Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jirgin sama jannatin NASA na dab da cin karo da dutse a sararin samaniya
Nan da sa'o'i masu zuwa hukumar kula da sararin samaniyar Amurka NASA, ta ce jirgin sama jannati zai yi yi karo da dutse. NASA na son ganin kwakwaf, kan yadda za a iya dakatar da madaidaicin dutsen daga karo da duniya.
Ana wannan gwaji ne daga nisan kilomita miliyan 11 daga inda ake nufin isa mai suna Dimorphos.
Hukumar ta ce a yanzu dutsen bai tunkari fadowa duniya ba, sannan gwajin ba zai sanya ya nufi inda bil adam suke ba.
An yi kiyasin, daga karfe 11 da miniti 14 na dare Litinin. Abin hangen nesa zai iya ganowa daga inda aka hango, ciki har da sabuwar hukumar da ke bibiyar harkokin sararin samaniya ta intanet mai suna James Wbb.
Mun ga yadda masu shirya fina-finan Hollywood ke yin nasu, ta hanyar amfani da manyan makaman nukiliya da 'yan sama jannati. Amma abin tambayar shi ne, a zahiri, ta yaya za a kare duniya daga irin wannan dutse?
Hukumar Nasa na kokarin gano hakan. Abin da ta ke son yin gwajin da shi, shi ne ta sanya su yi karo da juna tare da jirgin sama jannati.
Za ayi gwajin jirgin samma jannatin, ta amfani da wannan dabara da kokarin zuwa gab da yin karo da dutsen daga fadin mita 160, wanda ke nisan kilomita 20,000 cikin sa'a guda.
Wanna ka iya sauyawa daga ainahin yadda jiragen sama jannati suka gudanar da harkokinsu a baya, a yanzu za su fadada hakan, inda za su dinga bata sakamako a kowanne minti guda.
Nasa ta yi alkawarin yada hotunan daga nisan kilogiram 570 da zarar dutsen ya yi karo da jirgin sama jannatiun.
"Dart shi ne irinsa na farko cikin jiragen sama jannati da zai yi wannan aiki da dauko hotunan abin da ya ke nan da zarar sun faru, ya yin da ya ke jujjyawa, ta nan zai ci gaba da kusantar inda ake bukata,'' in ji Dakta Nancy Chabot mai bincike a jami'ar Johns Hopkins, wadda ke jagorantar aikin Nasa a halin yanzu.
"Wadannan na daga cikin abubuwan da muke bukatar yi, aikin da akan dauki shekaru ana bincike, amma wannan zai sauya yadda duniya ke tafiya ta yadda jiragen sama jannati za su yi aikin, tare da yin karo da dutsen," a hirarta da BBC.
Karo da shi ne babban kalubalen. A mintina 50 na karshe ko sama da hakan sannan zai iya kai wa inda ake bukatar ya tunkara daga fadin mita 780.
Wata fasaha da aka sanya za ta yi gaggawar angiza jirgin sama jannatin yadda zai yi karo kai tsaye da dutsen.
"Baboda tsabar gudun da ya ke yi, da kuma nisan da ke tsakani, babu tabbacin ko akwai matuki a kasa da zai dinga sarrafa shi," in ji Dakta Tom Statler, masanin kimiyya a hukumar Nasa.
"Dole ta sanya muka kirkiri wata manhaja da za ta iya samun hotunn da zarar an dauke su, tare da tantance inda ya kamata a maida hankali akai, da kuma gaggawar gyara kuskure cikin wani salo mai ban mamki, da kuma tabbatar da saita komai inda ake son ya fada."
Wata na'ura da aka harba, ita ke da alhakin dawo da hotunan da aka dauka daga sararin samaniya zuwa duniya, kuma cikin sakan guda za ta dinga motsawa.
Abu na farko da za a fara gani shi ne wani dan digo mai haske a jikin hoton, a hankali za su dinga fadada, sai kuma su dauke, kafin hakan wani haske kan bayyana, sai kuma ya yanke wani bangare da ya gurbata.
Abin damuwa, ba wai an gama ba ne. Na'urar daukjar hoton 'yar Italiya ta na da dauyin kilogiram 14, da aka sake su kwanakin da suka gabata. Aikinta shi ne shi ne nadar duk abin da ya faru da wanda ya shiga waccan na'urar.
Za a dawo da hotunan da aka dauka daga nisan kilomita 50, zuwa duniyarmu cikin kwanakin da za su biyo baya,'' in ji Simone Pirrotta na hukuamr sararin samaniyar Italiya ASI.
A yanzu, na'urar na daukar awa 11 da minti 55 kafin ta gama kewayawa. Aana sa ran za a ga tasirin hakan n dan lokaci, sai kuma na dindindin na awa 11 da minti 45. Awon da za a yi da na'urar hangen nesa za ta tabbatar da hakan nan da makonni masu zuwa.
Wani bincike da aka gudanar na sararin samaniya hadi da na kimiyya, ya yi hasashen an gano kashi 95 yadda jirgin sama jannatin ke dauka da ka iya kan hasashen yadda karonsu da dutsen zai kasance.
Daga yanzu zuwa shekaru hudu masu zuwa, hukumar sararin samaniya ta Turai ESA, za ta tattara abin da ake kira Hera Mision, da zai kara fadada bincike da nazari kan abin da aka samu yanzu.