Waiwaye: Zargin gwamnatin Najeriya da bai wa ƴanbindiga alawus da ɗaure Simon Ekpa a Finland

FB/Nasir El-Rufa'i Nuhu Ribadu

Asalin hoton, FB/Nasir El-Rufa'i & Nuhu Ribadu

Lokacin karatu: Minti 7

Sojin Najeriya sun ce sun kashe 'yan Boko Haram 12 a jihar Borno

Nigerian Army

Asalin hoton, Nigerian Army

A farkon ne sojojin Najeriya suka sanar da kashe mayaƙan Boko Haram 12 a wani samame da suka kai a yankuna da dama na jihar Borno, a cewar rundunar sojin ƙasar.

Gidan talabijin na gwamnatin ƙasar NTA ya ruwaito cewa dakarun rundunar Operation Hadin Kai ne suka halaka 'yanbindigar a ƙaramar hukumar Mafa mai nisan kilomita 59 daga Maiduguri babban birnin jihar.

Sun kai harin ne bayan samun bayanan sirri inda suka auka wa sansanonin mayaƙan a Tamsu Ngamdu, da Dalakaleri, da Gaza.

Cikin makamai da kayayyakin da suka ƙwace daga hannun 'yanbindigar har da bindigogi ƙirar AK-47 guda takwas, da ƙunshin harsasai takwas, da kuma ƙwayoyi.

An ƙone wata mata a Neja bisa zargin ɓatanci ga Annabi Muhammad

Haka kuma a farko-farkon ma mutanen garin Kasuwar-Garba da ke ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja suka ƙone wata mata da ranta a yammacin jiya Asabar bisa zarginta da ɓatanci ga Annabi Muhammad.

Matar, wadda ake kira da Amaye, tana sayar da abinci ne a yankin, inda jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani kwastomanta ya yi mata magana cikin raha cewa yana so zai aure, sai ya ambato maganar Annabin, ita kuma a nan ta faɗa wata magana ta zama ɓatancin.

An ce an fara miƙa ta ofishin ƴansanda ne domin a gudanar da bincike, amma sai mutane suka ci ƙarfin jami'an tsaron, suka ƙwace ta, sannan suka cinna mata wuta.

Shugaban ƙaramar hukumar Mariga, Abbas Adamu Kasuwar-Garba ya tabbatar aukuwar lamarin, inda ya ce komai ya lafa zuwa yanzu.

A nasa ɓangaren, kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya ce da misalin ƙarfe 2 na rana ne suka samu labarin cewa, "wata mata mai suna Amaye ta yi wasu kalaman ɓatanci ga Annabi."

Sai dai ya ce kafin su tura ƙarin jami'an tsaro, "mutane su kutsa inda suka fi ƙarfin jami'anmu, har suka ƙwace ta suka ƙone ta." in ji shi, inda ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike kuma da zarar sun kammala za su tabbatar da hukunci. a kan waɗanda aka samu da laifi.

Gwamnatin Sokoto ta ware wa kowane masallacin Juma'a naira 300,000 zuwa 500,000 duk wata

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani labarin da ya ɗauki hankali shi ne wanda gwamnatin jihar Sokota ta ce za ta fara ware wa masallatan Juma'a na jihar wasu kuɗaɗe duk wata domin gudanar da ayyukansu, sannan ta ce tana ware wa limaman masallatan da na'ibansu da ladanai alawus duk wata.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin jihar, Abubakar Bawa ya fitar, inda ya ce gwmnatin ta ɗauki wannan matakin ne domin haɓaka karatun Alƙu'ani da ilimin addini a tsakanin yaran jihar masu tasowa.

Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana haka a ranar Asabar a wajen yayen ɗalibai 111 da suka haddace Ƙur'ani a makarantar gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi da ke Sokoto, inda ya ƙara da cewa alawus ɗin zai taimaka wajen ba malaman addinin damar nazari da ci gaba da karantar da addini.

"Mun bayar da kwangilar sabunta masallatai 65 na Juma'a, kuma tuni an kammala guda 25, waɗanda a ciki mun buɗe guda 15 zuwa yanzu.

