Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙudurorin da ake taƙaddama a kai a daftarin zaman Lafiyar Gaza
- Marubuci, Tom Bennett
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Jerusalem
- Lokacin karatu: Minti 3
Masu shiga tsakani daga Isra'ila da Hamas na birnin Sharm El-Sheikh, Egypt, domin ganawar da ba ta kai-tsaye ba game da kawo karshen yaƙin Gaza.
Wannan ne karo na farko da wakilan ɓangarorin biyu suka kusanci juna tun bayan fara yaƙin shekara biyu da suka gabata.
To amma daftarin zaman lafiya da Donald Trump ya gabatar ya sanya wakilan ɓangaroroin kusantar juna domin tattauna.
Tuni dai Isra'ila ta amince da daftarin yayin da Hamas ta amince da wani ɓangare na daftarin mai ƙudurori 20.
Har yanzu dai akwai wasu manyan al'amura da duka ɓangarori hudu da ake takaddama a kansu.
Tsarin sakin Isra'ilawan ake garkuwa da su
Daftarin Trump ya yi tanadin cewa cikin sa'o'i 72 da amincewa da daftarin Hamas za ta saki duka Isra'ilawan da take garkuwa da su.
Ana tunanin cewa akwai kimanin Isra'ila 48 da har yanzu akew tsare da su a Gaza, waɗanda aka yi imanin 20 daga cikinsu na raye.
A ƙarshen mako Trump ya bayyana cewa za a saki Isra'ilawan ''nan ba da daɗewa ba'', yayin da Netanyahu ya ce za a sake su kafin ranar bikin ibadar Yahudawa da Sukkut, wato 13 ga watan Oktoba.
Ƙungiyar Hamas ta amince da ƙudirin sakin Isra'ilawan da ya ƙunshi musayar fursunoni, to amma ta ce sai an ''cika wasu sharuɗɗa''.
To sai dai waɗanda ake garkuwa da su ne kawai abin da ke Hamas za ta iya yarjejeniya a kansu - kuma ba a sani ba ko za ta yarda ta sake su kafin kammala cimma matsaya kan sauran sharuɗɗan yarjejeniyar.
Babu amana dai tsakanin ɓangaroin biyu.
A watan da ya gabata Isra'ila ta yi yunƙurin kisan tawagar masu shiga tsakani na Hamas, ta hanyar kai wani hari ta sama ta sama a birnin Doha, lamarin da ya fusata Trump da Qatar da manyan masu shiga tsakani.
Tawagar masu shiga tsakanin - ƙarkashin jagorancin Khalil a-Hayya, wanda aka kashe ɗansa a harin - a yanzu za ta gana da wakilan da isra'ila ta aika Masar.
Ƙwace makaman Hamas
Babban burin Isra'ila a tsawon wannan yaƙi shi ne wargaza ƙungiyar Hamas.
Netanyahu ya sha nanata cewa ba zai dakatar da yaƙin ba har sai an gama da ƙungiyar.
Wani babban kuduri cikin daftarin yarjejeniyar Trump shi ne ƙwace makaman Hamas.
To sai dai a baya hamas ta ki amincewa da ajiye makamanta, tana mai cewa za ta yi hakan ne kawai idan aka kafa ƙasar Falasɗinu.
A martaninta, Hamas ba ta ce komai ba kan batun ajiye makamanta - lamarin da ya sa aka yi ta yaɗa jita-jitar cewa ba ta sauya matsayarta ba.
A cikin ƙarshen mako, Netanyahu ya sha alawashin: ''Za a ƙwace makaman Hamas sannan a raba Gaza da masu gwagwarmaya da makamai - ko ana so ko ba a so''
Makomar gwamnatin Gaza
daftarin na Trump ya bayyana cewa babu rawar da Hamas za ta taka a makomar gwamnatin Gaza, wadda wasu ƙwararrun Falasɗinawa za su riƙe gwamnatin ta wucin gadi, ƙarƙashin kulawar ''kwamitin zaman lafiya'' na duniya da Trump zai jagoranta tare da tsohon Firaministan Birtaniya, Tony Blair.
Daga nan kuma za miƙa ragamar gwmanatin ga hukumar Falasɗinawa ta PA.
Kodayake Netanyahu ya amince da duka kudurorin daftarin 20 da Trump ya gabatar, ya nuna turjiya kan shigar da hukumar Falasɗinawa (PA), domin ko a makon da ya gabata lokacin da ya je Amurka ya dage cewa babu rawar da hukumar za ta taka a jagorancin yankin.
Wannan na ɗaya daga cikin ƙudurin da suka fuskanci suka tsakanin masu tsatauran ra'ayi a cikin gwamnatin hadaka ta Netanyahu - Da dama cikinsu na son ci gaba da riƙe ikon Gaza tare da gina matsugunan Yahudawa a yankin.
A martanin Hamas, ta nuna alamun sa ran samun rawar da za ta taka a Gaza a wani bangare na ''kafa kungiyar haɗin kan Falasɗinawa''.
Duk da cewa ƙungiyar ba su fayyace abin da kalaman nata ke nufi ba, ba alallai ne hakan ya samu amincewar Trump da Isra'ila ba.
Ficewar dakarun Isra'ila daga Gaza
Batun ficewar dakarun isra'ila daga Gaza shi ne abu na huɗu da ke taƙaddama a kansu.
Daftarin ya ƙunshi cewa sojojin isra'ila za su fice daga Gaza, "bisa ka'idoji da matakai, da kuma nasarorin da aka samu a lokacin" wanda dole duka ɓangarorin su amince da su.
Wata taswira da Fadar White House ta fitar ya nuna matakai uku na janyewar dakarun na Isra'ila.
A matakin farko kashi 55 na Gaza zai kasance ƙarƙashin ikon Isra'ila, a mataki na biyu za a rage kashi 40 cikin 100, yayin da a matsayi na uku za a rage kashi 15 kawai.
Mataki na karshe zai rage ''shinge tsaro'', ne kawai, wanda sojojin isra'ila za su ci gaba da ''kasancewa a wurin har sai an tabbatar da babu wata barazanar tsaro a yankin''.
Shi ma wannan na buƙatar cikakken bayani, saboda bai bayar da ƙayyadajjen lokacin da sojojin Isra'ila za su gama ficewa daga Gaza ba, wani abu da Hamas ke buƙatar karin haske a kai.
Daɗin daɗawa, taswirar da Fadar White House ta fitar ta saɓa wa wadda sojojin isra'ila suka fitar da ke nuna yankunan sojoji da kuma iyakokin Gaza da ak yi kuskuren zana su.