Ko an samu ci gaba a Zimbabwe bayan rasuwar Mugabe?

Asalin hoton, AFP
Fargaba ce ta lulluɓe zukatan al'umma, shekara biyar bayan tuntsurar da gwamnatin tsohon shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe.
Yayin da ƙasar ta kai wannan mataki, kaɗan ne daga cikin al'umma za su iya buɗe baki su yi tsokaci kan ko gwamnatin da ta karɓi mulki ta cika alƙawuranta na kawo sauyi a ɓangaren inganta rayuwar al'umma ko kuma kare haƙƙoƙinsu.
"Ta kaina kawai nake yi," in ji wani mai talla, a bakin titi wanda bai so a bayyana sunansa ba, kamar yadda ya shaida wa BBC.
"Waɗanda suke yawan magana - wasu suna tsintar kansu ne a gidan yari. Saboda haka ina barin komai ne a zuciyata, ina neman abin da zan sa a bakin salati."
Sauyin da aka samu ƙalilan ne tun bayan kifar da gwamnatin Robert Mugabe. Lauyoyi masu kare haƙƙin bil adama sun ce mutane gama-gari da ma masu suka da dama ne aka kama bisa zargin sun zagi shugaban ƙasa.
Tendai (ba sunan gaskiya ba) yana sayar da kayan masarufi a cikin motarsa - kamar garin sabulu, da turare, da man girki da kayan maƙulashe. Duk da cewar ya kammala jami'a, inda ya karanta fannin kasuwanci da kula da ma'aikata, ya ce sayar da kaya a bakin titi ne kaɗai hanyar da zai ɗauki nauyin kansa saboda babu ayyukan yi.
Ya ƙara da cewa "Abubuwa na nan yadda suke, ko ma a ce sun ƙara lalacewa bayan tafiyar Robert Mugabe. Duk da cewa abin da kamar wuya, ina sa ran abubuwa za su gyaru a nan gaba.”
Hauhawar farashi ya ninninka zuwa kashi 268 cikin ɗari - sama sosai fiye da lokacin da Mugabe ya bar mulki, kamar yadda alƙaluma suka nuna. Haka nan yawan mutanen ƙasar da ke cikin ƙangin talauci ya kusa ninkawa - daga kashi 30% zuwa kashi 50% a lokacin annobar korona, a cewar bankin duniya.
Wannan ya sa mutane sun tagayyara.
Wata mata na sayar da ɗanyen nama a robobi, daga cikin motarta, mutane na zuwa a ƙafa suna saye kaɗan-kaɗan, har na ƙasa sa dala ɗaya.

Asalin hoton, AFP
"Suna tsammanin cewa idan ya tafi za su rinƙa yin kalaci da burodi da ƙwai da shayin da ya ji madara a kullum - to amma ba abin da ake gani ba ke nan."
Yabo da alƙawura
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hanyoyin Harare, babban birnin ƙasar sun cika da murna a lokacin da Mugabe ya ajiye mulki ranar 21 ga watan Nuwamban 2017.
Mako ɗaya bayan haka tankokin yaƙi suka mamaye hanyoyin birnin lokacin da sojoji suka karɓe iko da kafar yaɗa labaru ta ƙasar kuma suka yi wa shugaban mai shekara 93 ɗaurin talala a gidansa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Emmerson Mnangagwa shi ne ya zamo jarumi, wanda ya nuna wa Mugabe iyakarsa. Ya sha alwashin kawo ƙarshen siyasar gaba, da inganta tattalin arziƙin ƙasar da kuma gyara alaƙar ƙasar da ƙasashen yamma.
Sai dai wasu sun bayyana cewa Mnangagwa ya yi aiki na ƙut da ƙut da Mugabe a tsawon shekaru, kuma ya taka rawa sosasi a munanan laifukan da ake zargin Mugabe da tafkawa, saboda haka sun yi kokwanto game da cewar shi ne wanda zai kawo sauyi a ƙasar. Jam'iyyar Mugabe ta Zanu-PF ce ta ci gaba da jan ragamar ƙasar.
A lokacin wata tattaunawa ta intanet domin nazari kan ƙasar bayan juyin mulki, wata lauya kuma marubuciya Petina Gappah ta ce "na shiga gwamnati ne saboda ina son ƙasata, ba domin ina son juyin mulkin da aka yi ba."
Ma'aikatar harkokin waje ce ta ɗauke ta aiki a matsayin mai bayar da shawara kan sake ƙulla alaƙa da kasashen ƙetare, sai dai wata 18 ne kawai ta yi tana aikin. Ta ce ta bar aikin ne cike da baƙin ciki.

