Tashar WhatsApp ta BBC Hausa: Yadda za ku shiga domin samun labarai

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labarai da dumi-duminsu daga BBC Hausa ta shafin WhatsApp.
Ma'aikatanmu na iya kokarinsu don kawo muku labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Tun shekarar 2023, WhatsApp ta fara barin masu amfani da manhajar samun bayanai da kuma labarai daga manyan kamfanonin da suke so. Tun watan Satumbar shekarar 2023 aka bude tashar WhatsApp ta sashen Turanci na BBC a Burtaniya, kuma ta samu mabiya miliyan 1.3.
Yanzu abokan hulɗarmu daga ƙasashen Afrika su ma za su iya samun labarai daga BBC Hausa a wayoyinsu.
- Danna nan don shiga shafin namu na Whatsapp idan kuna amfani da wayoyinku ko Whatsapp a kan kwamfutocinku.
- Kuna kuma iya nemo BBC News Hausa a ƙarkashin maɓallin "updates" da ke WhatsApp.
Za ku iya samun "updates" a hannun hagu idan kuna amfani da wayoyin Iphone, idan kuma kuna amfani da Android, ku duba hannun dama a manhajar ta WhatsApp.
Za ku iya saka alamomin yadda kuka ji bayan samun labaran namu ta hanyar amfani da emojis karkashinsu.
Meta ta ce ba wanda zai iya samun bayananku ko ganin lambobinku ta tashar.
Za ku iya samun karin bayanai kan yadda za mu tsare muhimman bayananku a tashar ta Whatsapp a nan

Asalin hoton, GETTY











