Yadda wata mahaifiya ta sayar da ƴarta domin samun kuɗin shan ƙwaya

Someone in a crowd holds up a poster of Joshlin Smith with the words underneath her image saying, 'Justice for Joslin (sic)'.

Asalin hoton, Gallo Images via Getty Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga riƙe da hoton Joshlin Smith suna neman a yi adalci kan ɓatar ta
    • Marubuci, Khanyisile Ngcobo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Johannesburg
  • Lokacin karatu: Minti 5

An yanke wa matar da aka samu da laifin sacewa da sayar da ƴarta ƴar shekara shida hukuncin ɗaurin rai da rai, tare da wasu mutane biyu da ke da hannu cikin lamarin.

An yanke wannan hukunci ne ga Racquel, wato Kelly Smith da saurayinta Jacquen Appollis da kuma abokinsu Steveno van Rhyn, kimanin shekara ɗaya bayan ɓacewar yarinyar mai suna Joshin, wadda aka rasa inda take sama ko ƙasa.

Faifan bidiyon da aka kunna na yarinya Joshin Smith, wadda ta ɓace tana ƴar shekara shida, shekara ɗaya da ta gabata a ƙasar Afirka ta Kudu, ya sanya mutane da dama da ke cikin kotun sun sharɓi kuka na tausayi.

An kunna bidiyon ne lokacin da ake sauraron shari'ar da ake yi a garin Saldanha Bay, kusa da birnin Cape Town, gabanin yanke wa mahaifiyar yarinyar hukunci - wadda ƴar ƙwaya ce da aka zarge ta da sayar da ƴarta domin samun kuɗi.

Mahaifiyar, mai suna Racquel Smith, wadda aka fi sani da Kelly Smith, an same ta da laifin sacewa da safarar ƴarta a farkon watan Maris. Matar mai shekara 35 - kotu ta kama ta da laifin ne tare da saurayinta mai suna Jacquen Appollis da kuma abokinsu Steveno van Rhyn.

Hatta tafintan da ya riƙa fassara zaman shari'ar sai da ya fashe da kuka lokacin da yake fassara bayanin.

Mutane da dama sun bayar da shaida kan yadda mahaifiyar ƙaramar yarinyar ta sayar da ita da kuma tasirin da hakan ya yi gare su.

Wani da ya bayar da shaida ya ce mahaifiyar yarinyar ta sayar da ita ne ga wani boka, wanda ake kira "sangoma", wanda ke son amfani da "idonta da kuma fatarta."

Wani fasto da ke yankin ya bayyana cewa ya ji lokacin da Kelly Smith ke tattaunawa kan yadda za ta sayar da ƴaƴanta a kan kuɗin Afirka ta kudu, rand 20,000 (dala 1,100) kan kowanne, amma ta ce za ta iya amsar dala 275.

Mahaifiyar da sauran waɗanda ake zargi da sayar da yarinyar sun ƙi amincewa su halarci zaman sauraron ƙarar da aka kwashe mako shida ana yi a ɗakin taro na garin, wanda aka yi hakan domin bai wa mutane da yawa damar halarta.

To amma a lokacin da mahaifiyar ta ji bayanan da aka yi da kuma bidiyon ƴar tata da aka kunna, ita ma ta sharɓi kuka.

Malamar ajin su Joshlin ta ce ƴan ajinta suna kewar yarinyar wanda hakan ya sa sukan kunnan waƙar da yarinyar ta fi so, bayan sun daɗe suna tambayar inda ƙawar tasu take.

Har ya zuwa wannan rana babu wanda ya san abin da ya faru da yarinyar.

Joshlin Smith's mother in a yellow, white and black stripped shirt, sits in court with her hands clasped. Two her left sit her two co-accused - 2 May 2025

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mahaifiyar Joshlin Smith da sauran waɗanda ake zargi sun ƙi yin bayani a gaban kotu
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ɓacewar yarinya Joshlin a ranar 19 ga watan Fabarairun 2024 ya jefa al'umma cikin alhini a fadin Afirka ta Kudu.

Wata ƙwararriya kan binciken laifuka kuma shugabar hukumar nemo yaran da suka ɓata a Afirka ta Kudu, Madeleine McCann ta ce duk da al'umma sun ji daɗi da hukuncin da aka yanke wa masu laifin "babbar tambayar ita ce babu wanda ya san inda Joshlin take, kuma wannan ne abin da mutanen Afirka ta Kudu ke son su sani".

