Alexander-Arnold ya faɗi dalilin barin Liverpool

Lokacin karatu: Minti 1

Ɗanwasan baya na Liverpool Alexander-Arnold ya tabbatar da cewa zai bar ƙungiyar a ƙarshen kaka bayan lashe kofin Premier a bana.

Tun yana ɗan shekara shida yake taka leda a Liverpool, a ranar 30 ga watan Yuni kwangilar shi za ta kawo ƙarshe, kuma ana sa ran zai koma Real Madrid.

"Bayan shafe shara 20 a Liverpool, yanzu lokaci ne da zan tabbatar da cewa zan tafi a ƙarshen kaka," kamar yadda Alexander-Arnold ya sanar da shafinsa na sada zumunta.

Alexander-Arnold yana cikin ƴanwasa a Anfield da kwangilar su za ta ƙare a wannan kaka, amma Mohamed Salah da Virgil van Dijk sun sabunta yarjejeniyarsu a makwannin baya.

Alexander-Arnold zai tafi bayan ƙarshen yarjejeniyarsa.

Ɗanwasan ya haska sau 352 a Liverpool, inda ya ci kwallo 23 da taimakawa a ci sau 86 tun da ya fara taka leda a 2016.

Ya taimaka wa Liverpool lashe kofin Premier a bana ƙarƙashin Arne Slot da kuma zamanin Jurgen Klopp a kakar 2019-20.

Ya kuma taimaka wa Liverpool lashe kofin Zakarun Turai a 2018-19 da kofin Fa a 2022.

Alexander-Arnold ya ce zai tafi ne domin fuskantar sabon ƙalubale da kuma samun ci gaba a rayuwarsa ta tamaula.