Amsoshin Takardunku 09/02/2024
Lokacin karatu: Minti 1
Cikin shirin namu na wannan makon - wanda Muhammad Annur Muhammad ya gabatar mun amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.
Shin su wane ne 'yantawayen M23, da suka ƙwace iko da birnin Goma na gabashin DR Congo a baya-bayan nan?
Me ya sa suke yaƙin, kuma me suke ƙoƙarin cimma?
Shin yaya tsarin bayar da beli yake a Najeriya?
Waɗannan su ne tambayoyin da muka gabatar wa masana domin amsa muku su, kamar yadda kuka buƙata.







