Real Madrid na neman ɗauke Rice daga Arsenal, Tottenham na zawarcin Ndiaye

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta shirya kashe Yuro miliyan 250 kan ɗan wasan tsakiya na Arsenal da Ingila Declan Rice, mai shekara 26, da kuma ɗan wasan Paris St-Germain da Faransa Bradley Barcola, mai shekara 23. (Fichajes)
Tottenham Hotspur ta sanya ido kan ɗan wasan Everton ɗan ƙasar Senegal Iliman Ndiaye, mai shekara 25, amma za ta fuskanci hamayya daga Newcastle United, da Juventus da AC Milan da Atletico Madrid.(TeamTalk)
Chelsea da Tottenham na shirin fafatawa kan zawarcin ɗan wasan Juventus da Canada Jonathan David, mai shekara 25 a watan Janairu. (TuttoMercatoWeb)
Everton na nazarin zawarcin ɗan wasan Midtjylland Franculino Dju, mai shekara 21, a watan Janairu, amma za ta fuskanci hamayya daga Bologna kan ɗan wasan na Guinea-Bissau. (Sun)
Liverpool a shirye take ta bayar da Yuro miliyan 100 don siyan ɗan wasan Italiya Alessandro Bastoni, mai shekara 26, daga Inter Milan. (Il Giorno)
Barcelona na zawarcin ɗan wasan Crystal Palace da Colombia Daniel Munoz, mai shekara 29 (Mundo Deportivo).
Real Madrid da Barcelona suna zawarcin ɗan wasan gaban Levante Etta Eyong, mai shekara 22, sai dai ɗan wasan na Kamaru ya bayyana burinsa na buga wa Chelsea wasa a gasar Premier. (Givemesport)
Atletico Madrid ta ayyana ɗan wasan baya na Real Madrid Ferland Mendy, mai shekara 30, a matsayin wanda ke kan gaba a jerin ƴan wasan da ta ke zawarci, yayin da ɗan wasan na Faransa ke fama da rashin tagomashi a filin wasan Bernabeu. (El Nacional.cat)
Kocin Manchester United Ruben Amorim na iya ƙoƙarin ƙara ƙaimi wajen neman ɗan wasan gaba a watan Janairu idan har ɗan wasan gaban ƙasar Slovenia Benjamin Sesko mai shekara 22 ya kasa warke wa daga raunin da ya ji a gwiwarsa, yayin da ya kocin ke fuskantar rasa ɗan wasan Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 26, da Amad Diallo na Ivory Coast, mai shekara 23, a gasar cin kofin nahiyar Afrika. (Mirror)











