Wasu birane biyar da ambaliya ta binne su suka koma karkashin ruwa

A karkashin ruwa, akwai wasu ɓatattun birane da garuruwa a cikin duniyar nan, da ruwa ya shafe su.

Ba wai ana batun tsibiran tatsuniyoyi ba ne, a’a, akwai wasu wurare da a da suke cike da mutane, amma yanzu sauye-sauyen yanayin da ambaliyar tekuna sun sa dole garuruwan sun koma karkashin tekuna.

Ku zo ninkaya tare da BBC Bitesize domin gano wasu zane-zanen alatu masu kayatarwa da bakaken rubuce-rubucen mutanen da can da wasu dogayen mutum-mutumi da a can suka kasance a kan doron ƙasa.

Birnin Baiae, Italiya

Kayan alatu na tarihi da ke birnin na Baiae na fuskantar barazana daga dabbobin cikin ruwa da za su iya lalata su.

Asalin hoton, ANDREAS SOLARO

Bayanan hoto, Kayan alatu na tarihi da ke birnin na Baiae na fuskantar barazana daga dabbobin cikin ruwa da za su iya lalata su.

A da can birnin Baiae wani sashe ne na tsohon birnin mutanen Romans.

Birnin na Baiae ya yi fice ne da yanayi na musamman mai ɗumi, yanayi mai dadi da gine-gine na a-zo-a-gani.

Julius Caesar da Nero duk sun kasance suna zuwa domin shaawata a birnin, sannan kuma Sarki Hadrian ma a birnin ya rasu a shekara ta 138 Miladiya.

Sai dai wani abin takaici shi ne yadda zaizayar dutse wanda ya yi sanadiyar samar da wani fitaccen dumamar yanayi na ruwa, ya yi sanadiyar kawo karshen birnin na Baiae ya zama tarihi.

Asali birnin na sama da tsibirin Dutsen Campi Flegrei (Phelgraean Fields) wanda babbantsibirin dutse me mai aman iskar gas da wuta da ke kusa da birnin Naples.

Lokaci bayan lokaci, sai aka rika samun wani sauyin yanayi mai suna bradyseism, wanda a sanadiyar hakan birnin ya riƙa dulmuyewa karkashin kasa da mita shida, wanda hakan ya sa mafi yawan birnin ya kasance a karkashin ruwa.

Tun a shekarar 2002, hukumomi a yankin suka ayyana birnin na Baiae a matsayin yankin da ke karkashin kulawarsu, wanda hakan ke nufin sai masu ninkayan da aka ba lasisi ne kawai za su iya shiga tekun tare da jagorancin wani madugu daga yankin.

Thonis-Heracleion, Masar

Jan mutum-mutumin dutse wanda abin bautar wasu mutanen Masar ne Hapi, wadanda suke girmama ambaliyar Tekun Nile da masu ninkaya suka gano a shekara 2001

Asalin hoton, CHRIS J RATCLIFFE

Bayanan hoto, Jan mutum-mutumin dutse wanda abin bautar wasu mutanen Masar ne Hapi, wadanda suke girmama ambaliyar Tekun Nile da masu ninkaya suka gano a shekara 2001
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ana yawan ambaton wannan birnin a tarihin mutanen farko.

Birnin Thonis-Heracleion, birni ne da ake tunanin fitaccen gwarzon nan na Girka, (Hercules) ya fara ziyarta a Masar, haka kuma masoya Paris da Helen sun taba ziyartar birnin kafin Yakin Trojan.

Asalin sunan birnin shi ne Thonis, shi kuma Heracleion sunan Girka ne da aka kara domin girmama Heracles.

Birnin yana yammacin Kogin Nilu ne, kuma tashar jiragen sama ce babba da ake gudanar da harkoki sosai.

Kayayyakin da aka sayo daga kasashen da suke kewaye da tekun suna bi ta wannan tashar.

Gano bangarorin lalatattun jiragen ruwa guda 60 da sarƙunan rike jirgin ruwa guda 700 ne ya tabbatar da hakan.

Wani muhimman abun tarihi da aka gano a birnin na karkashin ruwa shi ne ‘Decree of Saïs’, wanda wani bakin rufin dutse ne mai tsawon mita biyu da ake kira stelae.

