Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalibai mata da su da makomar ilimi a Afghanistan
Yayin da aka bude makarantu a wasu sassan Afghanistan, an tilasta wa 'yan mata zaman gida, inda suke kula da 'yan uwansu maza, yayin da sauran mazan ke tafiya makaranta domin daukar karatu.
Kasar ta kasance daya tilo a duniya da 'yan mata tsakanin shekara 12 zuwa 18 ba sa zuwa makaranta.
Dalibai maza sun koma bakin karatu, bayan Taliban ta karbe iko da kasar a shekarar da ta gabata, amma mayakan sun yi biris da kiraye-kirayen kasashen waje na su bude makarantun dalibai mata.
"Ban san makomata ba, ba na tunanin komai. Babu abin da nake yi baya ga taya aikin gida.
Babu wani fatan ci-gaba, sai dai a yi sha'ani kawai,'' in ji Maryam.
Yawancin matasan mata da BBC ta zanta da su, shekara guda da hana su zuwa makaranta, sun fitar da rai da sake zuwa aji daukar karatu.
Tun tana karama, Maryam ke son zama likita, ya kamata a ce ta kusan kammala Sakandare, ta tuna abin da ya faru a ranarsu ta karshe a makaranta, shekara daya ke nan.
Bakar rana
"Ranar da Taliban ta karbe iko da birnin Kabul, muna tsaka da jarr
abawar tsakiyar zangon karatu ne, shugabar makarantarmu ta ce mana mu yi maza mu gudu gida.
Tun a lokacin da na ji haka, na san kila wannan ce ranar karshe da za mu je makaranta.
Watanni 12 ke nan da mata ke zanga-zanga a wasu sassan Afghanistan, ciki har da birnin Kabul.
Suna kiran a sake bude makarantu domin 'ya'yansu mata su samu ilimi.
Maryam ba ta taba shiga wannan zanga-zangar ba, amma ranta a bace yake da matakin.
"Ana koyar da mu darasin tarihi, abubuwan da suka shafi shugabannin da suka shude.
Amma halin da nake ciki a yanzu ya zama tarihi, saboda ban kammala ba, zuciyata ta kasa yarda cewa hakan ta faru."
Makonni bayan Taliban ta karbe iko a watan Agustan bara, an sake bude makarantun sakandare na maza a ranar 18 ga watan Satumba 2021, to amma sun haramta wa daliban sakandare mata komawa karatu.
Yawancin 'yan matan Afghanistan, sun saci jiki sun koma zuwa makarantun da aka bude cikin sirri a birane da garuruwan kasar.
Sai dai kash, ba za su samu wata shaida da za ta ba su damar shiga jami'a ba.
Karatu ta intanet
Wasu daliban na kokarin koyon karatu daga gida, ta amfani da intanet.
Amma malamai sun ce ba za ka taba hada karatun da ake koyarwa a makaranta da wanda ake koyo ta intanet ba.
Wata malama kuma mai fafutuka a kasar, mai suna Pashtana Durrani, ta ce makaranta ''fage ne na cudanya da mutane da sanin mu'amala da wasu.''
"Muna daukar lokaci ba tare da mun tattauna ba, musamman saboda muna zaune wurare daban-daban.
Haduwa wuri guda domin karatu wani babban kalubale ne."
Ta ce ta kasa gane abin da ke faruwa, ta kasa gane dalilin Taliban na kin bude makarantun 'yan matan.
A watan Mayun bana, Taliban ta sanar da sake bude makarantun mata, amma sai a kurarren lokaci suka sanar da fasawa.
Yawancin makarantu a kudancin yankin Patkita, sun bude kofofinsu ga dalibai mata a watan Satumba, amma dole suka rufe saboda matsin lamba daga shugabannin yankin, labarin ya karade kafafen yada labarai a wancan lokacin.
Haramcin har abada
A wasu kasashen Musulmai, ana sanya dokoki a makarantun mata, amma ita Taliban daukar matakin haramtawa na har abada ta yi.
