Ina aka kwana dangane da yarjejeniyar gyara dangantaka tsakanin ƙasashen Larabawa da Israila?

Shugaban Amurka Donald Trump tare da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Ministan Harkokin Wajen UAE Abdullah bin Zayed Al Nahyan da Ministan Harkokin Wajen Bahrain Abdullatif Al Zayani kafin sa hannu a yarjejeniyar Abraham

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump tare da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Ministan Harkokin Wajen UAE Abdullah bin Zayed Al Nahyan da Ministan Harkokin Wajen Bahrain Abdullatif Al Zayani kafin sa hannu a yarjejeniyar Abraham
Lokacin karatu: Minti 3

Yaushe Saudiyya za ta shiga yarjejeniyar Abraham?

A mujallar Amurka ta "Newsweek," an rubuta wata maƙala mai taken: Shin har yanzu yarjejeniyar Abraham na da tasiri? wanda wani editan mujallar Josh Hammer ya rubuta.

Hammer ya ce Trump bai ƙoƙari sosai ba wajen janyo Saudiyya ta shiga cikin yarjejeniyar ko dai a lokacin da ya ziyarci Riyadh a watan Mayu ko kuma a ziyarar Yariman Saudiyya zuwa fadar White House.

Bayan ƙasashen yankin Larabawa biyu Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Bahrain sun amince da shiga yarjejeniyar domin gyara alaƙar diflomasiyya da Isra'ila a 2020, sai hankali ya koma kan: yaushe Saudiyya - ƙasar Sunni mafi girma a yankin - za ta shiga cikin yarjejeniyar? kamar yadda marubucin ya rubuta.

A jawabin Hammer, Yariman Saudiyya bai mayar da hankali kan yarjejeniyar ba, inda ya alaƙanta amincewarsa da yarjejeniyar da kafa ƙasar Falasɗinu ƴantacciya, wanda ke da wahala a yanzu saboda ya saɓa da abin d gwamnatin Amurka ke so, kamar yadda Hammer ya bayyana.

Editan ya ce kamata ya yi Trump ya sanya buƙatar Saudiyya ta shiga yarjejeniyar a matsayin sharaɗin cika mata wasu abubuwa da take buƙata, "amma sai bai yi ba."

Wannan ya sa Hammer ya yi tambayar cewa: Anya gwamnatin Trump ta damu da faɗaɗa yarjejeniyar?

Sai dai Hammer yana ganin har yanzu akwai sauran lokaci, inda ya ce "Saudiyya ƙawa ce ga Amurka, don haka ya kamata mu riƙa miƙa buƙatu ne domin musaya da ita na wasu buƙatunta cikin sauƙi domin a taimaki jun."

Yunƙurin Trump

Donald Trump

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Donald Trump

Ita ma mujallar The Wall Street ta yi nazari kan matakan da Trump ya ɗauka a wata maƙala da ta ce: Shin Trump ya fara kawo sauyi? kamar yadda Karl Rove ya rubuta, wanda hadimin tsohon shugaban ƙasar George Bush ne.

Rove ya ce Trump ya yi ƙoƙari wajen ɗaukar matakai masu kyau game da takardun Epstein.

Tsohon hadimin ya yi nuni da yadda Trump ya amince da ƙudurin fitar da bayanan binciken Jeffrey Epstein, lamarin da ya bayyana da "mataki mai kyau."

Haka kuma Rove ya bayyana matakin rage haraji kan kayayyaki irin su coffee da ayaba, wanda ya ce lamari ne mai kyau ga Amurkawa.

Rove ya ce ƙarin haraji yana ɗaga farashin kayayyaki, sannan wasu kayyyakin ba a samar da su a cikin Amurka, ko kuma sun yi ƙaranci, inda ya ƙara da cewa akwai kayayyakin da ake shig da su da suka cancani a cire musu haraji baki ɗaya.

Mece ce yarjejeniyar Abraham?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yarjejeniyar Abraham wasu sharuɗɗa ne da aka tsara domin gyara dangantaka tsakanin Isra'ila da wasu ƙasashen Larabawa, wadda aka fara da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Bahrain.

An fara sanar da yarjejeniyar ce a watan Satumban shekarar 2020 a birnin Washington DC na Amurka, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Amurka Donald Trump.

Sannan da Trump ya koma mulkin Amurka a watan Yulin shekarar 2025, sai ya ƙuduri aniyar ƙara faɗaɗa yarjejeniyar zuwa wasu ƙasashen Larabawa irin su Syria da Lebanon da Saudiya.

A cikin tsarin, an bai wa Isra'ila damar shiryawa da dukkanin ƙasashen Larabawa kan sharaɗin za ta janye daga dukkan yankunan da ta mamaye da suka haɗa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza da Tuddan Golan da Labanon.

Tare da bai wa Falasɗinawa Gabashin Birnin Ƙudus a matsayin babban birninsu, da kuma samar da mafita ga ƴan gudun hijirar Falasɗinu, waɗanda yaƙin Larabawa da Isra'ila na shekarar 1948 zuwa 1949 ya shafa, da aka kora daga gidajensu inda a yanzun nan ce ake kira Isra'ila.

Da UAE da Bahrain da Jordan da Masar a yanzu duk sun gyara dangantakarsu ta diflomasiyya da Isra'ila ta hanyar cimma yarjejeniya.