'Lodin manyan motocin kaya da mutane na damunmu'

Babbar mota da mutane

Asalin hoton, FRSC

Lokacin karatu: Minti 2

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu sayen kayan abinci da safarar dabbobi ta Najeriya, ta bayyana damuwa game da yadda tireloli da sauran manyan motoci da ke jigilar kayan abinci da dabbobi daga arewaci zuwa kudancin ƙasar, suke ɗaukar fasinjoji a saman motocin.

Sau da dama ana ganin yadda motocin kan ɗauki tarin mutane da kaya, al'amarin da kan haifar da haɗari da asara mai ɗimbin yawa ta rayukan mutane da dukiy.

A tattaunawarsa da BBC, shugaban ƙungiyar na shiyyar Funtuwa a jihar Katsina, Alhaji Bala AbdulMalik, ya bayyana yadda irin wannan lodi da ake yi a manyan motocin ya zamar musu babbar matsala a yanzu - inda yake damunsu matuka.

Ya ce : ''yanzu ba abin da ke ci mana tuwo a kawarya irin ka dauki mota daga nan zuwa Lagos naira miliyan 1 da rabi ko miliyan biyu ma, bayan kai ka bar kasuwa ka tafi an zuba kayanka za a tafi kuma a yi wa motocin balbela da fasinja.

''A karshe mukan rasa ya abin yake ne, direban ne ko 'yankamasho ko ko yaran mota ne. Karshe motar nan ta yi hadari ka zo ku da ke da kayan ku zo kuna neman ma ya za ku gane wannan gawa ta ina ce ku kai ta abin ya faskara,'' in ji shi.

Alhaji Bala ya ce a yanzu haka suna gudanar da bincike a kan matsalar ta wannan lodi da manyan motocin ke yi, wanda ya ce ba da amincewar su masu kaya ba.

Ya ce a duk inda suka yi taro shugabansu na kasa yana nuna cewa, ''doka ne a gwamnatance a ga mota sama da mutum goma a samanta tun da yaran mota ga masu bin shanu to sun isa.''

''Amman a yi balbela a dora fasinja babu dalili tun da abin da muke kallo yanda rayukan al'umma ke salwanta bai yi ba,'' a cewar shugaban.

ya ce wasu motocin za ka ga mutum sama da tamanin wasu ma sama da mutum dari a kansu bayan tarin kaya da aka makare motar nan da su.

Shugaban na shiyyar Funtuwa, ya ce babban abin damuwar ma shi ne rayuka da ake rasawa idan motar ta yi hadari ga kuma asarar dukiya, ta shanu da kuma ta mai mota.

''Muna kira ga shugabannin kungiyoyi na manyan motoci da jami'an tsaro na masu kiyaye hadura har da 'yansanda duk su zo mu hadu mu hada karfi da karfe don mu hana afkuwar wannan hadari, domin rayukan da ake rasawa ya yi tsanani ga asarar dukiyoyi,''

Ya kara da cewa, ''yanzu mota ta yo lodi wanda faduwarta za a yi asara ta wajen naira miliyan dari da wani abu to ta ina dankasuwa zai gano wannan kudin a kasuwanci?''