Japan ta zama ƙasa ta farko da ta samu gurbi a gasar Kofin Duniya ta 2026

Asalin hoton, Getty Images
Japan ta zama ƙasa ta farko da ta samu gurbi a gasar Kofin Duniya ta 2026 bayan doke Bahrain 2-0 a wasan neman gurbi da suka buga a Saltama.
Ɗanwasan Crystal Palace Daichi Kamada da na Real Socieded Takefusa Kubo, su ne suka ci wa Japan ƙwallayen bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Ta samu gurbin ne duk da saura wasa uku a kammala wasannin rukunin na nahiyar Asiya.
Tuni ƙasashen Canada, da Mexico, da Amurka suka samu gurbi a gasar da aka faɗaɗa a matsayinsu na masu masaukan baƙi, amma kuma tawagar ta Samurai Blue ce ta farko da ta samu gurbi ta hanyar cin wasanni.
Gurbi takwas aka warewa ƙasashen nahiyar ta Asiya cikin 48 da za su nemi lashe kofin, akwai kuma ƙarin gurbi ɗaya da za su samu bayan wasannin neman cike gurbi.
Japan ƙarƙashin mai horarwa Hajime Moriyasu ta kai zagayen 'yan 16 a gasar da ta gabata a Qatar, inda Croatia ta doke ta a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Ta cinye wasanninta shida gaba ɗaya a zagaye na biyu na wasannin neman gurbin, sannan ba a doke ta ba a zagaye na uku, inda ta ci shida kuma ta yi canjaras ɗaya.






