Me ya sa Ƙatar ta kasa dakatar da yaƙin Isra'ila da Hamas duk da ƙwarewarta kan hakan?

Ƙaramin Ministan Harkokin Waje na Ƙatar Sultan Saad al-Muraikhi lokacin da yake halartar wani taro a Jordan kan kawo ƙarshen yaƙin Gaza

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙaramin Ministan Harkokin Waje na Ƙatar Sultan Saad al-Muraikhi lokacin da yake halartar wani taro a Jordan kan kawo ƙarshen yaƙin Gaza
    • Marubuci, Jeremy Howell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 4

Gwamnatin ƙasar Ƙatar ta bayyana cewa za ta janye daga yunƙurin shiga tsakani domin ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Isra'ila da Hamas saboda rashin mayar da hankali daga kowane ɓangare.

Sannan rahotonni na cewa Amurka na matsa mata domin ta rufe ofishin ƙungiyar ta Hamas da ke Doha babban birninta.

Ƙaramar ƙasar mai arziki ta tsaga wa kanta shahara a matsayin mai samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, amma kuma tana shan fama wajen yin hakan a wannan karon.

Ta yaya Ƙatar ta zama babbar mai samar da zaman lafiya?

Ƙatar ƙaramar ƙasa ce a yankin Tekun Fasha (Persian Gulf) da ke da faɗin ƙasa 11,600 sq km, amma tana sayar wa ƙasashen waje iskar gas mai yawa, kuma ita ce ta shida a yawan kuɗin da 'yan ƙasa ke samu a duniya.

Gwamnatin ta zaɓi samar da zaman lafiya tsakanin ƙasashe, inda ta shiga tsakani wajen ƙulla yarjejeniyoyi da dama cikin shekara 20 da suka wuce a Gabas ta Tsakiya, da Turai, da Afirka.

Ƙatar ta taimaka wajen samar da yarjejeniyar da ta kai ga sakin wasu Isra'ilawa da Hamas ke garkuwa da su a watan Nuwamban 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙatar ta taimaka wajen samar da yarjejeniyar da ta kai ga sakin wasu Isra'ilawa da Hamas ke garkuwa da su a watan Nuwamban 2023

Ta karɓi baƙuncin tattaunawa tsakanin Hamas da Isra'ila domin tsagaita wuta ta ɗan lokaci a watan Nuwamban 2023, lokacin da aka saki Isra'ilawa 105 da 'yan gwagwarmaya ke garkuwa da su a madadin fursunonin Falasɗinawa 240.

A 2020, Ƙatar ta shirya tattaunawa tsakanin ƙungiyar Taliban da gwamnatin Amurka domin kawo ƙarshen yaƙin shekara 20 a Afghanistan. Hakan ta sa Amurkar da ƙawayenta na Yamma suka janye dakarunsu daga ƙasar kuma Taliban ta amshe mulkin ƙasar.

Haka nan, ta shiga tsakanin Amurka da Iran a 2023 - lokacin da Iran ta sako fursunoni Amurkawa a mdadin wasu kuɗaɗenta da aka riƙe.

A wannan shekarar, ta shiga tsakanin Rasha da Ukraine domin mayar da wasu yaran Ukraine gida bayan kwashe su zuwa Rashar a yaƙin da suke yi.

A 2020, Ƙatar ta samar da zaman lafiya tsakanin Chadi da ƙungiyoyi 40 na 'yan tawaye. Sai kuma a 2010, inda ta ƙulla yarjejeniya tsakanin gwamnatin Sudan da wasu 'yan bindiga a yammacin yankin Darfur.

Me ya sa Ƙatar ta rungumi aikin samar da zaman lafiya?

Ƙatar ta karɓi baƙuncin tattaunawa a 2020, wadda ta kawo ƙarshen yaƙin shekara 20 a Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙatar ta karɓi baƙuncin tattaunawa a 2020, wadda ta kawo ƙarshen yaƙin shekara 20 a Afghanistan
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙatar ta rattaba gudummawar ƙasar ta samar da zaman lafiya a kundin tsarin mulkinta.

