Ko harajin Trump zai sa China, Japan, Koriya ta Kudu su hade kai?

Wata mace da ke aiki a masana'antar ƙera farantan zuƙar lantarki a China

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mace da ke aiki a masana'antar ƙera farantan zuƙar lantarki a China
    • Marubuci, Yuna Ku
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Korean, Seoul
  • Lokacin karatu: Minti 6

Yayin da Amurka ke ta'azzara yaƙin da kasuwanci tsakaninta da China ta hanyar saka tsattsauran haraji kan ƙawayenta kamar Koriya ta Kudu da Japan, yanzu ƙasashen arewa maso gabashin Asiya na shirin ci gaba da tattauna batun kasuwanci maras shinge na FTA.

A watan da ya gabata ne ministocin kasuwanci na ƙasashen suka gana a birnin Soul na Koriya ta Kudu a karon farko cikin shekara shida domin ci gaba da tattauna haɗakar kasuwancin.

Sun amince su yi aiki tare domin ƙulla yarjejeniyar kasuwancin ta free trade agreement (FTA).

Wata mace a wani bikin baje-kolin kayayyaki a China

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mace a wani bikin baje-kolin kayayyaki a China

Mece ce yarjejenyar FTA?

Yarjejeniyar FTA wani alƙawari da ƙasashe ke ƙullawa tsakaninsu, inda za su dinga yin hada-hadar kasuwanci tsakaninsu ba tare da karɓar haraji kan kayayyakin juna ba, ko kuma wani shinge.

Ya danganta da nau'in kayan, za a iya ƙin karɓar harajin kwata-kwata, ko kuma a rage shi sosai ƙasa da yadda ake karɓa a hannun sauran ƙasashe.

Wannan sabo yunƙurin ya jawo tayar da jijiyoyin wuya a Amurka. A makon da ya gabata (na 7 ga watan Afrilu), sanatan jam'iyyar Democrat Brian Schatz ya siffanta yunƙurin haɗewar China da Japan da Koriya ta Kudu a fannin kasuwanci da "abu mafi ban mamaki".

Sanatan jam'iyyar Democrat Brian Schatz ya ce yunƙurin dunƙulewar China da Japan da Koriya ta Kudu a fannin kasuwanci abu ne mai 'ban mamaki'

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sanatan jam'iyyar Democrat Brian Schatz ya ce yunƙurin dunƙulewar China da Japan da Koriya ta Kudu a fannin kasuwanci abu ne mai 'ban mamaki'

Idan ƙasashen uku suka yi nasarar ƙulla yarjejeniyar, zai sa su dinga juya tattalin arzikin da ya kai dala biliyan 24 - lissafi ƙiyasi ne game da yawan kayayyakin da ƙasashen ke samarwa daga cikin ƙasarsu.

Sai dai kuma, ba yanzu suka fara tattauna batun ba. Sun gaza ƙulla yarjejeniya duk da yunƙurin sama da shekara 10.

Yaushe China, Japan da Koriya ta Kudu suka fara maganar FTA?

An fara maganar kasuwanci maras shinge tsakanin ƙasashen uku tun 2012

Asalin hoton, AFP / Getty Images

Bayanan hoto, An fara maganar kasuwanci maras shinge tsakanin ƙasashen uku tun 2012

An fara maganar ce a 2012, lokacin da ministocin ƙasashne suka sanar da fara tattaunawa yayin taron ƙasashen nahiyar Asiya a babban birnin Cambodia Phnom Penh.

An fara tattaunawa a hukumance a birnin Seoul shekara ɗaya bayan haka, amma an ɗauki lokaci har zuwa karo na 16 a 2019 - karo na ƙarshe kenan da aka san da tattaunawar.

Wane rashin jituwa ne tsakanin China, Japan, da Koriya?

An gudanar da zanga-zangar ƙin jinin Japan a China lokacin rikicin siyasa game da rikicin Yaƙin Duniya na II

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An gudanar da zanga-zangar ƙin jinin Japan a China lokacin rikicin siyasa game da rikicin Yaƙin Duniya na II

Ban da maganar tattalin arziki, akwai rashin jituwa game da siyasa da kuma tarihi.

Yaƙi, da tilasta yin aikatau, da rikici kan iyaka, da alaƙa tsakanin Koriyoyi biyu, su ne masu kawo tarnaƙi.

Masu zanga-zangar goyon bayan 'yancin yankin Hong Kong kenan a Japan a watan Yulin 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zangar goyon bayan 'yancin yankin Hong Kong kenan a Japan a watan Yulin 2020

A 'yan shekarun nan, masu zanga-zanga a Koriya ta Kudu da Japan sun yi macin goyon bayan tsarin dimokuraɗiyya a Hong Kong.

Masu zanga-zangar nuna goyon baya ga yankin Hong Kong a Koriya ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zangar nuna goyon baya ga yankin Hong Kong a Koriya ta Kudu

Dr Heo Yoon farfesa ne kan kasuwanci tsakanin ƙasashen duniya a kwalejin Sogang Graduate School of International Studies, kuma yana ganin babu wata yiwuwar ƙulla wannan yarjejeniya.

