Arsenal da Real Madrid na hamayya kan Yildiz, Man City na bibiyar El Mala

Kenan Yildiz

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal da Chelsea da Real Madrid na shirin shiga yaƙin neman sayen ɗan wasan Juventus Kenan Yildiz bayan an kasa samun ci gaba a tattaunawar tsawaita kwantiragin ɗan ƙasar Turkiyya mai shekara 20 da ƙungiyar taTurin. (Caughtoffside)

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya nuna sha'awarsa kan ɗan wasan Cologne ɗan ƙasar Jamus Said El Mala, mai shekara 19. (Sky Sports Germany).

Nottingham Forest ba za ta yi tunanin sayar da ɗan wasan tsakiya na Ingila Elliot Anderson a kasuwar musayar ƴan wasa mai zuwa ba sannan ta na ganin darajar ɗan wasan mai shekara 23 ta kai sama da fam miliyan 100, a daidai lokacin da Manchester United da tsohuwar ƙungiyarsa Newcastle ke zawarcin ɗan wasan (Telegraph).

Ɗan wasan tsakiya na Wolves Joao Gomes a shirye ya ke ya koma Manchester United, inda ake tunanin tayin fam miliyan 44 zai iya jan hankalin ɗan ƙasar Brazil mai shekara 24 ya bar Molineux a watan Janairu. (Record).

Manchester United ba za ta ƙarfafa ɓangaren ƴan wasan tsakiyarta a watan Janairu ba, kuma za ta haƙura har zuwa bazara mai zuwa lokacin da za ta matsa ƙaimi wurin zawarcin ɗan wasan Brighton da Kamaru Carlos Baleba da ɗan wasan Crystal Palace Adam Wharton na Ingila, mai shekara 21, da kuma ɗan wasan Stuttgart ɗan ƙasar Jamus Angelo Stiller mai shekara 24 .(ESPN).

Fatan Liverpool na sayen Antoine Semenyo, mai shekara 25, daga Bournemouth a watan Janairu na fuskanytar ƙalubale, inda Cherries ba ta son sayar da ɗan wasan na Ghana a kakar wasa ta bana. (Teamtalk).

Ɗan wasan gaban Jamus Niclas Fullkrug, mai shekara 32, na shirin barin West Ham a watan Janairu kuma yana tattaunawa da ƙungiyoyi a Bundesliga. (Fabrizio Romano).

Tsohon ɗan wasan Brentford Ivan Toney na shirin ci gaba da zama a ƙungiyar Al-Ahli ta Saudi Pro League duk cewa ɗan ƙasar Ingilan mai shekara 29 na jan hankalin Tottenham da Everton da kuma West Ham. (Football Insider).

Ɗan wasan tsakiya na Atletico Madrid da Ingila, Conor Gallagher, ya ce ba zai bar kulob ɗin na La Liga nan gaba ba, ya kuma ce ya na matuƙar farin ciki da zaman da ya ke yi a babban birnin ƙasar Sifaniya, duk da cewa ana alaƙanta shi da Manchester United. (AS).

Bajintar da ɗan wasan gaba na AZ Alkmaar Troy Parrott yayi da jamhuriyar Ireland ta sanya ƙungiyoyin Premier da dama suna rububin tsohon ɗan wasan Tottenham mai shekara 23. (Times)