'Yan Faransa 11 da suka ci Kofin Duniya a Rasha za su je Qatar

Tawagar Faransa ce mai rike da Kofin Duniya, wanda ta lashe a Rasha a 2018, za kuma ta kare kofin a 2022 a Qatar.

Tawagar da ta bayyana 'yan wasan da za su wakilce ta a bana, sun hada da 11 da suka lashe mata kofin a Rasha shekara hudu baya.

Cikin gurbin da tawagar ta yi sauyi mai girma shi ne masu buga tsakiya, inda ba ko daya da ya buga wasannin Rasha.

Cikin wadanda koci, Didier Deschamps zai je Qatar a gurbin tsakiya ba su taba buga kofin duniya ba da suka hada da Tchuoameni da Nkunku da kuma Camavinga.

Jerin 'yan wasa 11 da suka buga wa Faransa Kofin Duniya a Rasha da za su buga wasannin Qatar

  • Hugo Lloris
  • Kylian Mbappe
  • Dembele
  • Pavard
  • Varane
  • Griezmann
  • Areola
  • Mandanda
  • Kimpembe
  • Lucas Hernandez
  • Giroud

Faransa za ta fara wasan farko a rukuni na hudu ranar 22 ga watan Nuwamba da Australia a rukunin da ya kunshi Denmark da kuma Tunisia.

Paul Pogba da N'Golo Kante da suka je Gasar da aka yi a Rasha, suna jinya ba za su buga fafatawar da za a yi a Qatar ba.

Jerin 'yan kwallon tawagar Faransa da za su buga Kofin Duniya a Qatar:

Masu tsaron raga: Alphonse Areola (West Ham), Hugo Lloris (Tottenham), Steve Mandanda (Rennes)

Masu tsaron baya: Lucas Hernandez (Bayern Munich), Theo Hernandez (AC Milan), Presnel Kimpembe (Paris St-Germain), Ibrahima Konate (Liverpool), Jules Kounde (Barcelona), Benjamin Pavard (Bayern Munich), William Saliba (Arsenal), Dayot Upamecano (Bayern Munich), Raphael Varane (Manchester United)

Masu buga tsakiya: Eduardo Camavinga (Real Madrid), Youssouf Fofana (Monaco), Matteo Guendouzi (Marseille), Adrien Rabiot (Juventus), Aurelien Tchouameni (Real Madrid), Jordan Veretout (Marseille)

Masu cin kwallaye: Karim Benzema (Real Madrid), Kingsley Coman (Bayern Munich), Ousmane Dembele (Barcelona), Olivier Giroud (AC Milan), Antoine Griezmann (Atletico Madrid), Kylian Mbappe (Paris St-Germain), Christopher Nkunku (RB Leipzig)