Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ke sa mutum yin amai a mota yayin balaguro?
- Marubuci, Ghada Nassef
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 4
Wasu mutanen kan shiga damuwa da zarar sun san cewa za su yi balaguro a jirgi, ko mota, ko jirgin ƙasa.
Sai dai larurar tafiya kan daƙile duk wani jin daɗi da farin cikin balaguro kuma ta mayar da shirin yin hutu wani lokaci na baƙin ciki.
Larurar motsi na faruwa ne lokacin da ƙwaƙwalwa ta karɓi rikitattun saƙonni - tsakanin abin da idanimmu ke gani da kuma abin da jikinmu ya ji a lokacin da muke tsaye cak (kamar zaune a cikin mota) sai kuma ta fahimci aikin motsin da muke yi ba daidai ba.
Misali, idan muna zaune a cikin mota jikinmu na tsaye cak ba shi motsi amma kuma idanunnmu kan ga abubuwan da ke motsawa.
Masu fama da larurar motsi kan samu zaƙuwa, da jiri, da rashin jin daɗi.
Wasu mutanen kan ji abubuwa masu tsanani sosai da kan saka su haƙura da yin balaguron baki ɗaya.
Amma me ke haifar da larurar motsi kuma ta yaya ake maganinta?
Me ke haifar da larurar motsi?
Domin fahimtar dalilin da ke haifar da larurar motsi, zai yi kyau mu fahimci yadda ƙwaƙwalwarmu ke fahimtar saƙonnin da jikinmu ke aika musu.
Ƙwaƙwalwa kan karɓi saƙonni a kodayaushe daga kunnuwa, da tsokar jiki, da motsawar gaɓoɓin jiki, da kuma tsayuwarmu kanta.
Na'urorin ji na cikin jiki ne mafi muhimmanci. Suna cikin wani rukuni da ake kira vestibular system a Turance.
Rukunin ya ƙunshi wasu hanyoyi ƙanana da kuma wasu jakunkuna biyu, waɗanda ake kira saccule da utricle. Sukan aika bayanai game da motsin jiki da kuma inda wurin da mutum yake zuwa ƙwaƙwalwa.
Hanyoyin na ɗauke da ruwa da ke motsawa idan mutum ya motsa kansa. Sukan gane idan kan mutum ya motsa gaba ko baya, hagu ko dama.
Su kuma jakunkunan saccule da utricle suna aiki ne da yanayin da mutum ke ciki. Sukan faɗa wa ƙwaƙwalwa duk lokacin da mutum ya motsa gaba ko baya, gefe ko sama, ko ƙasa.
Amma idan idon mutum ya ga wani abu, sai kuma tsokar jikinsa ta ji wani abu daban, su ma kunnuwan cikin jiki su ji wani abu daban, daga nan kuma sai a aika wa ƙwaƙwalwa rikitaccen saƙo. Irin rikicewar ce ke haddasa larurar motsi.
Misali, idan mutum yana tuƙa mota, abubuwa za su dinga zuwa gaban idonsa yana gani kuma su dinga ɓacewa, abin da zai sa idon ya aika wa ƙwaƙwalwa saƙon cewa mutum yana motsawa ke nan.
Amma kuma kunnuwan cikin jiki, da lakar da ke cikin ɓargo da gaɓoɓi, za su ji cewa har yanzu a zaune mutum yake - ma'ana ba shi motsi - sai kuma saƙon ya rikice.
Haka nan, idan mutum yana cikin jirgin ruwa ko na sama, akasin haka zai iya faruwa: kunnuwan cikin jiki da tsokar jiki za su fahimci ana motsawa, amma kuma sararin ba zai sauya ba. Saboda haka sai wani ɓangare na jiki ya fahimci ana motsawa wani kuma ya ji ba wani motsi da ake yi.
Abin da hakan ke haifarwa su ne: murɗawar ciki, ciwon kai, da rashin jin daɗi baki ɗaya.
Waɗanne ne alamun larurar motsi?
Larurar motsi kan haifar da abubuwa da dama.
Akasari sukan fara ne a hankali kuma daga baya su girmama idan ba a daina motsin da ya haddasa su ba.
Alamomin sun ƙunshi:
- Jiri, jin ciwon kai, jujjuyawar kai
- Rashin jin daɗi a ciki
- Amai
- Ciwon kai
- Sauyawar fatar jiki
- Gumi
- Gajiya
Su wane ne suka fi fama da larurar?
Kowa zai iya kamuwa da wannan larura ta motsi, amma wasu sun fi shiga haɗari - kamar yara 'yan shekara biyu zuwa 12, mata masu ciki, da kuma masu larurar ciwon kai ta migraine.
Sai dai jarirai ba ruwansu da wannan larura. John Golding, farfesan nazarin tunanin ɗan'adam a Jami'ar Westminster da ke Landan, ya ce ba mamaki hakan na faruwa ne saboda ƙwaƙwalwarsu ba ta saba da karɓar saƙo daga idanunsu ba da kuma rawar da hakan ke takawa idan jiki ya motsa.
Haka nan aka gaji cutar. Kashi 65 cikin 100 na mutanen da ke fama da matsalar gadarta suka yi, a cewar Farfesa Golding.
Ta yaya za a rage girman matsalar?
Rigakafi har kullum ya fi magani.
Ga wasu abubuwa biyar da za su iya taimakawa wajen rage girman matsalar:
Kafin a fara balaguro:
- A guji cin abinci mai nauyi
- A rage yawan gahawar da ake sha ko kuma barasa
- A yi isasshen barci
Yayin balaguro:
- Zaɓi kujerar da za ku zauna a nutse: ku zauna a gaban mota, ko tsakiyar jirgin ruwa ko jirgin ƙasa, ku zaɓi inda za ku dinga leƙa taga
- Ku dinga leƙawa waje
- Ku guji yawan motsa kai
- Kada ku karanta wani abu, ko kallon fim ta waya ko kwamfuta
- Shagalar da kanku da wani aiki, kamar sauraron wani abu
- Ku rufe idanunku
- Ku sha ruwa da yawa
Citta
Wasu bincike da aka gudanar sun nuna cewa citta - idan aka sha ta a matsayin shayi ko a wani abu - za ta taimaka wajen rage jin amai da kuma jiri.
Farfesa Golding ya ce binciken sun sha bamban a wannan fuskar.
Ya ce idan citta na taimakawa to akwai yiwuwar "tana kwantar da 'ya'yan hanji ne. Saboda haka ba wai kare aukuwar larurar motsi take ba, kawai dai tallafa wa mutum take yi rage raɗaɗi".