'Yadda na yi ƙoƙarin ceto matuƙan jirgin da ya yi hatsari a Tanzania'

Majaliwa Jackson

Asalin hoton, Charles Mwebeya TBC

Masucin nan da ya kasance mutum na farko da ya kai agaji inda jirgi ya yi hatsari tare da kashe mutum 19 a Tafkin Victoria da ke Tanzania, ya bayyana yadda ya yi kokarin ceto ran matuƙan jirgin da kuma yadda ya kusa rasa ransa a kokarin wannan ceton.

Hadarin dai ya auku ne a ranar Lahadin karshen mako, kuma a lokacin da aka zanta da shi daga gadon asibiti a garin Bukoba, Majaliwa Jackson ya ce ya firgita lokacin da jirgin fasinjojin ya rikito daga wani bangare da ba hanyarsa ba ce, kafin ya fada cikin tafkin.

Cikin gaggawa ya doshi inda abin ya faru tare da wasu abokansa uku masunta, sun yi kokarin bude kofar jirgin ta hanyar amfani da sandar tuƙa kwale-kwale, hakan ya taimaka wajen ceto fasinjojin da ke zaune a kusa da kofar.

Mista Jackson ya ce daga nan sai ya koma gaban jirgin ta hanyar ninkaya a cikin ruwan.

Da shi da daya daga cikin matuƙan jirgin sun samu damar ganawa ta hanyar alamomi ta tagar jirgi.

"Ya bukaci na fasa tagar jirgin. Na shiga ruwa na yi ninƙaya zuwa wajen jami'an tsaron filin jirgi, da suka iso, na tambaye su ko suna da wani abu da zan iya amfani da shi na fasa tagar jirgin.

"Sai suka ba ni gatari, amma kuma sai wata sanarwar wani mutum da lasifikar isar da saƙo ya tsayar da ni komawa domin fasa tagar jirgin.

Ya ce suna cikin musayar bayanai da matukan jirgin kuma babu ta inda ruwa ke shiga cikin jirgin," a cewar Mista Jackson.

Ya ce bayan dakatar da shi "sai ya koma ya dagawa matukin jirgin hannu wato alamar salama da shi".

Amma kuma sai matukin jirgi ya nuna cewa yana bukatar taimako.

"Yana ta nuna kofar gaban jirgi da hannu. Kawai sai na yanke hukuncin komawa cikin ruwan na dauki igiya na daure a jikin kofar, sai muka yi kokarin jan jirgin da kwale-kwale, amma sai igiyar ta tsinke ta buge ni a fuska da sumar da ni.

Yanayi na gaba da na tsinci kaina shi ne a kan gadon asibiti," a cewar Mista Jackson.

Matukan jirgin biyu na cikin mutum 19 da aka tabbatar da mutuwarsu - a jirgin Precision na Tanzania, bayan hadarin.

Majaliwa Jackson

Asalin hoton, Charles Mwebeya TBC

Cikin fasinjoji 43 da jirgi ke dauke da su mutum 23 sun tsira, a cewar Precision Air.

An gudanar da jana'izar mutum 19 a fillin ƙwallo na Bukoba.

Firaministan Tanzania Kassim Majaliwa na cikin ɗaruruwan mutanen da suka halarci jana'izar.

Kafin wannan lokaci, ya ce za a gudanar da bincike mai zurfi domin gano musababbin hadarin.

Jirgin ya taso ne daga birnin Dar es Salaam a ranar Lahadi da niyyar sauka a Mwanza, kafin ya yi hadari da misalin 08:50 agogon kasar, a hanyarsa ta zuwa filin jirbin Bukoba.

An rufe fillim jirgin zuwa wani lokaci nan gaba.