Ko mata sun samu ƴanci a Syria bayan tafiyar Bashir al-Assad?

Asalin hoton, Louai Beshara / AFP / Getty Images
- Marubuci, Borza Shimshak
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Turkish
- Lokacin karatu: Minti 8
Watanni kaɗan da suka wuce, mai ɗakin shugaban Siriya, Latifa Droubi, ta kwatanta matan Siriya a matsayin "jagororin al'umma" a wani bikin yaye ɗalibai a Jami'ar Idlib, wanda shugaban riko na ƙasar Ahmed Sharaa ya halarta.
"Gudummawar ku a ɓangaren ilimi, tattalin arziki, yaɗa labaru, likitanci da kuma injiniyanci na da muhimmanci wajen sake gina ƙasa," kamar yadda Ms. Droubi ta faɗa wa matan da ke murnar kammala karatu.
Shugaban na Siriya ya gode wa uwargidansa, inda ya kira ta da "babbar mai ba shi goyon baya a matsayin mace, mata da kuma ɗaliba."
A ranar 8 ga watan Disamban, 2024, sojoji tare da jagorancin Tahrir al-Sham suka kutsa cikin Damascus, babban birnin Syria.
Bashar al-Assad ya tsere daga ƙasr, abin da ya kawo karshen mulkin jam'iyyarsa ta Baathist na tsawon shekara 61.
Abu Muhammad al-Julani, shugaban kwamitin Tahrir al-Sham, ya shiga fadar shugaban ƙasa karkashin sunansa na asali, Ahmed al-Sharaa, tare da hawa kan kujerar shugaban ƙasar a matsayin na riko.
Mata masu fafutuka a Syria sun faɗa wa sashen Turkiyya na BBC cewa a tsawon shekara ɗaya da ya wuce, tsarin siyasar ƙasar ya hana mata shiga domin a dama da su a ɓangarori da dama.

Asalin hoton, Louai Beshara / AFP / Getty Images
Shigar mata fagen siyasa
Lokacin da Ahmed Sharaa ya zo kan mulki, tarihinsa na alaƙa da ƙungiyoyin jihadi ya sanya shakku tsakanin waɗanda ke hanƙoron tsarin dimokraɗiyya, musamman kan daidaito tsakanin jinsuna.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A martaninsa, Mista Sharaa ya nanata muhimmancin kasancewar mara a kan manyan muƙamai.
Matakin farko da sabuwar gwamnatin ta ɗauka shi ne na kirkiro da ofishin kula da harkokin mata. Aisha Debs, darekta a ofishin, da farko ta sanar da cewa matan Siriya za su kasance a cikin dukkan ɓangarorin sabon sauyi da aka samu a ƙasar.
Sai dai kalaman da ta sake yi, sun fuskanci suka daga ƙungiyoyin kare hakkin mata.
"Kalamansa ba su karfafawa mata shiga harkoki a dama da su ba. Har ma ya ce abin da ya fi shi ne mata su mayar da hankali kan iyalansu da mazajensu," a cewar Hanan Zahreddin, wata babbar lauya wadda ke kallon kanta mai fafutukar kare hakkin mata, lokacin tattaunawa da BBC.
A cewarta, duk da cewa Aisha Debs na ci gaba da kasancewa kan kujerarta duk da irin adawa da masu fafutuka mata ke yi, "hana ya nuna cewa tana bin umarni ne da tsare-tsaren gwamnati."
Gwamnatin rikon kwaryar wadda aka kafa a watan Maris ɗin 2025, na da mace ɗaya tilo a matsayin minista, matakin da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam suka yi suka a kai.
Wakiliyar sashen Larabci na BBC, Dalia Haider ta ce lokacin mulkin Assad, gwamnati ta yi ƙoƙarin bayyana cewa akwai mata a cikin manyan mukamai, ciki har da kujerar mataimakin shugaban ƙasa, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, attoni-janar na ƙasa da kuma sauran hukumomi.
"Sai dai gaskiyar shi ne ba haka duka lamarin yake ba," kamar yadda ta faɗa, inda ta ƙara da cewa hakkokin mata kaɗan ne idan aka kwatanta da na maza.
Dalia ta ce tun da gwamnatin Sharaa ta hau kan mulki shekara ɗaya da ta wuce: "yawan mata a ɓangaren siyasa ya ragu matuka. Yawana mata a kujerun siyasa da hukumomi ya ragu sosai, har ta kai ga yanzu idan aka naɗa mace ɗaya a kan mukami lamarin ya zama lamari da masu goyon bayan gwamnati za su yi murna a kai a kafofin sada zumunta.
An gudanar da zaɓuka kan kujeru 140 cikin 210 na majalisar ƙasar ranar 5 ga watan Oktoba.
A cewar gidan talabijin na Siriya, kashi 14 na ƴan takara 1,500 da ke fafatawa a mazaɓu 50 ne suka kasance mata.
Saboda yanayin tsaro, ba a samu damar yin zaɓe a kujeru 21 cikin 140 ba.
Cikin mambobi 119 da aka zaɓa, shida kaɗai ne ko kuma kashi biyar suka kasance mata. Ana sa ran Ahmed Sharaa zai naɗa mambobi 70 zuwa majalisar dokokin ƙasar.
Da yake mayar da martani kan sukar da ake yi na rashin mata a majalisar, Ahmed Sharaa ya faɗa ranar 1 ga watan Disamba cewa: "maza sun kankane kowane ɓangare kuma mutane ba sa son ganin mata a wasu ɓangarori."

