Ƴan gudun hijirar Afirka da Asia da Amurka ta kora sun maƙale a Panama

    • Marubuci, Santiago Vanegas and Sheida Hooshmandi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 6

Sama da wata guda ke nan da aka kulle gwamman ƴan gudun hijira ƴan asalin Asia da Afrika a wani otel na alfarma, inda suke leƙe ta taga suna neman a taimaka musu.

An kwashe su ne daga Amurka zuwa babban birnin Panama, ƙasa mafi kasancewa a kudancin a tsakiyar Amurka, kuma sun rasa na yi, domin basu san yadda za su bar can ba.

Mutanen sun haɗa da maza, mata da yara daga ƙasashe kamar Iran, Afghanistan, Nepal, Pakistan, Somalia, Eritrea, Kamaru, Ethiopia, China, da Rasha, a cewar wata ƙungiyar addini, Fe y Alegría.

Ƙungiyar tana ɗaukar baƙuncin ƴangudun hijira 51 a babban birnin ƙasar ta Panama.

A cewar wasu alƙaluman da gwamnatin Panama ta fitar a baya-bayan nan, mutane 192 cikin 299 na ƴangudun hijirar da ba a yi musu rajista ba da aka kwaso daga Amurka, sun yarda a ƙashin kansu cewa suna so su koma ƙasashensu na asali.

Waɗanda suka zauna an basu izinin zama na wucin gadi na kwana 30, wanda za a iya da kwana 60. Amma bayan nan kuma za a fitar da su daga Panama.

BBC ta zanta da uku daga cikin ƴangudun hijirar, biyu daga Iran ɗaya kuma daga Afghanistan.

Kuma dukkaninsu sun ce komawa ƙasashensu na asali ba zaɓi ba ne a wurinsu.

"A shekarar 2022, na yanke shawarar sauya addini na na koma kiristanci. A iran hukuncin da za a yanke mini shi ne na kisa," Artemis Ghasemzadeh ta shaida wa BBC.

Gwamnatin Panama ta ce waɗanda basu da zaɓin komawa ƙasashensu, dole su samu wata ƙasar da zata karɓe su.

Sai dai waɗanda suka yi magana da BBC ba su samu inda za su koma ba.

Ya aka yi aka kai su Panama?

Artemis ta tsere daga Iran, bayan gwamnatin ƙasar ta gano cewa akwai wani coci da ke aiki a ɓoye, lamarin da ya kai aka kama abokanta biyu.

Ta shaida wa BBC cewa tun bayan kisan Mahsa Amini, wata matashiyar da aka kama kuma aka yi wa duka saboda bata san ya hijabi yadda ya kamata ba, ta fuskanci matsala a Iran saboda hijab."

Kafin ta isa Amurka, Artemis da farko ta je haɗaɗɗiyar daular Larabawa, sannan ta je Koriya ta Kudu sai Mexico.

Sun tsallaka cikin Amurka ba bisa ƙa'ida ba ta bakin iyakar Mexico ita da yayanta, suna fatan neman izinin samun mafaka.

A San Diego, California, jami'an da ke kula da bakin iyaka sun tsare ta.

An shaida mata tare da wasu gwamman ƴan gudun hijira cewa za a mayar da su Texas, amma sai aka kaisu birnin Panama.

Panama ta karɓi ƴn gudun hijira 299 kamar su Artemis a matsayin wani ɓangare na yarjejeniya da gwamnatin Trump.

BBC ta tuntuɓi gwamnatin Panama da na Amurka don samun cikakken bayani kan yarjejeniyar, amma ba ta samu amsa daga gare su ba.

Tun da fari an ajiye ƴan gudun hijirar ne a wani Otel na alfarma Decápolis na mako guda.

A wannan lokacin ministan tsaron Panama, Frank Ábrego ya ce ba tsare su aka yi ba "ana rike da su ne a wani wuri na wucin gadi domin kare su" a ƙarƙashin kulawar hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya.

Sai dai wani ɗan gudun hijira daga Afghanistan Hoh, ya ce

"a otel ɗin nan tamkar fursunoni muke."

"A bakin ƙofar ɗaki akwai jami'an tsaro, ƴansanda da jami'an shige da fice."

Wasu hotuna sun nuna yadda wasu da dama daga cikin ƴan gudun hijirar ke neman taimako ta tagogin otel ɗin.