"Haka kuma mun kasafta ware wa masallatan na Juma'a kuɗi tsakanin naira 300,000 zuwa 500,000, ya gandanta. Sannan ga biyan limamai da na'ibai da ladanai na masallatan alawus suma domin samun sauƙin gudanar da ayyukansu," in ji shi.

Gwamnan ya ce kula da harkokin addinin musulunci na cikin manufofi 9 na gwamatinsa, "kuma shi ne mai matsayi na biyu bayan tsaro."

An yanke wa ɗan Najeriya Simon Ekpa hukuncin ɗaurin shekara 6 a Finland

Simon

Asalin hoton, Simon/X

A wani labarin daban, kotu a ƙasar Finland ta yanke wa ɗan Najeriya mai 'rajin ɓallewar ƙasar Biyafara', Simon Ekpa hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan yari bisa laifukan ta'addanci.

Kotun ta same shi da laifin ƙoƙarin harzuƙa jama'a da niyyar ta'addanci da kuma shiga cikin ayyukan ƙungiyar ta'addanci.

Kotun ta kuma same shi da laifukan zamba ta haraji da kuma karya doka wanda hakan ya sanya kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari.

Kotun ta bayyana cewa Ekpa ya yi ƙoƙarin ƙarfafa rajin ɓallewar yankin Biyafara a kudancin Najeriya ta haramtacciyar hanya tsakanin watan Agustan 2021 zuwa Nuwamban 2024.

Kotun ta ce ya yi amfani da kafafen sada zumunta domin samun shigewa gaba-gaba a wannan fafutika.

Ƙungiyar ƴan-awaren ta kuma samar da wasu ƙungiyoyi masu ɗaukar makami, waɗanda kotun ta bayyana a matsayin na ta'addanci.

A cewar hukuncin, Ekpa ne ya samar wa waɗannan ƙungiyoyin makamai da abubuwa masu fashewa da harsasai ta hanyar wasu mutanensa.

Haka kuma, an same shi da laifin amfani da kafafen sada zumuntarsa wajen ingiza mabiyansa su aikata laifuka a Najeriya.

Kotun ta ce ya dikata duk wadannan laifuka ne ya yin da yake zama a garin Lahti na ƙasar ta Finland, sai dai ya musanta zarge-zargen.

Hukuncin da kotun ta yanke ba shi ba ne na ƙarshe, wanda ake zargin zai iya ɗauka ƙara zuwa kotu ta gaba.

El-Rufai da gwamnati na cacar-baki kan sulhu da ƴanbindiga

Daga cikin manyan labarin da ya ɗauki akwai sabuwar cacar-baki da ta kunno kai tsakanin Nasir El-Rufa'i da gwamnatin tarayya bayan tsohon gwamnan ya caccaki gwamnatin tare da zargin ta da ta'azzara matsalolin tsaro ta hanyar "ƙarfafa ƴanbindiga" maimakon ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalar baki ɗaya a sassan ƙasar.

El-Rufai ya yi zarge-zargen a zantawarsa da tashar talabijin ta Channels a ranar Lahadi, inda ya ce gwamnatin na taimakon ƴanbindigar ta hanyar ba su maƙudan kuɗaɗe ta bayan fage.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya take ta bayyana nasarorin da ta ce tana samu a yaƙin da take yi da ƴanbindiga da sauran matsalolin tsaro a ƙasar.

Tinubu da APC ne ke dagula jam'iyyar hamayya - Tambuwal

Tambuwal

Asalin hoton, Facebook

Haka kuma a makon ne tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya zargi shugaban Najeriya Bola Tinubu da jam'iyyar APC mai mulki da dagula lamuran jam'iyyun hamayya a ƙasar.

Yayin wata hira da gidan Talbijin na Channels a ranar Juma'a, tsohon kakakin majalisar wakilan ƙasar, ya yi iƙirarin cewa da gangan Tinubu ke kitsa rikicn da jam'iyyun hamayya ke ciki.

