Adamawa: Zaɓen da aka kammala ƙura ba ta kwanta ba

Kwana ɗaya bayan damƙa shaidar cin zaɓe ga Ahmadu Umaru Fintiri, ɗan takarar da ya yi nasara a zaɓen gwamnan jihar Adamawa wa'adi na biyu, har yanzu dambarwa da kuma zarge-zarge, ba su ƙare ba.

Batu na baya-bayan nan, shi ne wata sanarwa da hukumar zaɓe ta INEC ta fitar tana musanta wasu zarge-zarge da ake alaƙantawa da jami'an da ta aika, su gudanar da zaɓe a Adamawa.

Ta ce zargin da wani ko wata 'yar takara ke yi cewa - jami'an zaɓen Adamawa cikin dare sun kai ziyara gidan gwamnatin jihar - ba gaskiya ba ne.

Haka zalika, sanarwar wadda kwamishinan INEC kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Festus Okoye ya fitar, ta ce shi ma batun cewa an ba wani ɗan takara jerin sunayen jami'an sanar da sakamakon zaɓe na jihar, ba gaskiya ba ne.

A cewar INEC irin wannan ganawa da aka yi zargi, ta ci karo da rantsuwar zama 'yan ba-ruwanmu da dukkan ma'aikatan hukumar suka yi.

Ta kuma ce, ga duk mai lura zai fahimci cewa hukumar zaɓen ta naɗa mutum ɗaya ne, matsayin mai karɓar sakamakon jihar Adamawa a zaɓen shugaban ƙasa, kuma shi ne ta sake turawa jihar a zaɓen gwamna.

A jiya ne 'yar takarar da ta zo ta biyu a zaɓen, Aishatu Ɗahiru Binani ta fitar da wata sanarwa wadda a ciki ta yi zargin cewa jami'an INEC sun kai ziyara gidan gwamnatin Adamawa.

Ta ce wani abin bambarakwai ma, shi ne sanarwar da jami'an suka bayar lokacin da suka dawo daga gidan gwamnati, cewa sun karɓe aikin tattara sakamakon zaɓe.

Sanarwar ta ce rawar da waɗannan jami'an INEC da suka je Adamawa daga Abuja suka taka, da kuma haƙiƙanin abin da ya kai su gidan gwamnati, kamata ya yi, ya zama abin damuwa ga duk wani mai burin ci gaban dimokraɗiyya.

Ta kuma ce jami'an ta haramtacciyar hanya sun faɗa wa kwamishinan zaɓen jihar ya dakatar da aiki, duk da yake sun je Adamawa ne da sunan ba da shawara.

Sai dai INEC ta ce zarge-zargen duk ba gaskiya ba ne "musamman ma da yake babu wata shaida da aka iya gabatarwa".

Hatta iƙirarin da sanarwar ta yi cewa hedkwatar INEC ta ƙasa musamman ta ware jihar Adamawa wajen tura kwmaishinoninta na ƙasa da sauran jami'ai daga hedkwata da sauran jihohi maƙwabtan Adamawa, don canza sakamakon zaɓen cike-giɓi da kuma mayar da kwamishinan zaɓen jihar gefe.

"Duk ba gaskiya ba ne," in ji INEC.

Kafin wannan, rundunar tsaron farar hula ta Civil Defence ta fitar da wata sanarwa inda take bayyana kiran kwamandanta na jihar Adamawa, zuwa Abuja.

Ta ce matakin ya zo ne saboda zargin da wasu ke yi cewa, an haɗa baki da jami'an tsaro a dambarwar da ta dabaibaye zaɓen jihar.

Sanarwar wadda daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, CC Olusola Odumosu ya fitar ta ce babban kwamandan rundunar Civil Defence ya umarci Muhammad Bello ya gaggauta miƙa harkokin mulki ga mataimakinsa.

Kuma ya je Abuja, ya yi bayani game da rawar da ya taka cikin harkokin zaɓen.

Rundunar ta NSCDC ta nanata cewa ita ba 'yar siyasa ba ce, kuma ba hukuma ce ta siyasa ba, don haka ba za ta lamunci wani jami'inta ya sa hannu cikin taƙaddamar siyasa kamar yadda ake ta zargi an yi a jihar Adamawa ba.

Ta ce idan za a iya tunawa dai, ayyana Aisha Dahiru Binani ta jam'iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamna a jihar Adamawa, daga kwamishinan zaɓen jihar, lokacin da ake jiran sakamakon sauran ƙananan hukumomi, abu ne da ya fusata ɗumbin jama'a, kuma ya janyo zargin da ake yi wa hatta jami'an rundunar.

Shin me ya faru?

A ranar Litinin ne, Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta dakatar da kwamishinan zaɓenta na jihar Adamawa, Barrister Hudu Ari.

Inda ta umarce shi ya fice daga ofishinta, har sai abin da hali ya yi.

Daga bisani kuma, ta ce ta miƙa batun Hudu Ari hannun Babban Sufeton 'Yan sanda don gudanar da bincike, da kuma duba yiwuwar ɗaukar matakin gurfanar da shi gaban kotu.

Haka zalika, INEC ta ce ta aika wa Sakataren Gwamnatin Tarayya bayani game da halayyar kwamishinan zaɓen Adamawa, inda ta buƙaci ya sanar da hukumomin da ke da ikon naɗa jami'an zaɓe.

