Daruruwa sun mutu a mummunan haɗarin jirgin kasa a Indiya

Jiragen kasa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Hadarin jiragen kasa a kasar Indiya

Akalla mutum 288 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu 900 suka jikkata a haɗarin jiragen kasa biyu da ya auku a jihar Odisha da ke gabashin kasar Indiya, a cewar jami'an kasar.

An aika da motocin ɗaukar marasa lafiya fiye da 200 zuwa wurin da al'amarin ya faru a gundumar Balasore a cewar babban sakataren Odisha Pradeep Jena.

Ana tsamanin jirgin kasan farko ya kauce hanya ne kafin daga bisani wani jirgin kasan ya buge shi a layin dogon da ke kusa a yammacin Juma’a.

Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Indiya ta ce jiragen kasan biyu da suka yi karo da juna sun hada da Coromandel Express da Howrah Superfast Express.

Sudhanshu Sarangi, babban darakatan hukumar kwana-kwana ta Odisha, ya ce ya zuwa yanzu an zakulo gawarwaki 207.

Mista Jena ya kuma ce ana fargabar cewa adadin wadanda suka mutu zai ƙaru.

Wasu labaran da za ku so karantawa

Firaiministan Indiya Narendra Modi ya ce ya damu da al'amarin kuma ya nuna alhini ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu,

"Ana ci gaba da gudanar da ayyukan neman masu sauran numfashi a wurin da abin ya faru kuma ana ba wadanda suka tsira kulawar da ta kamata," sakon da ya wallafa a shafinsa na tweeter.

Wani da ya tsira da ransa ya ce "mutane 10 zuwa 15 suka fado mini a lokacin da hadarin ya faru kuma daga nan ne komai ya rincabe. Na kasance karkashin tulin mutane

"Na ji rauni a hannuna da bayan wuyana, lokacin da na fito daga cikin jirgin kasan. Na ga wani da ya rasa hannunsa , wani kuma ya rasa kafarsa, yayin da fuskar wani ta sauya sakamakon rauni da ya ji," wanda ya tsirar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasar ANI.

An yi ammanar cewa taragogin dayan jirgin, da dama sun kife inda wasu daga ciki sun koma dayan layin dogon da ke kusa.

Ana tsamanin dayan jirgin da ke kan hanyarsa ta zuwa Howrah daga Yesvantpur ya yi karo da tarogogin da suka kife.

Jami'an Indiya sun ce hadarin ya kuma shafi wani jirgin kasan kaya da ke wurin.

Sai dai ba su yi karin haske ba.