Aya ta Bakwai ta kundin ta ce: "An gina manufofin ƙasashen na Ƙasar kan kyautata alaƙar zaman lafiya tsakanin ƙasashen duniya da tsaro ta hanyar ƙarfafa musu gwiwar sasanta rikice-rikice."

Ƙatar ba ƙawar Amurka ba ce kawai - inda Amurkar ke da dubban dakaru a sansanin sojin sama na Al Udeid - tana kuma ƙyale ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi kamar Taliban da Hamas su kafa ofisoshinsu a ƙasar.

Hakan yakan ba ta damar taka rawa a matsayin mai shiga tsakanin ɓangarorin da ba su magana da juna gaba da gaba, a cewar Dr H.A. Hellyer na cibiyar Royal United Services Institute da ke Birtaniya.

"Ƙatar na da cikakkiyar dama sosai ta yin magana da ƙungiyoyi kamar Taliban da Hamas, saboda ba su taɓa samun rikici a tsakaninsu ba," a cewarsa. "Kuma saboda dakarun Amurka a ƙasar, wakilansu ba su jin wata fargaba a Doha.

"Suna jin cewa za su iya yin tattaunawa cikin aminci ba tare da yunƙurin kashe su ba. Hakan wani shiri ne da ƙasar ke so a dinga yi mata kallon ƙwararriya kan sasanta matsaloli," in ji Dr Sanam Vakil ta cibiyar Chattam House ta Birtaniya.

"Kasancewar Ƙatar mai shiga tsakani abu ne mai amfani ga Amurka, kuma zai ba ta damar cusa kanta wajen ƙasashen Yamma. Kazalika, matsayin na jawo zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya."

Ƙatar na da tawagar jami'an difilomasiyya da suka ƙware wajen jagorantar tattaunawar zaman lafiya, a cewar Vakil. Sai dai, ta ce ba kodayaushe suke iya shawo kan masu yaƙi da juna ba a teburin tattaunawa.

"Mutanen Ƙatar na da ƙwarewa sosai wajen kawo ƙarshen rikice-rikice idan faɗan ya kai ƙololuwa kuma ɓangarorin na da niyyar tsagaita wuta," in ji ta. "Amma in ba haka ba ba za ta iya kawo ƙarshen yaƙin ba."

Me ya sa Ƙatar ke shan wuyar shiga tsakanin Isra'ila da Hamas?

Ma'aikatar Harkokin Wajen Ƙatar ta ce za ta dakatar da yunƙurinta na shiga tsakanin Isra'ilar da Hamas.

Sai dai ta musanta rahotonnin da ke cewa za ta rufe ofishin ƙungiyar a ƙasarta.

Isra'ila ta daɗe tana sukar Ƙatar da cewa ta fi goyon bayan Hamas, da kuma tallafa mata.

Amma Dr Hellyer ya ce: "Gwamnatin Ƙatar ce ta gayyaci shugabannin Hamas su mayar da ofishinsu can daga Damascus na Syria bayan sun ɓata da gwamnatin ƙasar a 2012. Sun yi hakan da sanin Amurka, ƙila har da Isra'ila."

Ya ce Ƙatar ta taimaka wa Isra'ila da Hamas cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙe-yaƙen baya, "amma a lokacin ɓangarorin biyu na da niyyar neman zaman lafiya".

"Wannan karon lamarin ya sha bamban," in ji Dr Vakil. "Gwamnatin Isra'ila na son ta kyautata tsaron ƙasar sama da zaman lafiya. Cigaba da yaƙin zai ba ta damar samun nasarar da ta ce tana nema. Hamas kuma na neman zaman lafiya don tsira da rayuwarta."

Ana raɗe-raɗin cewa Hamas za ta iya barin Ƙatar tare da komawa Turkiyya ko Iran.

Amma Dr Hellyer na ganin Ƙatar ta fi zama wuri mafi aminci ga shugabannin ƙungiyar, idan da za su ci gaba da zama a can ɗin.

"Lokacin da Ismail Haniyeh ya fita daga Doha zuwa Iran, Isra'ila ta kashe shi cikin sauri," a cewarsa.