Rahotanni sun bayyana cewa an hana su magana da kowa a waje kuma an hana su ganin lauyoyinsu.

"Waɗannan mutane ba tare da bin wata doka ba an mayar da su Panama ba tare da sun nemi mafaka ba, ba tare da an barsu sun ga lauyoyinsu ba kuma ba a barsu sun yi magana da kowa ba tsawon makonni," a cewar Juanita Goebertus, darakta a hukumar kare hakkin bil'adama na Americas.

Bayan mako guda gwamnatin Panama ta sanar da cewa mutane 171 a cikin ƴn gudun hijirar sun amince a ƙashin kansu su koma ƙasashensu na asali kuma Amurka zata biya ƙudaden sufurinsu.

Waɗanda kuma basu yarda ba za a mayar da su sansanin San Vincente da ke gundumar Darién, wanda ke bai wa ƴn gudun hijirar da ke ƙoƙarin zuwa Amurka wurin zama na wucin gadi.

Tafiyar sa'oi huɗu ne zuwa sansanin daga babban birnin Panama, wanda kuma ke kusa da wani ƙungurmin daji.

Hoh ba shi da masani kan wannan matakin a lokacin da ya shiga wata mota ƙirar bas a ƙofar otel Decápolis yana mai yin biyayya ga umarnin jami'an tsaro.

"Sun shaida mana cewa za su sauya mana otel ne, suka sanya mu a cikin bas, kuma bayan tafiyar sa'oi takwas a lokacin ne muka san cewa muna ƙungurmin dajin Darién," In ji shi.

Yanayi marasa kyau

Duka mutane ukun sun shaida wa BBC cewa yanayi a sansanin Darién ba shi da kyau, inda ba isasshen abinci da ruwan sha.

"Ina da ciwon suga kuma ba su bani magani na ba. Suga na ya tashi babu wanda zai taimake ni. Sun mai da ni kamar wani wanda ya aikata wani babban laifi ko kuma na aikata kisan gilla, a cewar Arsalan, wanda shi ma ɗan ƙasar Iran ne.

Hoh ya ce masu gadinsu na binsu duk inda suka je, har zuwa banɗaki.

A cewar gwamnatin Panama, hukumar ƴan gudun hijira ta duniya, da hukumar kula da ƴan gudun hijira na Majalisar Ɗinkin Duniya ne ke sa ido a kan ƴan gudun hijirar da ke cibiyar.

Kakakin hukumar ƴan gudun hijira ta duniya, ya shaida wa BBC cewa ba su da mutane a can.

Artemis ta shaidawa BBC cewa hukumomin majalisar ba su isa San Vicente sai bayan wasu kwanaki.

Daraktan hukumar kare hakkin bil'adama na Americas ya ce an tsare ƴn gudun hijirar a yanayin ƙunci ba tare da sanin ina za a kai su ba ko kuma yin abubuwan da hakinsu ne".

Sakaka

Ƴan gudun hijira sun kasance a sansanin na tsawon mako biyu, kafin gwamnatin Panama ta sanar da shirinta na sake su tare da basu izinin zama a ƙasar na kwana 30.

An kwashi ƴan gudun hijirar a motocin jami'an shige da fice na Panama a ƙarshen mako inda aka zube su a tashar shiga motocin bas da ke Albrook a birnin Panama.

Bayan isarsu, a cewar Artemis sun ji daɗin cewa an sake su, amma ba su san me zai faru da su ba.

"Ba za mu iya komawa ƙasashenmu na asali ba, mun kasa samun wata ƙasar, ba mu san me zai faru da mu ba," In ji Hoh.

Yanayinsu ya ƙara tsananta ne saboda basu da kuɗi kuma ba su iya magana da harshen Sifaniyanci ba.

Tun da farko shugaban ƙasar Panama, José Raúl Mulino ya ƙulla yarjejeniya da Amurka cewa Panama za ta zama ''zango'' ga ƴan ciranin Amurka ba masaukinsu ba.

Amma a yanzu tsarin ya sauya, kuma hukumomin Panama ne ke da iko kan abin da zai faru a nan gaba.

BBC ta tuntuɓi ma'aikatar tsaro da hukumar shige da ficen Panama do jin matakan da suke ɗauka domin kare ƴancin ƴan ciranin, amma ba mu samu amsa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.