Kelly Smith ce ta haifi Joshlin a watan Oktoban 2017, kuma mahaifinyta shi ne Jose Emke, tsohon saurayin Kelly, wanda shi ma ya yanke jiki ya fadi a lokacin sauraron ƙarar a ranar Laraba.

Wata jami'ar kula da al'umma ta bayyana wa kotu cewa Joshlin, wadda ita ce ta biyu ga mutanen, ita da ɗansu na farko mai shekara 11 sun yi fama da rashin kula a rayuwarsu.

Kelly Smith ta rayu ne da kakarta a lokacin da take tasowa, kuma ta yi fama da matsalar shan ƙwaya tun tana da shekara 15 a duniya - inda a yawan lokuta takan yi ƙoƙarin bugun kakar tata da kuma ƴaƴanta, kamar yadda jami'ar kula da al'ummar ta bayyana wa kotu.

Wani rahoto ya bayyana yadda matsalar shan ƙwaya da Kelly ke fama da ita ta yi muni a lokacin da aka haifi Joshlin.

Kakar Kelly ta kore ta daga gidanta ne a lokacin da matsalar shan ƙwayarta ta tsananta, inda a lokacin ta yi yunƙurin caka wa ɗan nata wuƙa.

A corrugated iron shack in Middelpos

Asalin hoton, Mohammed Allie / BBC

Bayanan hoto, Rumfar da Joshlin ta rayu tare da mahaifiyarta da ƴan'uwanta

An bayyana cewa Kelly ta riƙa yin ayyuka na ƙasƙanci domin kula da iyalinta, ciki har da aikatau da ta riƙa yi a gidan wata mata mai suna Kelly Zeegers, a kusa da su, inda aka riƙa biyan ta da kayan abinci a maimakon kuɗi.

Kelly Zeegers ta ce ta yi hakan ne "domin tabbatar da cewa matar ta samu abin da za ta ci, ita da ƴaƴanta," kamar yadda ta fadi a lokacin da take bayar da shaida a kotu.

Laurentia Lombaard ita ce kaɗai matar da ta bayar da ɗan bayanin da aka sani kan Joshlin a ranar da ta ɓace, wadda daga baya ta zama mai bayar da shaida ta gwamnati.

Lombard ta kasance a gidan su Joshlin domin shan ƙwaya tare da Appolis da kuma Van Rhyn a lokacin.

Ta bayyana wa kotu cewa a Joshlin, wadda ita da yayanta suka fara zuwa makaranta ƴan makonni kain bacewarta, a ranar ba su je makaranta ba saboda kayansu sun yi datti.

Ta ce an bar yaran ne ƙarƙashin kulawar Appollis, sai dai Kelly kan shigo gidan lokaci zuwa lokaci domin zuƙar sigari.

Babu tabbas kan takamaiman lokacin da Joshlin ta ɓata, to amma kotu ta iya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da rana - sai dai ba a kai rahoton ɓacewarta ba sai kimanin ƙarfe 11 na dare.

Jami'in da aka bai wa aikin tattara rahoto kan abin da ya faru daga mutanen uku da ake zargi ya ce Kelly Smith mace ce da "ba ta jin kunyar zabga ƙarya" da kuma "yaudara".

"Saboda haka ba za a yi kuskure ba idan aka ce Kelly Smith ita ce ta kitsa sayar da ƴar tata," in ji shi.

The three accused walking in for a sentencing hearing in Saldanha Bay in a community centre - 27 May 2025.

Asalin hoton, Gallo Images via Getty Images

Bayanan hoto, Mutane uku da ake zargi a lokacin da aka yanke musu hukunci ranar 27 A community centre has played host to the High Court trial

Sau da yawa dai akan samu ɓacewar yara da dama a Afirka ta Kudu ba tare da an kai rahoto ba.

Wani shafin wallafa labarai na ƙasar mai suna IOL, ya ruwaito cewa yara 632 ne aka bayar da rahoton ɓacewar su a Afirka ta Kudu a bara, sannan an samu rahoton ɓatan yara 8,743 a cikin shekara 10.

Amma a farkon wannan wata, maimagana da yawun ƴansanda Athlenda Mathe ta ce an samu yara da dama waɗanda aka sake haɗa su da iyayensu.