Dr Yoon na ganin muradin China na ƙulla yarjejeniyar "siyasa ce kawai" don ɓata wa Amurka rai.

Ya ce lamarin ya yi kama da lokacin da China ta nemi a fara tattaunawa a 2012 game da yarjejeniyar Trans-Pacific Partnership (TPP) - wata yarjejeniyar kasuwanci tsakanin ƙasashe 12 da ke maƙwabtaka da Tekun Pacific wadda tsohon Shugaban Amurka Barak Obama ya jagoranta.

Wani ɗan gwagwarmaya a Koriya ta Kudu kenan yake zanga-zanga a 2001 kan Japan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani ɗan gwagwarmaya a Koriya ta Kudu kenan yake zanga-zanga a 2001 kan Japan

Shugaban Koriya na riƙo ya faɗa wa kafar yaɗa labarai ta CNN cewa "ba za mu yi haka ba" lokacin da aka tambaye su ko za su haɗa kai da sauran ƙasashe wajen yaƙar harajin da Amurka ta saka musu.

Amma kuma nan watan Yuni 'yan ƙasar za su yi sabon zaɓe bayan tsige shugaban ƙasar.

Wace yarjejeniya suke da ita tsakaninsu?

Dr Heo ya ce yarjejeniyar da ke tsakaninsu na da buƙatar a sake duba ta da kyau.

A yanzu babu wata yarjejeniya tsakanin Koriya da Japan, ko kuma tsakanin Japan da China.

"Duk lokacin da gwamnati ta fara maganar FTA tsakanin Koriya da Japan, sai ya zama lamari na siyasa, inda ake zargin goya wa Japan baya," a cewarsa.

China da Japan na da rikicin iyaka tsakaninsu game da wasu tsibirai - ana kiran su Senkaku a Japan, a China kuma ana kiran su Diaoyu.

Wace matsala za a iya samu?

Ana nuna damuwa game da muradan wasu manyan kamfanoni - ciki har da masu ƙera motoci, da ƙarafa, da ƙananan na'urori, da na makamashi.

Raymond Yeung, shugaban sashen tattalin arziki a bankin ANZ ya yi gargaɗi cewa yana ganin FTA ba lallai ta yi nasara ba.

"Ba za a iya ware yarjejeniyar kasuwanci daga siyasa ba. Japan da Koriya ta Kudu ƙawayen Amurka ne kuma sun dogara da taimakonta aɓangaren soji.

"Idan aka zo maganar kasuwar China ko ta Amurka, wacce kuke zaton za su ɗauka?"

China ta ƙaƙaba wa Amurka harajin kashi 125 cikin 100 na ramuwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, China ta ƙaƙaba wa Amurka harajin kashi 125 cikin 100 na ramuwa

Ta yaya za su iya cim ma yarjejeniya?

Har yanzu wasu masharhanta na da ƙwarin gwiwa.

Dr Kang In-soo na jami'ar Sookmyung Women's University da ke Koriya ta Kudu na ganin yanzu ne ya fi kamata a ƙulla yarjejeniyar.

"A baya, China na iya jin cewa ba ta shirya ba wajen buɗe kasuwanninta...Amma yanzu, China za ta so ta nuna kanta a matsayin jagorar kasuwanci ba tare da shinge ba da zimmar shatale Amurka."

Me ma'aikata ke tunani?

An ga rashin mai yawan gaske a 'yan makonnin nan a kasuwannin duniya saboda harajin da Trump ya saka - kafin kuma ya sauya shi.

To ta yaya ɗaiɗaikun ma'aikata ke kallon yunƙurin ƙulla kasuwanci maras shinge?

Mai shirya taruka Moon Tsui na ganin yarjejeniya ba lallai ta yi wani babban tasiri kan sana'arta ba

Asalin hoton, Moon Tsui

Bayanan hoto, Mai shirya taruka Moon Tsui na ganin yarjejeniya ba lallai ta yi wani babban tasiri kan sana'arta ba

Moon Tsui mai tsara taruka ce a ƙasashe ciki har da China da Japan da Koriya.

Ta ce yarjejeniyar za ta taimaka wa san'arta "na ɗan lokaci", amma ta yi watsi da tunanin cewa hakan zai kawo babban sauyi.

"Ina ganin kawai tunani ne na yunƙurin saka kasuwannin hannun jari su tashi kuma su sauko," kamar yadda ta shaida wa BBC. "Masu kuɗi ne kawai ke buga wasan...idan talaka ne kai lamarin ba zai shafe rayuwarka ba."

Wani ma'aikacin ɓangaren kudi a Hong Kong mai suna Charles na da ƙwarin gwiwa.

"Rage kuɗaɗen fito da na shigo da kayan aiki...zai jawo saukar farashi. A irin wannan lokaci da ake fama da hauhawar farashi a duniya, ba kawai masu samar da kayan za a taimaka ba, zai sa a ƙara yawan kayan da ake saya da kuma taimaka wa tattalin arziki."