Me ya sa mawaƙan Kudancin Najeriya suka fi na Arewa ɗaukaka?

.

Asalin hoton, Others

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

A daidai lokacin da mawaƙan Kudancin Najeriya suke gasar halartar manyan tarukan duniya, tare da shirya tarukan kalankuwa a ƙasashen duniya, takwarorinsu na Arewacin ƙasar har yanzu fafutikar samun karɓuwa suke yi, lamarin da masana suka ce bai rasa nasaba da yanayin harshe da al'ada da addini.

Zamani ya zo da sauye-sauye a ɓangaren waƙoƙi a Najeriya, musamman a Arewacin ƙasar, inda ake samun matasa suna tuttuɗa suna baje fasaharsu.

A da can, an fi samun mawaƙan sana’o’i da na sarakuna da wayar da kan al’umma, kafin daga bisani aka fara waƙoƙin siyasa da nishaɗi.

Masana’antar Kannywood ta taimaka wajen ƙara ɗaukaka waƙoƙin Hausa a Arewa, inda ta fitar da gwarazan mawaƙa fasihai.

Sai dai wani da abu da ke haifar da muhawara a tsakanin ma’abota waƙoƙin shi ne shin mawaƙan Arewa suna cin moriyar fasaharsu kamar na Kudu da sauran sassan duniya?

Ko a YouTube ma, BBC ta lura an yi wa mawaƙan na Arewa zarra. Misali, waƙar 'Buga' ta mawaƙi Kiz Daniel ta aka fitar a ranar 22 ga Yunin 2022 tana da masu mallo 220,142,316.

Mawaƙan Kudancin Najeriya da suka halarci manyan tarukan duniya

Rema

..

Asalin hoton, Rema/Facebook

Sunansa Divine Ikubor amma an fi sanin sa da Rema harkar waƙoƙin gambara.

Rema ya halarci taron karrama gwarazan ƴan ƙwallon ƙafa ta Ballon d’Or wanda aka yi a ranar 30 ga Oktoban 2023, inda ya rera waƙasar ta ‘Calm Down’.

Shi ne mawaƙin Najeriya na farko da aka fara gayyata a tarihin taron.

Tiwa Savage

..

Asalin hoton, Tiwa/Facebook

Sunanta Tiwatope Omolara Savage da aka fi sani da Tiwa mai shekaru 44 kuma mawaƙiya ce kuma jarumar fina-finan Nollywood.

Ta shahara a fagen zuben waƙoƙi na Afirka da kuma gambara.

Tiwa ta halarci bikin naɗa Sarkin Ingila, Sarki Charles III.

Burna Boy

..

Asalin hoton, Burna boy/Facebook

Shi kuma mawaƙi Damini Oguku, wanda aka fi sani da Burna Boy ya halarci ƙaddamar da Gasar Chamions League na Turai da aka yi a Filin Wasa na the Ataturk Olympic Stadium da ke Turkiyya a 10 ga watan Yunin 2023.

Bayan wannan kuma mawaƙan Kudu suna shirya tarukan kalanluwa a ƙasashen duniya.

David Adeleke wanda aka fi sani Davido ya taɓa halartar taron karrama ƴan ƙwallo na Ƙungiyar Ƙwararrun ƴan ƙwallo karo na 50 a birnin Manchester a ranar 29 ga Agustan 2023.

Shi ma Ayodeji Balogun wanda aka fi sani da Wizkid ya shirya taron kalankuwa a filin wasa na Tottenham Hotspur da ke London, a ranar 29 ga Yulin 29, 2023. Taron ya samu mahalarta 45,000.

Me ya sa ake barin mawaƙan Hausa a baya?

Abubakar Sani, fitaccen mawaƙi ne a Kannywood wanda za a iya cewa ya ga jiya, ya ga yau a waƙa.

A cewarsa, “Asali a Kudu waƙoƙin Yarbanci muka sani. A zamanance kuma gaskiya kowa da ɗauki ɓangarensa, mun ɗauki salo na nanaye kasancewar yawancin waƙoƙinmu na fina-finai ne. Sai daga baya muka fara CD."

