Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Qatar 2022: Messi ya ci kwallo Argentina ta kai Quarter finals
Argentina ta doke Australia da ci 2-1 a wasan zagaye na biyu a Gasar Cin Kofin Duniya da Qatar ke karbar bakunci da suka kara ranar Asabar.
Lionel Messi ne ya fara cin kwallo a wasa na 1,000 da ya buga a tarihin taka leda tun daga Barcelona da Paris St Germain da Argentina.
Kwallo na 789 jumulla da ya ci a raga tun fara sana'arsa ta tamaula, kuma a wasa na 119 da ya yi wa tawagar Argentina.
Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu Argentina ta kara na biyu ta hannun Julian Alvarez.
Australia ta zare kwallo daya a minti na 77, bayan da Enzo Fernandez ya ci gida.
Ranar juma'a Netherlands za ta buga karawar daf da na kusa da na karshe da Argentina.
Ranar Asabar Netherlands ta kai zagayen Quarter finals, bayan da ta doke Amurka da ci 3-1.