Inter da Man United na neman Adeyemi, Ake na tunanin barin Man City

Asalin hoton, Getty Images
Inter Milan da Manchester United sun fara tattaunawa da wakilan Karim Adeyemi, a daidai lokacin da ɗan wasan na Jamus mai shekara 23 ya shirya barin Borussia Dortmund. (Bild).
Ɗan wasan bayan Netherlands Nathan Ake, mai shekara 30, yana daya daga cikin ƴan wasan Manchester City uku da ke nazari kan makomarsu kafin a buɗe kasuwar musayar ƴan wasa ta watan Janairu. (Mail).
Crystal Palace ta yi imanin cewa Liverpool ce kaɗai za ta iya ƙoƙarin siyan Marc Guehi, mai shekara 25, a watan Janairu, yayin da ɗan wasan na Ingila zai kasance mai zaman kansa a bazara mai zuwa. (Sky Sports).
Ɗan wasan gaba na Al-Ahli da Ingila Ivan Toney a shirye ya ke ya matuƙar rage albashinsa don komawa gasar Premier a watan Janairu, inda Tottenham da Everton ke zawarcin dan wasan mai shekara 29. (Teamtalk).
Manchester United za ta ci gaba da zawarcin ɗan wasan Real Madrid da Faransa Aurelien Tchouameni, mai shekara 25, duk da cewa kulob ɗin na Sifaniya ya ƙi amincewa da tayin Yuro miliyan 90. (Fichajes).
Napoli na da jerin sunayen ƴan wasa da za ta iya ɗauka a watan Janairu a madadin ɗan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, amma ɗan wasan na Manchester United, mai shekara 20, ya kasance zabinta na farko. (La Gazzetta dello Sport).
Juventus ta fara tattaunawa da ɗan wasan bayan Lecce Tiago Gabriel, mai shekara 20, duk da cewa Brentford ma na sa ido kan ɗan wasan na Portugal na ƴan ƙasa da shekara 21. (Tuttosport).
Atletico Madrid dai ta kwashe watanni tana sa ido kan ɗan wasan bayan Chelsea da Sifaniya Marc Cucurella, kuma ta na tunanin miƙa tayin Yuro miliyan 40 kan ɗan wasan mai shekara 27. (Fichajes).
Besiktas na shirin ɗaukar golan Barcelona da Jamus Marc-Andre ter Stegen, mai shekara 33, a matsayin aro. (Sport).
Tottenham Hotspur na neman siyan gogaggen gola a watan Janairu. (Mail).











