Me ƙasashen yankin Gulf suke nema daga tattaunawar Amurka da Iran?

    • Marubuci, بخش مانیتورینگ
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, بی‌بی‌سی
  • Lokacin karatu: Minti 5

Hankali ya fara kwantawa tsakanin ƙasashen Yankin Gulf (GCC) yayin da Amurka da Iran suka amince da tsagaita wutar makwonni biyu a ranar 8 ga watan Afrilun. sanarwar na nufin Iran zata dai na kaiwa gine ginen farar hula da sojoji hare-hare a waɗannan ƙasashe.

Buƙatar ƙungiyar ƙasashe membobin yankin Gulf ita ce a cimma matsaya mai ɗorewa wadda zata bayar da damar wucewar jiragen ruwa ta mashigin Hormuz ba tare da wata matsala ba.

Amma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta yi Allah Wadai da Tehran da kakkausar murya. Ita kuwa Oman kai tsaye ta soki Washington ba tare da fargaba ba sannan ta gayyaci Tehran don tattaunawar kai tsare.

Abin tambaya shi ne, ko ƙulla yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran zata samar da sakamakon da Hukumar Ƙasashen ƴankin Gulf ke buƙata?

Qatar

Qatar ta mayar da hankali wajen hanyoyin da za a bi wajen rage rikici da samar da hadin kai tsakanin ƙasashen yankin da kuma kare yadda ake safarar makamashi tsakanin ƙasashen duniya.

Majid Al-Ansari, kakakin Ma'aikar Harkokin Wajen Qatar ya shaidawa ƴan jarida cewar a ranar 14 ga watan Afrilu abinda ya fi muhimmanci a wurin Doha shi ne ''mayar da tsagaita wuta zuwa zaman lafiya na din-din-din.''

Ɗaya daga cikin buƙatun Qatar shi ne samar da ingantaccen tsaro a hanyoyin ruwa. Mista Ansari ya bayyana ''muhimmancin kasuwanci ta mashigin Hormuz ga ƙasashen duniya'' da kuma bukatar a yi watsi da amfani da mashigin Hormuz wajen matsin lamba da yin barazana.

A wani taron ganawa da manema labaran da aka gudanar ranar 21 ga watan Afrilu kuwa, ya ce dukkan ƙasashe na da damar amfani da mashigin Hormuz.

Qatar ta goyi bayan tattaunawar sulhu wadda Pakistan ke shiga tsakani.

Saudiyya

Daga cikin muradin Saudiyya na shekara ta 2030, akwai batun mai wanda shi ne ƙashin bayan tattalin arziƙin ƙasar.

Rikicin zai iya haifarwa muradun Saudiyya tarnaƙi.

Kodayake yaƙin ya fito da gazawar wata yarjejeniya tsakanin Saudiyya da Iran da aka ƙulla a shekara ta 2023 wadda Chaina ta jagoranta, amma alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu na nan daram.

Rahotannin sun bayyana yadda Yarima Mohammed bin Salman ya goyi bayan harin da Washington ke kaiwa Iran.

A shekara ta 2018 ne Yarima Mohammed bin Salman ya yi gargaɗi idan Iran ta mallaki makamin nukiliya, Saudiyya ma zata yi gaggawar mallakar nata.

Ɗaya abinda dake ciwa Riyadh tuwo a ƙwarya shi ne yadda Iran ta ke samun goyon baya daga waje musamman daga ƴan tawayen Houthi da ke Yemen mai maƙotaka.

Idan Yan Houthi suka rufe mashigin Bab al-Mandab kamar yadda suke barazana, babu shakka ƙasar ta yankin Gulf zata rasa muhimmiyar hanyar fiton mai.

Bahrain

Bahrain ta bayyana farin cikin ta da tsagaita wuta a mashigin Hormuz. Ta kuma yi kira a gaggauta dakatar da hare-hare.

Ranar 8 ga watan Afrilu Ma'aikatar Harkokin Wajen Bahrain ta jaddada buƙatar ɗaukar matakan da suka dace don hana Tehran mallakar makamin nukiliya sannan kuma a hana ta ci gaba da shirinta na ƙirƙirar makamai.

Bahrain ta yi kira ga Tehran ta biya diyyar gine-ginen da ta rusa da kuma rayukan da ta kashe cikin gaggawa.

Kuwait

Ita ma Kuwaita ta yi murna da batun tsagaita wuta a ranar 8 ga watan Afrilu, inda ta goyi bayan shiga tsakani wanda ta ce zai iya samar da yarjejeniya mai ɗorewa da zata daidaita tsaron yankin.

Kuwait ta yi kira ga Iran da ƙawayenta na bayan fage su mayar da takubban su cikin kube, su mutunta ƴancin ƙasashe sannan su guji abinda zai haifar da rashin tsaro a yankin.

Kuwait ta kuma yi Allah wadai da yadda Iran ke amfani da makamai masu dogon zango da kuma jirage marassa matuƙa wajen kaiwa gine-gine hari a yankin Gulf.

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

Daga cikin ƙasashen yankin Gulf, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ɗauki wani matsayi mai tsauri na sukar Iran a fili, ta zargi Tehran da tayar da rikici kuma ta yi watsi da iƙirarin da Iran ta yi cewar ta na mayar da martanin tsokanar da aka yi mata ne.

Abu Dhabi ta nemi a kawo ƙarshen yaƙin tattalin arziƙi a Iran da kama jirage a mashigin Hormuz.

Anwar Gargash mai baiwa shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa shawara ya nemi Iran ta biya diyya cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar 29 ga watan Maris.

Abu Dhabi ta yi barazanar goyon bayan Amurka wajen karɓe mashigin Hormuz da kuma fuskantar gwamnatin da ta zamarwa ƙasashen yankin Fasha barazana.

Oman

Oman ta jima da tarihin shiga tsakanin Washington da Tehran ta hanyar amfani da diflomasiyya wajen kawo ƙarshen rikici.

Muscat ta ɗauki mataki mai tsauri kan Amurka tsakanin ƙasashen Yankin na Gulf, inda Ministan Harkokin Wajen Oman Badr Busaidi bayan Amurka da Isra'ila sun kaiwa Iran hari ya bayyanawa Washington rashin jin daɗi sakamakon karya yarjejeniya da Washington ta yi.

Ya bayyanawa Amurka cewar: ''Wannan ba yaƙin ki ba ne.'' yayi wannan jawabi ne lokacin da ake cece-kuce cewar Isra'ila ce ta sa Donald Trump ya kaiwa Iran hari.

Oman ta yi farin ciki da batun tsagaita wuta amma ta nemi ''a kawo ƙarshen yaƙi'' gabaɗaya a yankin.

Kafafen yaɗa labarai sun bayyana cewar Oman da Iran na aikin haɗin gwiwa wajen sanya ido kan jiragen da suke zirga zirga a mashigin Hormuz.

A ranar 4 ga watan Afrilu ne manyan jami'an Oman da Iran suka tattauna yiwuwar fara zirga zirgar jiragen ruwa a hanyoyin ruwa.