Ya ce har yanzu mawaƙa a Arewa ba su samu karɓuwa sosai ba, wanda a cewarsa ya taimaka wajen fara kawo wa harkar tsaiko.

“Ba a kallon gudunmuwar da muka ba harshen. Waƙoƙi da fina-finai da marubuta sun ba harshen gudunmuwa sosai. Amma a Arewa ne mawaƙi zai taimaka a siyasa, bayan an gama kamfe da shi idan ba a yi sa’a ba, sai ka ga an ɗauko mawaƙin Kudu a ranar ƙaddamar da shi,” in ji shi, inda ya ce su mutanen Kudu suna ba mawaƙansu taimakon da suke buƙata.

.

Asalin hoton, Abubakar Sani/ Facebook

Ra'ayin Ibrahim Sheme

..

Asalin hoton, Ibrahim Sheme/Facebook

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Domin jin ko me ya sa hakan ke faruwa, BBC ta tuntuɓi Malam Ibrahim Sheme, wanda masani ne a kan harkokin Kannywood da fina-finai, inda ya ce yanayin harshen na cikin abubuwan da suka jawo hakan.

A cewarsa, “Yawanci mawaƙa ne na Hausa shi kuma Hausa harshe ne na wasu ba gama-gari ba.”

Sai dai ya ce ko a Kudun akwai waƙoƙin Yarbawa da na Ibo, waɗanda ya bayyana cewa ba sa yin tasiri kamar na turancin.

“Ko a irin su YouTube masu amfani Turanci sun fi samun kuɗi a kan na Hausa. Shi ya sa ake gayyata na Turanci saboda su aka fi sani sannan sun fi mu wayewa da shiga wurare. Misali muna da mawaƙa a Turai irin su Chizo Germany da Bello Cisko amma an fi sanin na Turancin fiye da su. Turanci yare ne duniya.”

Shi ma Dokta Muhsin Ibrahim, malami a jami’ar Cologne da ke Jamus ya bayyana cewa lamarin bai rasa nasaba da addini da al’ada.

“Akwai abubuwan da aka saba gani a waƙoƙin duniya na yadda maza da mata suke haɗuwa ko yanayin saka kaya. Mu irin wannan ana ƙoƙarin kiyayewa duk da cewa ba ina nufin wanda ake yi sun dace da doron addini ba, amma hakan ya rage sha’awar waƙoƙin a kasuwannin duniya. Sai kuma inganci, inda wataƙila ba kowa ba ne a cikinsu ke da kuɗin da zai iya kashewa ya yi mai inganci sosai ba misali wajen kyamara da ɗauko darakta da furodusa manya.

“Kuma a Arewacin Najeriya babu masu hada-hada da tallata harkokin nishaɗi yadda ya kamata kamar Legas.”

Me ya kamata su yi?

A game da yadda za a yi domin mawaƙan su fara kai wa matakin duniya, Ibrahim Sheme cewa ya yi, “Su riƙa yin waƙoƙi da Turanci suna haɗa wa da na Hausa. Misali idan mutum ya yi na Hausa biyar, sai ya yi na Turanci ɗaya.”

Shi kuma Abubakar Sani cewa ya yi, “A da mukan yi CD guda miliyan 10 ko 20 har zuwa miliyan 100. Ka lissafi min a wancan lokacin muna bayar da sari a Naira 50. Ka lissafa Naira 50 sau miliyan 1 ka gani. YouTube kuwa kafin ka fara samun kuɗi akwai wahala, sannan ga rashin tsari. Wani sai ya saci waƙata ya ɗora, idan na ɗauko na saka a tawa tashar sai a rufe tawa."

Ya kuma yi kira da abokan sana’arsa da su gyara harshe, sannan su riƙa karatu da bincike.

“Ina yawan misali da waƙar Abubukar Liman ta Allah ya Allah ya Allah, haɗa kanmu Arewa mu so juna. Ka ga babu kiɗa amma har yanzu idan kana sauraronta, za ka ji tana taɓa ka. Sannan gwamnati ta taimake mu a gyrar harkar a yi wata tsangaya da za a riƙa bayar da ko da ƙaramar difloma ce.”