A jikinsa akwai alamar bakaken rubutun karni na 4 kafin Annabi Isa, wanda ke nuni da hanyoyin tara kudin shiga na Masar na wancan lokaci tare da tabbatar da cewa Thonis-Heracleion birni daya ne.

Derwent, Ingila

Kayataccen karfen kofar dakin taro na birnin Derwent ya bayyana a lokacin zafin shekarar 2018

Asalin hoton, ANTHONY DEVLIN

Bayanan hoto, Kayataccen karfen kofar dakin taro na birnin Derwent ya bayyana a lokacin zafin shekarar 2018

Da gangan aka nutsar da kauyen Derwent da ke yankin Derbyshire domin a samu ma’adanar ruwa ta Ladybower.

A daidai lokacin da birane irinsu Derby da Leiecster da Nottingham da Sheffield suke ta fadada a tsakanin karni na 20, karuwar mutanensu na bukatar ruwa mai yawa.

Domin samun haka, akwai bukatar a gina dam da kuma ma’adana.

Asali, an so ne a gina ma’adana guda biyu, Howden da Derwent a tsakanin tsaunuka masu ruwa a tsakaninsu domin a bar kauyen.

Amma sai aka gano cewa hakan ba zai wadatar ba.

Wannan ya sa ake bukatar ma’adana ta uku.

A shekarar 1933 aka fara aikin, sannan a shekarar 1945, birnin Derwent baki dayansa ya koma karkashin ruwa.

Idan lokacin tsananin zafi ya yi, ruwan ma’adanar ta Ladybower tana ja baya sosai ta yadda za a iya hango birnin na Derwent, inda baki na iya zuwa kallo.

Villa Epecuen, Ajantina

Wani wajen wanka da aka yi watsi da shi a Villa Epecuen

Asalin hoton, IVAN CASTRO

Bayanan hoto, Wani wajen wanka da aka yi watsi da shi a Villa Epecuen

Kusan shekara 25, wajen shakawata na Villa Epecuen yana boye a kasan ruwa kafin ya sake bayyana a shekarar 2009.

Tare aka assa birnin da na Salt Lake a shekarar 1920, kuma birnin na Lake Epecuen yana samun baki da dama da suke zuwa su yi wanka da ruwan cikinsa, wanda aka yi amanna yana maganin cututtuka.

Sai tekun ta kone bayan ta yi ambaliya da kanta, amma daga shekarar 1980 sai aka rika samun yawaitar ruwan sama na shekaru masu yawa wanda hakan ya sa tekun ya fara dagowa.

An gina masa bangon karfe ne domin karin kariya daga ambaliya.

Amma wata guguwa da aka yi a Nuwamban shekarar 1985 ce ta sa tekun ta yi ambaliya da har ta balla katangar sannan ta shafe birnin da nisan mita 10 a karkashin teku.

Sai dai ruwan yana ta dan ja kadan-kadan, wanda hakan ya sa ake samun ganin birnin na Villa Epecuen.

Port Royal, Jamaica

Yanzu birnin Port Royals ya zama wajen kamun kifi, amma a karni na 17, a daidai wannan yawan ruwansa na yanzu a wancan lokacin ana kiransa da “the wickedest city on Earth”, wato birnin da aka fi mugunta saboda masu ta’adin da suke da yawa a cikinsa.

Port Royal ya kasance birni mai matukar muhimmanci domin kasuwanci a duniyar wancan lokacin, ciki har da kasuwancin bayi, kuma birnin ya samu daukaka cikin sauri.

A shekarar 1662 akwai mutane 740, amma a shekarar 1692 an kiyasta samun mutane daga 6500 zuwa 10,000.

Suna zama ne a gidajen kasa ko na katako, wadanda yawancin benaye masu hawa hudu.

Da misalin minti 20 kafin rana ta fadi a ranar 7a ga watan Yuni ne aka yi wata zaizayar kasa mai karfi wadda ambaliyar tsunami ta biyo bayansa.

An kiyasta akalla biyu bisa ukun birnin ne ya nutse a ruwa inda ya faro daga rumbunan abinci ya shiga gari.

An ce kimanin mutum 2,000 suka mutu a ranar, sannan wasu da dama suka jikkata.

Ba laifi ba ne idan masu ninkaya sun shiga domin gano daruruwan jiragen ruwan da suka nutse, amma sai an nemi izini daga hukomomin yankin.

A Disamban shekarar 2021 aka wallafa wannan labarin.