Asalin hoton, Getty Images
Ta ce "mun yi tunanin za a samu nasara - amma hakan ba ta faru ba." Ziyarar wata tawagar ungiyar asashe rainon Ingila ta Commonwealth a makon da ya gabata, domin duba yiwuwar sake shigar da Zimbabwe cikin ƙungiyar wani ci gaba ne tun bayan tafiyar Robert Mugabe.
A shekarar 2003 ne Zimbabwe ta fice daga ƙungiyar. Dama a shekarar 2002 an dakatar da ƙasar daga ƙungiyar bisa zargin ta da take haƙƙin bil'adama, ciki har da amfani da ƙarfi wurin ƙwace filayen noma daga turawa, da kuma cuzguna wa ƴan adawa.
Sake shigar da Zimbabwe cikin Commonwealth zai zamo wata nasara ga gwamnatin shugaba Mnangagwa, abin da zai nuna cewar an kawo ƙarshen taƙaddamar da ke tsakanin Zimbabwe da Birtaniya kan filayen noma.
Manyan harkokin kasuwanci
Sai dai manyan ƴan kasuwa sun ce an samu ci gaba. Arziƙin al'umma ya ƙaru daga dala biliyan 17.5 a 2017 zuwa dala biliyan 20.2 a bara. Kuari Matsheza, shi ne shugaban ƙungiyar masu kamfanoni na Zimbabwe, ya ce "wannan gwamnatin tana jin koke-koken ƴan kasuwa. Za su iya ƙara ƙoƙari, amma dai wannan gwamnatin ta fi ta baya."
Ya ce kamfanonin da aka rufe bayan zuwan gwamnatin mai ci ba su kai yawan waɗanda aka rufe ba lokacin mulkin Mugabe. Ya ƙara da cewa akwai sauyi a kan manufofin gwamnati da kuma yadda gwamnati ke tsoma baki kan farashin kayan masarufi idan aka kwatanta gwamnatocin biyu. Gwamnati ta ta janyo masu zuba jari na miliyoyin dalolli, musamman a ɓangaren haƙar ma'adanai. Kamfanin Zimplats zai zuba jarin dala biliyan 1.8 a cikin shekaru 10 masu zuwa bayan wata tattaunawa da gwamnati.
Sai dai duk waɗannan abubuwa ba su yi wani tasiri na a zo a gani ba wajen kawar da matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa.

Asalin hoton, AFP
Wane mataki gwamnati ke ɗauka?
"Yanzu haka kashi 50% na kuɗin da ƙasar ke samu na tafiya ne kan manyan ayyukan zuba jari - domin bunƙasa rayuka, dole ne gwamnati ta samar da abubuwan da za su taimaka wa tattalin arziƙi," in ji mai magana da yawun shugaban ƙasa Emeerson Mnangagwa.
Ya ƙara da cewa "Bankin Duniya ya ce an samu bunƙasar kudaɗen shiga na hannun al'umma. Ba mu kai inda muke so ba, amma muna aiki domin cimma nasara."
Amma Ranga Mberi, editan labaran kasuwanci na shafin Newzwire ya ce akwai sauran aiki a gaba. "Duk da ana magana kan ci gaba a ɓangaren haƙo ma'adanai, babban abin da ya fi damun al'umma shi ne mene ne ke shiga hannaun jama'a." "Tashin farashin kayan masarufi ne babbar matsalar."
"Babban abin da mutane ke son su gani shi ne yadda ci gaban zai bunƙasa abin da ke shiga hannunsu. Wannan ne babban ƙalubalen da ke gaban Mr Mnangagwa yayin da ake shiga shekarar 2023."