Asalin hoton, Omar Albaw / AFP / Getty Images
Ra'ayin matan Siriya
Buthina Rahal, wadda ta koma garin mahaifarta na Idlib watanni uku da suka wuce bayan shafe tsawon shekara 14 a Turkiyya, yanzu tana da wata cibiya da ke ilmantar da matan Siriya kan sanin hakkokinsu.
Idlib dai ya kasance cibiyar ƙungiyar siyasa na Hayat Tahrir al-Sham lokacin yaƙin basasar ƙasar da ya fara tun 2011.
Da aka tambaye ta kan kalaman Sharaa na baya-bayan nan, Buthina Rahal ta ce, "Ahmed Sharaa ba shi da abin da zai yi nan take. Lokacin da ya karɓi mulki, an riga da an wargaza Siriya baki-ɗaya kuma yanayin rayuwa yayi tsanani. Watakila ba ya son fuskantar duka matsalolin da kuma ƴan adawa a lokaci guda, kuma yana son cigaba a hankali a hankali. Yana buƙatar lokaci."
Sai dai masu fafutukar kare hakkin mata da yawa a Siriya ra'ayinsu ya sha bamban.

Asalin hoton, Alaa al-Muhammad
Mai fafutuka kuma ƴar jarida Alaa Muhamad ta faɗa wa sashen Turkiyya na BBC cewa ta koma Siriya daga Turkiyya ne bayan faɗuwar gwamnatin Assad domin taka rawa a makomar ƙasarta.
A wannan lokaci, ta kasance mai bai wa ministar kwadago da harkokin yau da kullum, Hind Qabvat shawara - ta kasance minista ɗaya tilo a gwamnatin.
Sai dai bayan samun barazanar kisa kan wani sako da ta wallafa a shafukan sada zumunta, lamarin ya tilasta mata sake barin Siriya watanni uku da suka wuce.
Alaa Mohammed na da yaƙini mai kyau kan makomar ƙasarta: "Masu fafutukar kare hakkin mata na cike da damuwar cewa ba za a dama da mata ba kan makomar Siriya."
Me kundin mulkin gwamnatin Siriya ya ce kan mata?
A watan Maris, Ahmed Sharaa ya saka hannu kan wani daftari na kundin mulkin gwamnatin riko na ƙasar, wanda zai yi aiki na tsawon shekara biyar. Kwamitin lauyoyi da masana kimiyya da malaman jami'a da kuma ƴan jarida ne a Siriya suka tsara daftarin.
Daftarin ya nanata cewa tsarin shari'ar Musulunci shi ne matakin shari'a na farko.
Har ila yau daftarin ya ƙara da cewa "ƴan ƙasa na da hakki da doka ya tana da musu, kuma babu wanda za a yi wa wariyar addini, jinsi ko kuma kabila."
Ya kuma ce iyali shi ne "ginshikin al'umma" don haka wajibi ne a kare iyaye mata da yaransu.
Wani rubutu cikin daftarin kundin mulkin ya bayyana cewa: "Mata na da hakkin shiga siyasa don a dama da su, harkokin yau da kullum, tattalin arziki da kuma kare su daga duk wani abu na cin zarafi."
Buthina Rahal ta ce tana da yaƙini gwamnati za ta inganta hakkokin mata a na gaba, inda ta ce: "Ya yi wuri a yanke wa Ahmed al-Sharaa hukunci. Lokaci kaɗan kawai ya shade kan mulki."
Shin dokokin tsarin shari'ar Musulunci za su sauya?
A Siriya, dokoki da suka danganci gado, aure, saki da kuma ikon rike ɗa dukansu na aiki ne kan tsarin shari'ar Musulunci.
A cewar Alaa Mohammed, wannan shi ne "abin da yake yi wa matan Siriya cikas wajen komawa ƙasar."

