iya sa ido kan tsarin shige da fice, kuma za su iya sauyawa fice da alƙalumman haihuwa.
"Ko a ƙasar da ake samun ƙarancin haihuwa, ba zan taɓa tunanin zai ragu sosai ba, ba zai iya sauya ba da sauri. Amma shige da fice zai iya sauyawa nan-take, saboda bala'o'i na yau da kullum ko kuma yaƙi."
Me ya sa bayanan ƙidaya ke da mahimmanci
Al'adar ƙidayar al'umma domin faɗakarwa da kuma taimakawa wajen ɗaukar matakai, yana da tsohon tarihi.
Masana binciken yawan al'umma sun ce an fara tun 4,000 BC lokacin Daular Babylon a Mesopotamia (da yanzu ake kira Iraƙi) da ta gudanar da ƙidayar al'umma.
Tun a lokacin aka samu fasahar ƙidaya, amma aikin ƙidayar ba abu ba ne mai sauƙi.
Dr Kaneda ta ce ƙoƙarin ƙasashe na tattara bayanai, ko a ƙasashe da suka ci gaba kamar Amurka, "suna fuskantar ƙalubale, musamman samun aminci da yarda a gwamnati da kuma damuwa kan sirrin jama'a."

Asalin hoton, Getty Images
Dr Kaneda ta ce an datse kasafin kuɗi ga hukumomi da ke tattara bayanai a kasashe masu arziki - kuma aikin tattara bayanai na yawan al'umma ya fi zama ƙalubale fiye da ƙasashe masu tasowa.
Amma, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce "duk dala ɗaya da aka kashe wajen ƙarfafa tsarin tattara alƙalumma za a iya samun ribar dala 32.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayar da shawarar fifita tattara bayanai musamman a ƙananan ƙasashe; "misali, yankunan da ke da matsala wajen tattara bayanai musamman ƙananan iyaye mata da shekarunsu ba su wuce 15 zuwa 19 ba, inda ake yawan samun haihuwa."
Sabon hasashen shi ne na 28 daga Majalisar Ɗinkin Duniya. Kuma binciken ya dogara ne daga sakamakon ƙidayar al'umma 1,700 da aka gudanar tsakanin 1950 zuwa 2023 da kuma sauran bayanai da aka tattara daga rijistar al'umma da aka yi.
Cibiyar tattara bayanan lafiya (IHME a Jami'ar Washington da cibiyar IIASA-Wittgenstein a Vienna su ne sauran manyan waɗanda suka jagoranci hasashen na yawan al'umma.










