'Yan Afirka da suka maƙale a Lebanon: ‘Ina son komawa gida amma babu dama’

Masu aikatau ƴan Habasha sun taru a bakin ofishin jakandancin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu aikatau daga Habasha da dama sun rasa aikinsu bayan da Lebanon ta faɗa matsin tattalin arziki
    • Marubuci, Priya Sippy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, London
    • Marubuci, priya
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 5

Eulita Jerop, wata mai yin aikatau wadda ta fito daga Kenya ta kasance tana rayuwa a wajen birnin Beirut, babban birnin Lebanon a tsawon watanni 14 da suka gabata. A cikin makonni kalilan da suka wuce, tana cikin fargaba sakamakon ƙarar abubuwa da take ji waɗanda ba ta saba ji ba.

"Abin firgitarwa ne. An faɗa mana cewa ƙarar bama-bamai ne, amma ƙarar kamar ta jirage ne," in ji ta. "Amma ƙarar da karfin gaske."

Ƙarar da suka yi ta ji ta fito ne daga sararin samaniya sakamakon kara-kaina da jiragen yaƙi ke yi.

Isra'ila da Hezbollah dai na artabu da juna a kullum a faɗin iyaka tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai cikin Isra'ila. Hakan ya janyo zazzafan martani daga Isra'ila inda ta kai har ta mamaye Gaza, inda suka ce suna da zimmar kawar da Hamas.

Hezbollah, da ta kasance ƙungiyar gwagwarmaya ta siyasa wadda ke samun goyon bayan Iran da ke a Lebanon, ta ce tana kai wa Isra'ila hari ne domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa.

A makonnin baya-bayan nan, ana nuna fargaba kan yiwuwar yaɗuwar faɗa a yankin yayin da Hezbollah ta tabbatar da cewa an kashe wani babban kwamandan ta a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai Beirut ranar 31 ga watan Yuli.

Dakarun juyin-juya halin Iran sun ɗora laifin mutuwar shugaban Hamas Ismail Haniyeh kan Isra'ila. Sun sha alwashin mayar wa Isra'ila martani.

Rundunar kula da makaman atilari ta Isra'ila ta harba makamai a faɗin iyaka zuwa Lebanon

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rundunar kula da makaman atilari ta Isra'ila ta harba makamai a faɗin iyaka zuwa Lebanon

An gargaɗi ƴan ƙasashen waje da su fice

Game da halin da ake ciki a Lebanon, ƙasashe da dama ciki har da Amurka, Birtaniya, Australiya, Faransa da kuma Canada sun fitar da sanarwar gargaɗi a hukumace ta ofisohin jakadancinsu, inda suke gargaɗin ƴan ƙasashensu da su fice daga Lebanon ba tare da ɓata lokaci ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai samun ficewa daga Lebanon ba abu ne mai sauki ba ga wasu mutane.

Eulita, mai shekara 35, ta ce ƙasar ta zama wuri ga yawan masu zuwa neman aiki waɗanda kuma ke amfani da fasfo ɗin aiki da zarar sun isa.

Duk da samun fasfo, suna kuma buƙatar biza domin samun damar ficewa daga Lebanon - wanda har sai waɗanda suka ɗauke su aiki sun saka musu hannu.

Wannan na faruwa ne karkashin wani tsari mai suna 'kafala' wanda ke bai wa kamfanoni da mutanen da suka ɗauki ƴan waje aiki damar samun iko a kansu - inda aka kiyasta cewa akwai ma'aikata 250,000.

Ma'aikatan da aka ɗauka kuma ba su ƴanci mai yawa muddin suka samu aiki a can Lebanon.

Masu ɗaukar aiki na amfani da damar da suke da ita wajen bai wa mata aiki mai yawa wanda ya fi karfinsu, rashin biyansu da kuma cin zarafi.

Duk da kiraye-kirayen kawo sauyi, tsarin na ci gaba da wakana karkashin ƙasashen yankin Gulf.

Daniela Rovina, jami'ar yaɗa labaru a Hukumar Kula da Ƙaurar Jama'a ta duniya (IOM), ta faɗa BBC cewa abu ɗaya da yake kare ƴan ƙasa karkashin dokokin ƙasa da ƙasa shi ne "hakkin barin kowace ƙasa, ciki har da ƙasarsa ta haihuwa" da kuma ƴancin komawa ƙasar haihuwa.

Ta ƙara da cewa karkashin tanade-tanaden Yarjejeniyar Geneva kan ƴancin kare hakkin ɗan'adam, idan aka samu rikici a wata ƙasar da mutum ke zaune, to dokokin ƙasa da ƙasa za su yi aiki a wurin - abin da ke nufin za a bar fararen hula su fice kafin ko kuma lokacin rikici.

Zaman tankiya tsakanin Isra'ila da Hezbollah ta wanzu tsawon shekara 40, lokacin da Isra'ila ta mamaye kudancin Lebanon. Yaƙi na karshe da ya ɓarke tsakanin ɓangarorin biyu ya afku ne a 2006, lokacin da Hezbollah ta kai wani samame na kan iyaka.

