Mai Roma Friedkin na son sayen Everton

Mai ƙungiyar Roma, Dan Friedkin ya zama ɗaya daga cikin waɗanda ke son sayen Everton, mai buga Premier League.

Ɗan kasar Amurka, wanda ake cewar yana da dukiyar da ta kai £4.8bn, na fatan ƙulla yarjejeniyar mallakar hannun jarin kaso 94 cikin 100 na Farhad Moshiri.

BBC Sport ta fahimci cewar MSP Sports Capital da wani ɗan kasuwa, Andy Bell da George Downing, wadanda suka rantawa Everton £158m, suma suna son sayen ƙungiyar.

Haka shima Michael Dell da babban jami'in Dell Technologies da kuma kamfanin zuba hannun jari na Kenneth King, suna cikin masu son mallakar Everton.

Haka John Textor, wanda yake da hadakar mallakar Crystal Palace ya nuna aniyar sayen Everton a watan jiya, mai neman wanda zai mallaki kasonsa na kashi 45 cikin 100 na ƙungiyar Selhurst Park.

Moshiri ya amince zai sayar da ƙungiyar ga wani kamfanin zuba hannun jari da 777 Partners a watan Satumba, amma cinikin bai yiwuba, inda wa'adin da aka gindaya ya kare a 31 ga watan Mayu.