Mai gyaran agogon da zamani ya mayar da shi mara sana'a

Asalin hoton, Ifiokabasi Ettang / BBC
- Marubuci, Mansur Abubakar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kaduna
- Lokacin karatu: Minti 5
Ƙarar bugawar agogo ce ta cika shagon gyaran agogon Bala Muhammad da ke kan wani titi a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Kamar wani magani ne cike da agogunan da suke maƙale a shagon da mabanbanta lokuta a maƙale a jikin bango, ga kuma wata ƙaramar kujerarsa da yake zama da ake turawa ƙarƙashin teburin da yake gyara a kai.
Shagonsa na kan wani babban titi mafi hada-hada a titinan Kaduna - yana tsakanin shagunan sayar da kayan gini.
Kafin yanzu, yana da tsayayyun abokan hulɗarsa da ke kawo masa gyaran agoguna ko kuma sauya batiran agogunansu.
"Akwai lokacin da a baya nakan samun aguguna sama da 100 da ake kawo mani gyara a rana ɗaya," kamar yadda dattijon mai shekara 68 ya bayyana, wanda aka fi sani da Baba Bala.
Amma yana fargabar kwarewarsa da ya samu daga wajen mahaifinsa da shi da ƙaninsa za ta tashi a kawai.
"Wata ranar babu mai kawo gyara," in ji shi, yaa kukan cewa mutane sun fi duba lokaci a wayoyinsu a yau, wani abu da yake neman durƙusar da sana'arsu.
"Waya da fasahar zamani na neman kawar da aikin da shi kaɗai na sani a duniya kuma kullum a fusace nake dalilin haka."
Sama da shekara 50 da agogo nake ciyar da iyalina.
"Na gina gida na ɗau nauyin karatu yarana duka daga wannan aiki na gyaran wayar," in ji shi.
This is what I love doing, I consider myself a doctor for sick wristwatches"
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mahaifinsa a baya yana tafiya kusan duka yammacin Africa sama da wata shida daga Senegal zwa Saliyo domin gyaran agogo kawai.
A wani lokaci a baya Baba Bala ya zauna a Abuja babba birnin Najeriya, inda nan masu hannu da shunin ƙasar ke rayuwa - inda ya samu damar gyara agogunan masu arziki da dama - kuma ya samu alheri.
Ya tuno lokacin da wasu manyan mutane da ke aiki a NNPC ne masu yawan kawo masa gyara.
Wasunsu na amfani da agogon Rolex - waɗanda suka banbanta ta fuskar farashi amma mafi ƙanƙantar farashi shi ne dalar Amurka 10,000 kwatan kwacin fan dubu 8,000 ko miliya 16 a kuɗin Najeriya.
A cewarsa agoguna ne masu kyau - kuma sun ƙara fito da soyayyar da yake yi wa agogunan ƙasar Switzerland. Shi da kansa yana sa Longines, wani nau'in agogon ƙasar Swiss - bacci n ke raba shi da agogon.
"Idan na fita daga gida na tuna ban fito da shi ba to sai na koma. Ba zai yiwu ba na fita ba shi - ka ji muhimmancinsa a wajena."
A cikin shagonsa ya maƙale wani ƙatoton hoton mahaifinsa - Abdullahi Bala Isa, an ɗauki hoton lokacin yana kan kujerarsa ta aiki shekaru gabanin rasuwarsa a 1988.

