Yaya ake ji idan gwamnatoci suka katse intanet?

Yaya ake ji idan gwamnatoci suka katse intanet?

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Intanet ta zama wani ɓangare na rayuwarmu ta yadda mutane da dama ba sa jin daɗin rayuwa idan babu shi a yau.

Amma a ƙasar iran, kwanan nan gwamnati ta katse sadarwar intanet wanda ya hana samun labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a kasar sosai.

Hakan na zuwa ne sakamakon zanga-zangar da ta karade kasar, inda masu boren ke nuna fushinsu kan mutuwar wata matashiya Mahsa Amini da ta mutu lokacin da take tsare a hannun yan sanda.

Jami’an tsaro sun kama Mahsa ne da zargin cewa ba ta saka hijabi ba kamar yadda dokokin kasar suka tanadar.