Ɗanmajalisar dattawan - wanda ke cikin jam'iyyar ADC ta masu haɗaka - ya ce idan aka yi la'akari da abubuwan da ke faruwa a jam'iyyun hamayya a yanzu za a fahimci cewa da wata a ƙasa.

''Ba sai an faɗa maka ba, duk musan da kowa zai yi ciki kuwa har da Shugaba Bola Tinubu, cewa ba shi da hannu na ƙoƙarin ruguza jam'iyyun hamayya, ba gaskiya ba ne'', in Tambuwal.

Tsohon gwamnan na Sokoto ya ce ''ba zargi nake yi ba, suna da hannu a duka abubuwan da ke faruwa a jam'iyyun hamayya''.

A baya-bayan nan dai an ga yadda manyan jam'iyyun hamayyar ƙasar suka faɗa rikicin cikin gida, wani abu da masana ke gargaɗin zai jonyo musu mummunan koma-baya.

Tuni dai wasu ƴaƴan jam'iyyun hamayyar cikin kuwa har da gwamnoni da ƴan majalisar dokokin ƙasar suka fice daga jam'iyyun nasu tare da komawa APC mai mulki.

DSS ta shigar da jagororin ƙungiyar Ansuru ƙara kan zargin ta'addanci

ONSA

Asalin hoton, ONSA

Bana makonni ana jira, a makon ne dai hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya ta shigar da ƙarar jagororin ƙungiyar Ansaru biyu, bisa zarginsu da hannu a wasu hare-hare a Najeriya.

Makonni uku da suka gabata kenan bayan da hukumoin Najeriya suka sanar da kama mutanen biyu, waɗanda ake zargi da hannu a kitsa munanan hare-hare a faɗin ƙasar.

Mutunen biyu su ne Mahmud Usman, da aka fi sani da Abu Bara'a da aka bayyana a matsayin Sarkin Ansaru, tare da mataimakinsa, Mahmud Al-Nigeri, da aka fi sani da Malam Mamuda.

Hukumar ta DSS na tuhumarsu da laifukan da suka ƙunshi ta'addanci da da ɗaukar nauyin ayyukan ƙungiyar, da ɗaukar sabbin mambobi tare da shirya munanan hare-hare a faɗin Najeriya.

An dai zargi mutanen biyu da hannu a kitsa harin gidan yarin Kuje a watan Yulin 2022, inda fiye da fursunoni 600, ciki har da waɗanda ake zargi da kasancewa mayaƙan Boko Haram.

Wike ya gindaya wa PDP sababbin sharuɗa

A wani taro da wasu ƴan jam'iyyar PDP da ake ganin ƴan tsagin Ministan Abuja, Nyesom Wike ne sun gudanar a Abuja, sun fitar da wasu sharuɗa da suka ce a cika kafin babban taron jam'iyyar, wanda za a yi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamban bana a birnin Ibadan na jihar Oyo.

A wata sanarwa da suka fitar a yau Talata, mutanen waɗanda suka kira kansu da suna Eminent Leaders and Concerned Stakeholders of the PDP, sun ce sun amince da tsarin rabon muƙaman jam'iyyar, amma suka ce ba za su aminta da ƙara rarraba muƙaman ba zuwa jihohi, bayan rabon a tsakanin yankunan.

Haka kuma sun ce duk da sun amince a bar shugabancin jam'iyyar a arewa, suna so ne shugaban ya fito daga yankin arewa ta tsakiya.

Sauran sharuɗan su ne:

Sake zaɓen shugabannin jam'iyyar a Ebonyi da Anambra

Sake zaɓen shugabannin jam'iyyar na Kudo maso Gabas

Amincewa da sakamakon zaɓen shugabannin Kudu maso Kudu da aka yi a Calaba

Sake zaɓen shugabannin jam'iyyar na ƙananan hukumomin a Ekiti ba tare da ɓata lokaci ba

Sanarwar ta ƙara da cewa idan har aka yi adalci, jam'iyyar PDP za ta magance matsalolin da take fuskanta sannan ta dawo da ƙarfinta.