Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da naɗin Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar bayan ta tantance shi.
A ranar 22 ga wannan watan ne gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya miƙa sunan Murtala Garo ga majalisar.
Mataimakin kakakin majalisar Hon. Muhammad Bello Butubutu wanda ya tabbatar wa da BBC amincewar, ya ce sun tabbatar da cewa Garo ɗan asalin jihar Kano ne, kuma ya yi karatu har matakin HND wanda ya kai ya riƙe muƙamin, hakazalika sun tabbatar ya kai shekarun zama mataimakin gwamna.
Ya kuma ce sun tabbatar Murtala Sule Garo na da gogewar da zai iya zama mataimakin gwamna domin a baya ya zama shugaban ƙaramar hukuma, da kwamishinan ma'aikatar kula da kananan hukumomi, hakazalika ya taɓa yin takarar neman zama mataimakin gwamna.
Hon Muhammad Bello ya ce bayan sun tabbatar da hakan, ya gabatar da rahotonsa a zauren majalisar, inda aka bayar da damar yin tambayoyi ko kalubalantar rahoton, sai dai ba a samu wanda ya kalubalanci rahoton ba wanda ke nufin an amince da shi.
Zaɓen sabon mataimakin gwamnan dai na zuwa ne bayan murabus ɗin da tsohon mataimakin gwamna Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi a ranar 27 ga watan Maris ɗin 2026.
Wannan dai ya samo asali ne sakamakon sauye-sauyen sheƙa da aka samu tsakanin gwamnan da mataimakinsa da wasu 'yan majalisar jihar da sauran masu ruwa da tsaki cikin gwamnatin.