Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilin da ya sa na ƙi janye wa Peter Obi - Kwankwaso
Rabi'u Musa Kwankwaso, shugaban jam'iyyar NNPP kuma dan takarar mukamin shugaban kasa a babban zaben da ke tafe a watan Fabarairu, ya tattauna da BBC kan wasu muhimman batutuwa, cii har da dalilinsa na kin mara wa Peter Obi - dan takarar mukamin shugaban kasa a jam'iyyar Labour baya.
Kwankwaso ya ce ya fi Mista Obi kwarewa, "Na yi ayyuka iri-iri; na yi aikin gwamnati shekara 17, shi bai yi ba, Na zama mataimakin kakakin majalisar wakilai, shi bai yi ba. Ko iliminmu ma idan ka duba, za ka ga ba iri daya ba ne".
Sai ku latsa hotonsa a sama domin jin cikakkiyar hirar.