Shin Birtaniya za ta iya jure yaƙi mai tsawo da Rasha?

A treated image of a soldier holding a gun
    • Marubuci, Frank Gardner
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Tsaro
  • Lokacin karatu: Minti 6

A daidai lokacin da ya rage ɗan lokaci kaɗan yaƙin Ukraine ya shiga shekara biyar da farawa, ƙasashen Turai na fuskantar matsin lamba da barazana kan abubuwan da ka iya faruwa.

A Birtaniya, manyan hafsoshin tsaro sun yi gargaɗin cewa idan suna so su guje wa yaƙi, dole su fara shirin yaƙin. Amma idan yaƙin ya ɓarke da Rasha, shin Birtaniya za ta iya jurewa ko da na mako ɗaya tana yaƙin?

"Ba mu da burin ƙaddamar da yaƙi kan ƙasashenTurai. Amma idan suna son yaƙin, mu a shirye muke," in Shugaban Rasha Vladimir Putin ranar 2 ga Disamba, inda ya zargi ƙasashen Turan da daƙile shirin Amurka na samar da zaman lafiya a Ukraine.

Sai dai a bayyane yake cewa zai yi wahalar gaske Birtaniya ta fafata yaƙi ita kaɗai ba tare da gudunmuwar ƙasashen ƙungiyar Nato ba.

'Ba ma yunƙurin ƙaddamar da yaƙi da turai, amma idan sun shirya, to muma a shirye muke," in ji Putin.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, 'Ba ma yunƙurin ƙaddamar da yaƙi kan Turai, amma idan sun shirya, a shirye muke," in ji Putin

Akwai hanyoyin yaƙi da dama a yanzu. Bayan amfani da bamabamai da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa, akwai kuma hanyoyin amfani da kimiyya da fasaha.

Aikin sirri da Rasha ke yi ta hanyar amfani da jami'an sirri irin su Yantar ya taimaka wajen lalata wasu wayoyin ƙarƙashin ƙasa waɗanda ke jawo tsaiko ga ƙasashe da dama a yaƙin zamani, wanda hakan ya sa sojojin ruwan Birtaniya suka fara aikin haɗa jirage marasa matuƙa da za su riƙa aiki a ƙarƙashin ruwa.

Manyan hafsoshin Birtaniya sun ce domin guje wa yaƙi, dole a shirya wa yaƙin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Manyan hafsoshin Birtaniya sun ce domin guje wa yaƙi, dole a shirya wa yaƙin

A wani taron ƙara wa juna sani kan yaƙi da aka yi a Landan, wanda cibiyar Royal United Services Institute (Rusi) ta shirya, masana harkokin tsaro da siyasa sun haɗu domin tattaunawa kan shin rundunar tsaron Birtaniya ta yanzu za ta iya jure yaƙi mai tsawo.

"Babu tabbacin ko Birtaniya za ta iya makonni yana cikin yaƙi a yanzu," in ji Hamish Mundell na Rusi.

Ya ƙara da cewa idan kana so ka shiga yaƙin da za a daɗe ana gwabzawa, dole kana buƙatar shiri sosai.

Sojin ƙasa na Rasha

Rundunar sojin ƙasa na Rasha na cikin runduna marasa inganci, sojojinta ba su da ƙwarewa sosai.

Sashen tattara bayanan sirrin Birtaniya ya ƙiyasta cewa tun bayan ƙaddamar da yaƙin Ukraine a watan Fabrailun 2022, Rasha ta yi rashin kusan sojoji miliyan 1.1 waɗanda ko dai aka kashe ko suka ji rauni ko aka kama.

Waɗanda aka kashe sun kai aƙalla mutum 150,000, amma Ukraine ma ta yi rashi sosai, sai dai babu alƙaluman da suke nuna adadinsu.

Haka kuma tattalin arzikin Rasha na fuskantar matsala na tsawon shekara uku da suka gabata.

A wani rahoto da cibiyar tattalin arziki na Kiel, ya nuna cewa Rasha na haɗa tankokin yaƙi kusan 150 da motocin yaƙi aƙalla guda 550 a jirage marasa matuƙa kusan a duk wata.

Birtaniya da ƙawayenta na turai babu ƙasar da take kusa da Rasha a irin wannan shirin.

Masana sun ce ƙasashen turai za su kwashe shekaru da dama kafin su zo kusa da Rasha wajen haɗa makamai.

Ukraine ta yi asarar sojoji da dama, amma da wahala a iya taskancewa

Asalin hoton, EPA/Shutterstock

Bayanan hoto, Ukraine ta yi asarar sojoji da dama, amma da wahala a iya tantance adadinsu

Tattaunawa tsakanin ƙasashe

Faransa da Jamus sun fara yunƙurin dawo da aikin soji na sa kai ga ƴan ƙasar da suka kai shekara 18.

Tsohon babban hafsan sojin ƙasan Birtaniya, Janar Sir Patrick Sanders ya ce a shekarar da ya yi ritaya daga aiki a shekarar 2024 ne ya kamata Birtaniya ta fara horar da ƴan ƙasar aikin soja domin shirin fuskantar yaƙi a gaba.

"Muna da tsarin tun a tsakankanin shekarun 1960, amma yunƙurin mayar da shi dole bai samu karɓuwa ba."

Faransa ya yunƙurin dawo da dokar aikin soja na sa kai ga ƴan shekara 18 a ƙsar

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Faransa ya yunƙurin dawo da dokar aikin soja na sa kai ga ƴan shekara 18 a ƙasar

"Mun ƙara kuɗin da muke kashewa a ɓangaren tsaro zuwa fam biliyan biyar a bana, sannan mun shiga yarjejeniya guda 1,000 tun bayan zaɓe, sannan mun ƙara kuɗin da ma'aikatar tsaro ke kashewa da kashi 6 daga abin da aka kashe a bara," in ji kakakin sakatariyar tsaro ta Birtaniya, John Healey.

