Rashin abinci ya sa ƴan Zimbabwe tunanin ko dawa da gero na iya maye gurbin masara

A wani abu da ba lallai a iya tunanin faruwarsa ba a baya, dangin Svosve da ke arewa maso gabashin Zimbabwe na kwashe masara domin shawo kan matsalar fari da karancin abinci.
Wannan na faruwa ne duk da cewa masara ita ce ta biyu bayan ruwa wajen muhimmanci a Zimbabwe, saboda ana amfani da garin masara wajen yin abinci sosai.
Masara na taka rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.
Amma karancin amfanin gona ya tilasta wa iyalan Svosves, wadanda ke noma su mayar da hankali sosai kan noman dawa da gero.
Dukkan abubuwan biyu na da muhimmanci a wajen 'yan kasuwar Portugal da suka shigar da masara kasar a shekarun 1500 daga Amurka, a cewar masana tarihi.
Lokacin da na ziyarci Svosves a gidansu a Mduzi, wani yanki mai dausayi yan uwansa sun taru.
Uban gandun Lovemore Svosve ya ce za su sami wadataccen abinci, duk da cewa damina na ta samu tangarda.
“Mun shuka masara mai yawan gaske da kuma dawa da gero, amma ba mu samu komai daga masarar ba, ta ƙone saboda ba a yi ruwan sama tsawon wata uku ba, hatsi kawai muka girbe,” in ji shi.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daya daga cikin matansa mai suna Rose Karina, ta fito da wata ‘yar karamar tukunya da ‘yar masara a ciki. Iyakar abin da suka girbe daga irin masarar ke nan.
Idan aka kwatanta, an jera su a kan barandarsu akwai buhunan dawa da yawa.
Sun sami damar samun fiye da tan ɗaya daga nau'i mai nauyin kilo biyar da taki.
"Ba za mu sake shuka masara ba, " in ji ta, tana girgiza kai.
Kalaman nata dai za su tayar da hankulan galibin 'yan kasar ta Zimbabwe, sai dai ana nuna bukatar sake noman hatsi saboda yadda wasu mutane miliyan hudu ke bukatar agajin abinci.
Sannan kuma a bana za a shigo da kimanin tan dubu 400 na masara daga kasashen waje.
Karancin abinci dai ya kara dagulewa ne sakamakon yadda tattalin arzikin kasar ke cikin wani hali mai cike da hadari, inda hauhawar farashin kayayyaki ya karu zuwa kashi 19 cikin 100 a duk shekara a watan Yuni.
Yayin da kasar Zimbabwe ke fama da matsalar tsadar rayuwa sakamakon wasu batutuwan da suka shafi duniya ciki har da yaki a Ukraine.
Farashin masara da kuma wani nau'in alkama, ya haura sama da kashi 50 tun bayan da aka fara yakin a watan Janairu.

Haka kuma farashin taki ya ninka sau uku, lamarin da ya kara haifar da matsala yayin da kasar Zimbabwe ta dogara da taki daga kasar Rasha.
''Ba ni da cikakkiyar masaniya, amma idan ka kalli abin da ya bayyana a wannan hali da ake ciki ta fuskar sauyin yanayi, da rikicin Ukrain za ka ga cewa wannan ita ce mafita, Mia Seppo, wakilin Zimbabwe a shirin na Majalisar Dinkin Duniya.
Sai dai akwai babban kalubale da za a magance, duba da cewa hatsin da ake nomawa bai taka kara ya karya ba, kuma kalilan din da suke noma shi suna noma abun da bai wuce tan dubu dari uku da saba'in da bakwai ba ne.
Dangin Svosves, sun ce injin da suke amfani da shi na taka rawa wajen aikinsu maimakon yin aikin hannu.
''Abu ne da muke yi cikin awanni, wanda yana iya daukar tsawon wata guda inda ace da hannu za a yi aikin''.
Shirin MDD na UNDP ya yi alkawarin samar da karin wasu injinan da zummar kara bunkasa noman.
Kallon da ake yi wa iyalin Svosves na wadanda suka yi nasara a noma zai iya zaburar da suaran jama'ar Zimbabwe wajen kara himma ta fuskar noma abincin gida wanda ake fama da karancinsa a yanzu.










