Ko sabon tsarin Giorgia Meloni ta Italiya a Africa zai yi tasiri ?

Asalin hoton, Getty Images
Italiya ta fitar da "Sabon daftari na tsarin haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka ta hanyar kyautata alaƙa da kuma ci gaba" ba kamar abin da aka saba a baya ba.
Firaministar Italiya mai tsattsauran ra'yi, Giorgia Meloni, ita ce ta bayyana hakan yayin da take jawabi a taron ƙasashen Afirka da Italiya a birnin Rome a farkon shekarar nan.
Yayin taron wanda ya samu halarcin shugabanni da wakilansu daga ƙasashe 45, Meloni ta ƙaddamar da tsarin da ta kira “Mattei plan”.
Tsarin na son ya kawo ƙarshen hijirar da baƙin-haure kan "ta hanyar ƙarfafa alaƙa" da ƙasashe wajen ɗaukar nauyin wasu ayyuka kamar a ɓangaren makamashi, da lafiya, da kuma ilimi.
Enrico Mattei, mutumin da ya kafa kamfanin Eni a shekarun 1950 wanda a lokacin ya dinga kiran Italiya ta taimaka wa ƙasashen Afirka wajen kyautata tattalin arzikinsu.
"Muna so mu kyautata alaƙarmu mai ɗumbin tarihi," in ji Meloni.
Gwamnatin Italiya ta yi alƙawarin samar da yuro biliyan biyar don tallafa wa ayyuka da dama a ƙasashen Afirka, ciki har da Ivory Coast, da Aljeriya, da Morocco, da Masar, da Mozambique, da kuma Dimokuraɗiyyar Congo.
A madadin haka, tana sa ran ƙasashen za su ɗauki matakan hana mutanensu tsallaka Kogin Baharrum ta ƙananan jiragen ruwa zuwa Italiya.
"Ba za a taɓa iya hana yin hijira ba. Ba za a iya daƙile masu safarar mutane ba idan ba a magance abubuwan da ke janyo mutane na barin ƙasashenu ba." Meloni ta bayyana a taron.
A ƙarkashin shirin Mattei, akwai wasu ayyuka da gabatar ciki har da inganta samar da lafiya ga mata da yara a Ivory Coast, da gina cibiyar noma da samar da abinci a Mozambique da kuma karfafa noman alkama da waken suya da dawa a Masar.
Shugaban Kenya William Ruto, ya yi maraba da shirin, yana mai cewa hakan na nu na ci gaba musamman ga alaƙar Italiya da ƙasashen Afirka.
Ya ce a kodayaushe ana danganta Afirka da rikice-rikice da cutuka da yaƙi.
A yanzu ta na sauyawa zuwa wuraren zuba jari da dai sauransu.
Suka
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Manufofin Melini sun fuskanci shakku a wajen ƙungiyoyin kare hakkin dan adam, musamman a kan abin da ta ke nanatawa a kan 'yanci rani da kiran da aka rufe iyakokin ruwa a yankunan Afirka.
Yawancin kungiyoyin kare hakkin dan adam din na ganin an tsara shirin Mattei kare domin kare muradun Italiya.
Kwanaki kafin sanarwar da wannan matakai, tawagar masu talla ciki har da ta wani kamfanin Italiya sun je Maputo, babban birnin Mozambique domin duba inda za su gudanar da wasu manyan ayyuka musamman gina ababen more rayuwa.
A wajen taron, Moussa Faki, shugaban hukumar Tarayyar Afirka, ya yi bayani a kan nuna kin amincewa shirin, maimakon haka ya yi kira da a samar da wasu sabbin ayyuka a nahiyar.
Ya ce," Mu ba mabarata ba ne.Wasu alkawura da ke mana ba za su burge mu ba."
A wajen taron
Su ma wakilan kungiyoyin al'umma sun nuna damuwarsu a kai.
Wasu sun ce," Sanya sunan Enrico Mattei, matsayin sunan shirin, wanda shi ne mutumin da ya ke da iko da kamfanin mai da iskar gas na Italiya Eni, ya nuna karara cewa akwai yiwuwar Italiya na son fadada inda za ta rinka samun mai da iskar dinta ne musamman a Afirka.
Wannan na daga cikin damuwar da Alissa Pavia, daraktar wani shiri a arewacin Afirka ta nuna, wadda ta bayyana shirin Mattei a matsayin wata hanyar Italiya na karfafa matsayinta a game da makamashi a Turai.
Ta ce ta na ganin bai kamata gwamnatin Meloni ta rinka bin wadannan hanyoyi don cimma wata manufa ta ta ba, ya kamata ta guji maimaita wani kuskure da aka yi taba yi a baya.
Ta ce," A maimaikon kawo wasu tsare tsare, kamata ya yi a duba hanyoyin da za a bi wajen magance abubuwa da dama ciki har da batun yadda za a magance matsalar sauyin yanayi da smaar da makamashi marar gurbata muhalli, yin haka zai kara dangantakar ta da Afirka mai karfi."
A bara, Meloni, ta bayar da gudunmuwar fam miliyan 108 ga yarjejeniyar da aka cimma a kan 'yanci rani tsakanin hukumar Tarayyar Turai da kuma Tunisia.
To amma taimakon nata ya janyo damuwa inda wasu ke ganin kamar an tura wa Tunisiya kudi don karfafawa shugaban kasar Ka'is Sa'id gwiwa , a yayin da shi kuma ya ke yin biris ga batun kare hakkin dan adam.
Ana dai ganin Meloni, wadda ke da goyon baya mai yawa, ta ke kuma son kara wasu shekaru uku a kan mulki, zata iya fuskantar matsaloli da dama musamman daga wajen 'yan adawa a kan shirinta na Mattei.
To amma a Nahiyar Afirka, yawancin kasashe ba su da tabbas.










