La Liga na son Barcelona da Atletico Madrid su buga wasansu a Miami

Lokacin karatu: Minti 1

Hukumomin La Liga na son a buga wasan Barcelona da Atletico Madrid da aka tsara yi a watan Disamba a birnin Miami - amma idan Fifa ta amince.

Wannan zai zama karon farko da za a buga wasan La Liga a Amurka.

Hukumar kwallon ƙafa ta duniya Fifa ce za ta yanke hukunci na ƙarshe kan wannan buƙata.

An tsara buga wasan ne a ranar 22 ga watan Disamba, gabanin La Liga su ta fi hutun lokacin sanyi.

Daga Barcelona har Atletico na cikin ƙungiyoyi huɗu da aka tsara za su buga Super Cup na Spain a farkon watan Janairu, wanda ake buga a Saudiyya.

A watan Afrilu ne Fifa ta fice daga kalubalantar da aka yi mata da Relevent ya jagoranta, wanda ya nemi ta rika sanya idanu kan wasannin da ake yi a Amurka.

Watan da ya biyo baya Fifa ta sanar da kafa wani kwamiti da zai duba yadda za a riƙa haɗa wasanni a ƙasashen waje.

Shugaban gasar La Liga Javier Tebas ya bayyana buƙatarsa ta a riƙa ɗaukar wasannin La Liga zuwa wasu ƙasashen.

Barcelona ta so buga wasa da Girona a Miami a watan Janairun 2019, sai dai buƙatar ta fuskanci suka daga wasu a hukumar kwallon kafa ta La Liga da kuma ƙungiyar tsofaffin 'yan wasan Barcelona.

Wasu majiyoyi daga La Liga sun ce har yanzu akwai sauran aiki amma suna da kwarin gwiwar za su samu amincewar Fifa kan hakan.