Sojojin Mali na janyewa daga yankin Tessit

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Rahotanni daga Mali na cewa sojojin ƙasar na janyewa daga garin Tessit da ke arewa maso gabas, yayin da masu ta da ƙayar baya ke ƙara zafafa kai hare-hare bayan wani sabon farmaki da suka kaddamar a ƙarshen mako.
A cewar wakilin BBC, Arewacin birnin Kidal da Kudancin yankin su ne inda aiyukan ƴan tada ƙayar bayan yafi mamayewa a Mali.
Wata ƙungiya mai alaƙa da Al-Qaeda ta ce ta bai wa sojojin damar ajiye makamansu tare da barin yankin lami lafiya.
Wannan ya biyo bayan janyewar Rundunar sojojin hayan Rasha da ke aiki a Afirka daga garin Kidal da ke yankin arewacin ƙasar, tare da sojojin Mali.
Sojojin ƙasar sun ƙwace garin shekaru uku da suka gabata tare da taimakon Rasha. Kawo yanzu dai gwamnatin mulkin sojin Mali ba ta yi tsokaci kan lamarin ba.

