A ranar Lahadi ne dai, Hudu Yunusa Ari ya shiga zaure karɓar sakamakon zaɓen jihar, ya sanar da Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamna, tun ma kafin a kammala tattara sakamako.

Ya dai sanar da matakin ne ba tare da ya yi bayani dalla-dalla kan yadda Aisha Binani ta ci zaɓen ba, da kuma ƙuri'un da kowacce jam'iyya ta samu a zaɓen.

INEC daga bisani dai, ta ce matakin da Hudu Ari ya ɗauka haramtacce ne, don haka ba za a yi aiki da shi ba.

Zargin biyan naira biliyan biyu a murɗe zaɓe

Ita dai 'yar takarar da ta zo ta biyu a zaɓen gwamnan jihar Adamawa a cikin sanarwar da ta fitar, ta zargi muƙarraban gwamnatin jihar Adamawa da ayarin 'yan sandan gidan gwamnati da 'yan bangar siyasa da cewa su ne suka ritsa wani jamin hukumar tsaron farin kaya na DSS da bakin bindiga.

Ta kuma yi zargin cewa tursasawar da aka yi wa jami'in ce ta sa ya yi furucin cewa an ba da cin hancin naira biliyan biyu don a murɗe zaɓen jihar Adamawa.

Bayanin nata na zuwa ne bayan an ga bidiyon wasu jami'ai masu alaƙa da zaɓen cike-giɓi na jihar Adamawa, inda wani da aka yi raɗe-raɗin cewa jami'in tsaron farin kaya ne a bayan mota, yana iƙirarin cewa kuɗi aka bai wa jami'an zaɓe don su bayyana Aishatu Binani a matsayin wadda ta yi nasarar lashe zaɓen gwamna.

Aisha Binani dai rubuta da babban baƙi a cikin sanarwarta cewa ba taɓa yin haka ba. Kuma ba za ta taɓa yi ba.

'Ni ba 'yar siyasar ko a mutu ko a yi rai ba ce'

Ta ce "ni 'yar dimokraɗiyya ce, kuma a ko da yaushe na kasance 'yar dimokraɗiyya ta alƙawari.

Ba zan taɓa yin wani abu da zai kawo zagon ƙasa ga tsarin dimokraɗiyya ba".

Aisha Binani ta ce ita ba 'yar siyasar ko a mutu a yi rai ba ce.

A cewarta, ta ci zaɓuka a baya har ta je Majalisar Wakilai da ta Dattijai, kuma da zaɓen gaskiya, mai tsafta ta yi hakan.

A yi bincike

Ɓangarori da dama a Najeriya sun yi ta kiraye-kirayen a yi bincike.

Kuma a gurfanar da duk wani jami'i da aka samu da hannu wajen aikata ba daidai ba, a zaɓen gwamnan na jihar Adamawa a gaban shari'a.

Cikin masu waɗannan kiraye-kiraye har da zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannunsa ranar Laraba, Tinubu ya buƙaci 'yan sanda su gudanar da cikakken bincike.

Kuma su bankaɗo duk abubuwan da suka faru a zaɓen cike-giɓi na gwamna a jihar Adamawa da kuma taƙaddamar da ta biyo baya.

Ya yi kira ga waɗanda zaɓen ya ɓata wa rai, su bi kadi ta halastacciyar hanya don ganin an share musu hawaye.

Ya ƙara da cewa a tsarin dimokɗiyya, mutum ɗaya kawai yakan kasance mai nasara.

Buhari ba ya katsalandan - Lai Mohammed

Kafofin labaran Najeriya sun ambato ministan harkokin yaɗa labarai Alhaji Lai Mohammed yana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙi sa baki ne kan abin kallon da ya faru a zaɓen gwamnan jihar Adamawa, saboda shi ba ya katsalandan cikin harkokin hukumomin gwamnati.

Ya ce hukumar zaɓe ta INEC na da cikakken iko, ta hukunta duk wani jami'inta kamar kwamishinan zaɓen jihar Adamawa da ta dakatar, Hudu Yunusa Ari. .

"Ba na tunanin gwamnatin nan ta taɓa yin katsalandan cikin harkokin hukumar zaɓe mai zaman kanta game da yadda take gudanar da zaɓuka," Lai Mohammed ya ce a lokacin da yake musayar bayanai da 'yan jarida a fadar shugaban ƙasa.

Ministan ya kuma ce shi bai karɓi wani rubutaccen ƙorafi da aka aika wa Shugaba Buhari game da buƙatar neman hukunta kwamishinan zaɓen da ake zargi da aikata ba daidai ba, wanda a taƙaice ya bayyana a matsayin ma'aikacin INEC.

“Don haka, babu buƙatar sai mun shiga cikin wannan lamari. Gaba ɗaya batu ne na hukumar zaɓe ta INEC kuma hukumar za ta iya maganin wannan matsala.

“Shugaban hukumar zaɓe shi ne ke da wuƙa da nama kan dukkan ma'aikatan INEC kuma yana tafiyar da al'amuranta. To, me kuma kuke so gwamnati ta yi?” Lai Mohammed ya tambaya