Tinubu ba ya tsoron mahawara da sauran 'yan takara - Fani Kayode

Asalin hoton, TINUBU
Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Femi Fani Kayode ya ce Bola Tinubu ba ya jin tsoron shiga muhawara da sauran 'yan takara kai-tsaye a talabijin.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da dan takarar na APC bai amsa gayyata ko daya ba na shiga mahawara da kafafen yada labarai a Najeriya suka shirya.
A hirarsa da BBC Pidgin, Femi Fani Kayode ya ce "ya danganta da lokacin da aka shirya muhawarar. Tinubu ya fi kowane dan takarar shugaban kasa yin gamgamin yakin neman zabe."
'Bama jin tsoron Peter Obi'

Asalin hoton, PETER OBI-FACEBOOK
Femi Fani Kayode ya kara da cewa a yayin da ake shirin zabe a shekara mai zuwa, dan takarar jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ba ya ba su tsoro.
"APC ba ta da wani fargaba game da jam'iyyar Labour. Babbar abokiyar hamayarmu ita ce PDP," in ji shi.
Game da cewa tsohon sakataren gwamnatin Babachir David Lawal ya nuna goyon bayansa ga Peter Obi kuwa, FFK ya ce ba dole ba ne kowa ya amince da tsarin APC na tikitin musulmai zalla a takarar shugabancin Najeriya.
'Muna maraba da su Wike a jam'iyyar APC'

Asalin hoton, OTHER
Fani-Kayode wanda tsohon dan jam'iyyar PDP ne ya ce ya jinjina wa kungiyar Integrity ta su gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike kuma yana ba su kwarin gwiwa su ci gaba da abin da suke yi.
"Ina basu shawara su ci gaba da abin da suka sa a gaba saboda ba a yi masu adalci ba a cikin jam'iyyarsu," in ji shi.