Asalin hoton, Ifiokabasi Ettang / BBC
Isah ya yi fice wajen gyara agogo a garuruwa da dama kamar Freetown da Dakar, sukan nemi ya j idan aka tara agoguna masu yawa da ake son gyarawa.
Yakan yawan zuwa birnin Ibadan da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya - garin da aka fara ƙirƙirar Jami'a a cikinsa.
Baba Bala ya ce babu wanda ya san a inda mahaifinsu ya koyi gyaran agogo ko a cikin dangi - amma ko shakka babu hakan ya faru ne lokacin tuan mulkin mallakar Burtaniya.
Saboda an haifi Baba Bala ne shekara huɗu gabanin baiwa Najeriya 'yanci a 1960.
"Babana ya yi fice kan harkokin gyaran agogonsa kuma an ɗauke shi wurare daban-daban domin gyaran. Ya koyan lokacin da nake yaro domin na bi sahunsa in na girma."
Lokacin da Baba Bala na shekara 10 ya fara gane tsinkayen da ke cikin agogo, dogon da gajeren da kuma yadda suke aiki - kuma ya ƙara riƙe sanar'ar da kyau ne lokacin da ya fara girma ya fara samun kuɗin kashewa.
"Lokacin da abokaina a sakandire ke kukan rashin kuɗi - ni ina da kudaden kashewa saboda ina aikin gyaran agogo."
Ya ba da labarin yadda kwarewarsa a wajen gyaran agogo ta burge ɗaya daga cikin malaman makarantarsu: " Ya samu matsala da agogunansa ya ta kai wa masu gyara amma ba su iya gyara masa. Lokacin da ya faɗan labarain a kwana guda na gyara masa su."
A wannan lokacin, ana ɗaukar agogog a matsayin wani ɓangare na kayan da ake sawa yau da kullum - mawuyacin abu ne ka ga babban mutum baya da ko ɗaya.

Asalin hoton, Ifiokabasi Ettang / BBC
A Kaduna akwai wuraren da aka keɓe da masu sayar da agogo da masu gyaransa suke.
"An ruguje wurin yanzu babu kowa a yankin," in ji Baba Bala ya faɗa cikin damuwa, yana cewa wasu daga cikin abokansa sun mutu ko kuma sun haƙura da kasuwancin.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka haƙura da sana'ar shi ne Isa Sani.
"Indai zan je shagona kullum hakan na nufin inje in zauna babu abin yi - shi ya sa na haƙura da zuwa tun 2019," in ji mutumin mai shekara 65.
"Ina da gona da yarana ke taimakan na noma - yanzu haka nake rayuwa a yanzu."
Cikin ɓacin rai ya ce: "Bana tsammanin gyaran agogo zai dawo ganiyarsa har abada."
Matasan da ke zama a wajen da ake sayar da gini sun amince da wannan zance.
Faisal Abdulkarim da Yusuf Yusha'u duka suna cikin shekarunsu na 18, kuma dukkansu babu mai agogo cikinsu.
"Zan iya duba lokaci a wayata a ko da yaushe nake buƙata," in ji ɗayansu.
Dr Umar Abdulmajid, wani malamain sadarwa a jami'ar Yusuf Maitama da ke Kano ya yi amannar abubuwa za su sauya.
"Agogo irin na baya da muka sani babu shi, kuma ba shakka masu gyaransa ma sun rasa aikinsu, amma irin agogo mai amfani da intanet na nan shi kuma.
"Baba Bala wanda ya komaKaduna daga Abuja domin ya buɗe shagonsa kimanin shekaru 20 baya, ya na so ya zauna gida kusa da iyalansa, sabon gyaran agogon ba zai brge shi ba.
"Wannan abun nake so yi sosai, ina kallon kaina a matsayin likitan agogon da ba shi da lafiya."

Asalin hoton, Ifiokabasi Ettang / BBC
"Wasu da dama sun kawo agogunansu har yanzu sun ki dawowa su karba," in ji Baba.
Amma Baba ya ƙi sarewa ga sana'arsa kuma kullum sai ya buɗe shagonsa - babbar 'yarsa da ke sayar da kayan sawa a gefe, takan saya masa katin waya idan kasuwa ta yi nauyi.
Yana jin dadin cewa ɗansa ɗan shekara 12 na son zama matuƙin jirgin sama - yana farin cikin cewa iyalansa na kallon duniyar ta wata fuskar ta daban.