Asalin hoton, Chris McGrath/Getty Images
Tun lokacin da Ahmed Sharaa ya zo kan mulki, babu abin da ya sauya kan hakkon matan ƙasar.
Hanan Zahraddin ta ce: "A ɓangaren harkokin iyali, namiji shi ne shugaban iyali har yanzu."
Karkashi tsarin shari'ar Musulunci, maza a Siriya suna da damar auran mace fiye da ɗaya, abin da fi yawaita tun lokacin yaƙin basasar ƙasar, kamar yadda majiyoyi suka tabbatarwa BBC.
Ms. Zahreddin ta bayyana cewa maza na da ikon sakin matansu a kowane lokaci suke so, sai dai mata kan nemi saki ne kaɗai idan suka yafe dukkan hakkokinsu.
Ta ƙara da cewa: "Idan mace ta yi niyyar sake aure bayan saki, tana rasa ikon yaranta. Haka kuma, ba a bayar da shaidar ɗan ƙasa daga mahaifiya zuwa yaro."
A ɓangaren rabon gado, maza na da ikon mallakar kashi biyu bisa uku na abin da aka raba, mata kuma kashi ɗaya bisa uku.
Alaa Mohammed ta nuna damuwar cewa mata za su iya rasa ƴan hakkoki da suka rage musu, inda ta ce, "waɗannan abubuwa suna da matsala, sai dai damuwar mu ita ce za a aiwatar da dokoki da za su ƙara musgunawa mata."
"Mata za su iya samun ayyukan sa-kai"
A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, sama da kashi 70 na al'ummar Siriya wanda suka kai mutum miliyan 16, sun dogara ne da kayan agaji.
A wani ɓangare, hakkin nema wa iyali abin da za su ci ya faɗi kan mata, watakila saboda an kashe mazajensu a fagen daga, ko kuma saboda namijin ya bar su ya je ya sake yin aure.
Sai dai mata a wannan yanki na ci gaba da fuskantar matsaloli.
Alaa Mohammad ta ce: "Yayin da maza ke samun ayyukansu da za a biya su, mata kuwa na samun ayyuka ne da ba a biya ko kuma na sa-kai. Mun fuskanci wannan yanayi lokacin neman sauyi."
Ta kuma ce babu damarmaki ga mata, inda ta ce matsaloli na rashin tsaro, ciki har da garkuwa da mutane sun sanya wahala wa mata su samu aiki.
Yaya yanayin tsaron mata yake a Siriya?
A kan titunan Siriya, jami'an tsaro na ɗaukar da suka ga dama a lokuta.
"Mata da ke Damascus da wasu birane da ke tsakiyar ƙasar sun fi samun tsaro da kuma ƴanci idan aka kwatanta da na sauran yankuna. Amma a wasu birane, ɗabi'un dakarun gwamnati a kan tituna ba shi kan tsari," in ji Dalia Haidar, wadda ta yi tafiya daga zuwa Siriya a bara.
Wasu masu fafutukar kare hakkin mata a Siriya waɗanda BBC ta tattauna da su sun ce duk da cewa babu dokar da ke tilastawa mata rufe fuskokinsu, wannan ɗabi'a za ta saka mata cikin matsin lamba kan tituna.
A cewar Alaa Mohammed, wasu mata ƴan kabilar Alawee sun fara saka nikabi da hijabai domin ɓoye addininsu, don fargabar garkuwa.
"A wannan lokaci, akwai ƙarin alamu kan tituna da ke kiran a saka nikabi. Akwai kuma alamu da ke nanata buƙatar a raba maza da mata a motocin haya da gine-ginen gwamnati," in ji Dalia Haidar.

Asalin hoton, Butheina Rahal











