Sai da na nemi shawarar Aguero kafin na tafi Man City - Echeverri

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan tsakiya na tawagar Argentina ta 'yan ƙasa da shekara 20, Claudio Echeverri ya ce sai da ya yi magana da tsohon tauraron ɗanwasan gaba na Manchester City Sergio Aguero kafin ya yarda ya je ƙungiyar ta Premier.
City ta sayi Echeverri a kan fam miliyan 12.5 daga River Plate a watan Janairun 2024 a yarjejeniyar shekara huɗu da rabi, amma kuma ta bar shi zaman aro a ƙungiyar ta Argentina har ya taso.
Ya shafe farkon 2025 a gasar 'yan ƙasa da shekara 20 ta Latin Amurka, inda ya yi wa tawagar ƙasarsa Argentina kyaftin suka zama na biyu a gasar.
Echeverri, mai shekara 19, shi ne ɗan Argentina na 12 da ya shiga Manchester City, kuma a yanzu zai iya fara taka leda a ƙungiyar kasancewar ya shiga tawagar ta Pep Guardiola.
"Na yi magana da [Sergio] Aguero, na san da alaƙar da ke tsakanin Argentina da Manchester City. Musamman ma Aguero, saboda ya fita daban," in ji Echeverri.
"Shi tsohon ɗanwasa ne da ya kafa tarihi a nan Manchester City saboda abubuwan da ya cimma da kuma kasancewarsa gwarzo."
Tsohon ɗanbayan Manchester City Martin Demichelis ne ya fara sa Echeverri a tawagar manya a karon farko a River Plate a watan Yuni na 2023.
Echeverri ya ci wa ƙungiyar ta birnin Buenos Aires ƙwallo huɗu a wasanni 48.