Ga lamarin Eulita, waɗanda suka ɗauke ta aiki na son ta ci gaba da zama a Lebanon.

"Suna cewa yanayin da ake ciki a nan Lebanon ya kasance tsawon shekaru da yawa, kuma ba abun damuwa bane" in ji ta. "Amma gare mu al'amarin mai girma ne. Ba mu saba jin ƙarar tashin bama-bamai ba kamar yanzu."

"Ina son na koma gida," in ji Eulita.

Nan wani hari ta sama ne da Isra'ila ta kai kudancin Lebanon a garin Chihine a watan Yuli

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan wani hari ta sama ne da Isra'ila ta kai kudancin Lebanon a garin Chihine a watan Yuli

Tsadar tikitin jirgi

Sai dai duk da samun biza ko kuma muhimman takardu, Eulita tare da wasu abokan aikinta na fuskantar kalubale wajen barin Lebanon.

"Jirage kaɗan ne ke tashi kuma suna da tsadar gaske," in ji ta.

Tikitin jirgi zuwa Kenya na kai wa dala 1000, wanda ya yi matukar tsada ga marasa karfi.

Banchi Yimer, wadda ta kafa wata ƙungiya da ke taimakon ƴancin ƴan Habasha da ke aiki a waje, ta ce albashin da suke karɓa a wata bai fi dala 150 ba, sai dai tun bayan shiga halin matsin rayuwa a Lebanon "ba a biyan da yawa daga cikin masu aiki."

Wata mai yin aikatau mai suna Chiku wanda ta fito daga Kenya, wadda muka sauya sunanta domin kare lafiyarta, ta ce ba za ta iya biyan kuɗin jirgi ba saboda tsadarsa.

Ta ce tana zaune ne a birnin Baabda, da ke yammacin ƙasar, tsawon shekara ɗaya.

"Zan so na koma gida. Sai dai tikitin jirgi ya yi tsada," in ji ta.

Ta kasance tana zaune cikin fargaba a makonni da suka wuce, sai dai kamar Eulita, ita ma waɗanda suka ɗauke ta aiki sun ce ta zauna.

"Sun ce ba zan tafi ba saboda kwantiragina bai kare ba," in ji Chiku. "Amma shin wannan kwantiragi ya fi rayuwata muhimmanci ne?'

BBC ta tuntuɓi Ma'aikatar Kwadago ta ƙasar Lebanon domin mayar da martani ga wannan iƙirari sai dai ba ta uffan ba zuwa yanzu.

Gwamnatocin Afirka ‘shirye suke don kwashe’ mutanensu

Roseline Kathure Njogu, babbar sakatariya a sashen Kula da mazauna waje a Ma'aikatar Harkokin Wajen Kenya, ta faɗa wa BBC cewa sashen zai iya bayar da takardun tafiya na gaggawa ga waɗanda ba su da fasfo.

Ta ƙara da cewa akwai shirin kwashe mutane a ƙasa kuma gwamnatin Kenya sun samar da jiragen da za su yi aikin.

"Muna da ƴan Kenya aƙalla 26,000 a Lebanon, kuma mun yi wa 1,500 rajista domin fara kwashesu," in ji ta.

Ms. Ngoju ta ƙara da cewa akwai haramcin tafiya cirani zuwa Lebanon tun watan Satumban 2023, sakamakon korafe-korafe da ƴan ƙasashe suka yi kan tsarin na 'kafala'.

Mai magana da yawun gwamnatin Habasha, Nebiyu Tedla, ya faɗa wa BBC cewa suna "shirye-shiryen kwashe jami'an diflomasiyya da kuma ƴan ƙasar daga Lebanon idan ya zama dole."

Sai dai, Banchi Yimer wata mai aiki, ta ce tun kafin a fara rikici tsakanin Isra'ila da Gaza, akwai matan Habasha da yawa waɗanda suka maƙale a Lebanon da kuma suka matsu su fice daga Lebanon.

Karayar tattalin arziki da Lebanon ta faɗa a 2020 ya janyo masu aikatau daga Habasha rasa ayyukansu.

"Tattalin arzikin Lebanon na ci gaba da fuskantar kalubale musamman na rashin isassun kuɗaɗe, iftila'in annobar korona, da kuma fashewar wani abu a tashar jiragen ruwa. Hakan ya janyo masu aiki da dama rasa aikinsu. Da yawa daga cikinsu ba sa iya biyan kuɗin haya ko kuma na lafiya, musamman kuma kuɗin jirgi zuwa gida" in ji ta.

Yayin da ofisoshin jakadancin suka ci gaba da aiki domin kwashe ƴan ƙasashensu, mutane da yawa na jin kamar gwamnatocinsu sun wofantar da su.

Chiku da ta kasance mai aikatau daga Kenya, tuni ta fara tara kuɗi domin samun damar biyan kuɗin jirgi zuwa gida.

"Sai dai ya ga batun waɗanda ba za su iya biyan tikitin jirgi ba?" in ji ta.