Ya nuna yarjejeniyar da suka shiga da ƙasar Norway, inda aka tsara zuba fam miliyan 300 domin samar da makaman sojojin ruwa da kuma fam biliyan tara domin samar da gidaje.

Ita ma Jamus ta fara aiki da dokar aikin soja ga ƴan shekara 18

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ita ma Jamus ta fara aiki da dokar aikin soja ga ƴan shekara 18

Amma wannan ba batu ne na siyasar jam'iyyar Labour, batu ne na tsaron Birtaniya da kuma maganar ko dai ba a zuba wa ɓangaren tsaron ƙasar kuɗin da ya dace ne da har ta kai matakin da take fuskantar barazana, musamman ta sama.

A ƙarshen yaƙin ƙasashen Nato da dakarun Soviet a shekarar 1990, lokacin da nake ƙaramin sojan ƙasa, Birtaniya na kashe kashi 4.1 ne na kuɗin shiga na cikin gida a ɓangaren tsaro.

A shekarar da ta biyo baya kuma, ta tura sojoji 45,000 domin hana sojojin Saddam Husseini samun nasarar kutsawa zuwa Kuwait.

Birtaniya na fuskantar yaƙi?

Wasu masu sharhi suna ganin Birtaniya ta riga ta fara yaƙi da Rasha, inda suke nuni da abubuwan a suke faruwa a bayan fage kamar kutse ta intanet da yaɗa bayanan bogi da zargin aiki jirgi mara matuƙi kusa da bakin iyakar shiga ƙasashen Nato.

Amma abin da zai fi tayar da hankali shi ne idan Rasha ta ƙaddamar da hari kan ƙasar Nato, musamman idan yaƙin ya ƙunshi ƙwace wasu iyakoki da kashe mutane.

Akwai abubuwan da ake fargaba a game da yaƙin, inda manyan hafsoshin ƙasashen Nato suke fargabar idan Putin ya samu damar samun abin da yake so a Ukraine, zai ci gaba da faɗaɗa abin da yake yi.

Wani abu da yake so shi ne yankin Suwalki, bakin iyaka mai tsawon kusan mil 60 da ke tsakanin Poland da Lituania waɗanda duk ƙasashe Nato ne.

Jirgin yaƙin Typhoon

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jirgin yaƙin Typhoon

Haka kuma akwai ƙasashen Baltic ma suna fuskantar barazana, inda akwai ƙasasshen Estonia da Latvia da Lithuania da suka kasance a baya ƙarƙashin mulkin Soviet.

Sun zaɓi warewa ne daga baya, sannan suka shiga ƙungiyar Nato, amma har yanzu suna da mutane masu magana da harshen Rasha, wanda hakan ya sa ake fargabar akwai yiwuwar Putin zai iya tura sojoji domin a kare su daga "muzgunawa."

Misali akwai birnin Narva da ke Estonian, wanda mafi yawanta da harshen Rasha suke magana.

Wani yankin da ke fuskantar barazana shi ne Arctic archipelago na Svalbard da ke ƙarƙashin gwamnatin Norway amma yake gab da Rasha.

Birnin Narva

Asalin hoton, AFP via Gettty Images

Bayanan hoto, Birnin Narva

Birtaniya ta Rasha

Akwai yiwuwar Birtaniya ta zama babbar abokiyar adawar Putin kasancewar ita ce kan gaba wajen goyon bayan Ukraine, sannan take kira da a ba Zelensky manyan makamai domin kare ƙasarsa.

Akwai abubuwa da suka faru a Birtaniya da ake alaƙantawa da Putin, ciki har da amfani da sinadarin Polonium-210 wajen kashe Alexander Litivinenko a Landan a shekarar 2006, sannan bincike ya yi zargin akwai yiwuwar Putin ne ya bayar da umarnin kisan, da kuma yunƙurin kashe tsohon jami'in tattara bayanan sirri na Rasha Sergei Skripal a Salisburry a 2018.

Haka akwai Dawan Sturgess mai ƴaƴa uku da ta mutu bayan fesa turaren Novichok, lamarin da bincike ya nuna "akwai hannun Rasha."

Sai dai Rasha ta musanta a hannu a duk abubuwan da ake zarginta.

Putin ya zargi ƙasashen turai da kawo tsaiko a yunƙurin Amurka na tabbatar da zaman lafiya a Ukraine

Asalin hoton, Sputnik/ AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Putin ya zargi ƙasashen turai da kawo tsaiko a yunƙurin Amurka na tabbatar da zaman lafiya a Ukraine

Sai dai Birtaniya na cikin na gaba-gaba a ƙasashen Nato, sannan duk da cewa akwai kokwanto kan taimakon da Amurka za ta iya yi a gwamnatin yanzu, lallai akwai tabbacin ba zai yiwu ba Birtaniya ta yi yaƙi ita kaɗai da Rasha.

Duk da cewa shugaban kwamitin soji na Nato Adm Cavo Dragone ya tabbatar a kwanakin baya cewa shugaban Amurka a shirye yake ya ba ƙasashen Nato kariya, wasu na shakku kan iƙirarin.

Misali, shin zai yiwu Trump ya shiga yaƙi kawai domin ya kare birnin birnin Narva da ke ƙasar Estonia?

Akwai hotuna daga ma'aikatar tsaro da PA Wire da Getty Images.