A matsayin martani ga kiraye-kirayen kasashen duniya, Taliban cewa ta yi: ''Za a bude makarantu bayan daukar mataki kan yadda dalibai mata za su sanya kayan makaranta karkashin koyarwa da dokokin addinin Musulunci da al'adun Afghanistan.''
Al'ummar Afghanistan na da tsattsauran ra'ayi da riko kan addini, kuma yawanci mata na tafiyar da rayuwarsu karkashin dokar Musulunci kama da ga sutura da zamantakewa da sauransu.
Kuma haka abin yake tun kafin bayyanar kungiyar Taliban. Sannan sanya Hijabi ko Burqa ba sabon abu ba ne ga matan kasar.
Sheikba da Shadi, 'yan uwan juna ne, mazauna Kabul, suna tsakanin shekara 15 zuwa 16, kuma shekara guda kenan suna zaman gida, ba tare da zuwa makaranta ba.
''Muna amfani da suturar da addinin Musulunci ya amince da ita, amma yanzu Taliban ta hana mu zuwa makaranta ko da mun sanya hijabi.'' in ji Shadi lokacin hira da BBC.
''Taliban sun yi alkawura da dama, amma sun kasa cikawa.''
Sakon na Sheikba a bayyane yake: ''Ku daina wasa da iliminmu domin cimma bukatar siyasa.''
Abin tambayar shi ne, za su saurara? Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga Taliban su sake bude makarantu.
Markus Potzel, shi ne mukaddashin mataimakin Majalisar Dinkoin Duniya a Afghanistan, ya bayyana halin da ake ciki da mai daga hankali, abin kunya, abin da za a iya kauce wa abkuwarshi domin kawo sauyi da ci-gaba a kasar.
A ranar Lahadi, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya wallafa wani sako a shafinsa na tuwita cewa: ''Watanni 12 da suka wuce, lokaci ne da aka yi wa ilimi kafar ungulu, aka yi wasa da damar, wasu wannan dama ta wuce su har abada.''
Tun kafin Taliban ta karbe iko da Afghanistan, asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce yara sama da miliyan 4 ne aka cire su daga makaranta, kusan kashi 60 cikin dari na adadin mata ne.
Malaman Addini
Haramcin da Taliban ta yi, ya janyo yawancin kungiyoyin agaji sun dakatar da bayar da tallafi a fannin ilimi,
Sakamakon rashin kudin biyan albashin malaman makaranta, yanzu Taliban ta dauki matakin rarraba malaman addini makarantun maza domin koyar da su.
Tattalin arzikin Afghanistan ya dogara ne ga tallafi, kuma yanzu Taliban hankalinta tashe yake na ganin an samu kudaden da kuma fafutukar ganin kasashen duniya sun aminta da su ta fuskar difilomasiyya.
''Ya kamata kasashen waje su ba da fifiko kan hakkin mata da 'yan mata ta fuskar ilimi, a lokacin zaman sasantawa da Taliban,'' in ji Samira Hamidi, jami'a a hukumar kare hakkin dan adam ta Amnesty International mai kula da yankin kudancin Asiya.
Ta kara da cewa: ''Yancin ilimi hakki ne na kowanne dan-Adam, abin da ya kamata Taliban da ta kwace mulki ta sani kenan, dole a dauki mataki.
Tsare-tsaren da a yanzu Taliban ke amfani da su, haramtattu ne, babu adalci, akwai musgunawa kuma sun take dokokin kasa da kasa.''
'Muna neman dauki daga Allah'
Babu wata kasa a duniya da ta amince da shugabancin Taliban, amma wasu kasashe kamar Pakistan da China na mu'amala da su lokaci zuwa lokaci.
A yanzu dai 'yan mata a Afghanistan, sun fara sarewa, amma duk da haka suna neman dauki daga kasashen waje.
''Muna neman dauki daga Allah,'' in ji Maryam. ''Muna son makomarmu ta yi kyau.''
(An sauya sunayen daliban domin ba su kariya)