Amsar muhimman tambayoyi biyar kan shekara biyu na yaƙin Ukraine

    • Marubuci, Kateryna Khinkulova and Victoria Prisedskaya
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Bayan shafe shekara biyu ana yaƙi a Ukraine, babu alamar kawo karshen rikicin nan kusa.

Ukraine da Rasha, ko manyan kawayenta daga kowane bangare, ba su ga wani dalili na sasantawa ba.

Ukraine da Rasha, ko manyan kawayensu, ba su ga wani dalili da fata na yarjejeniyar zaman lafiya ba.

Kyiv ta dage kan mayar da iyakokinta da kasashen duniya suka amince da su tare da fatattakar sojojin Rasha, yayin da Moscow ta tsaya tsayin daka kan cewa Ukraine ba halastacciyar ƙasa ba ce kuma za ta ci gaba da kokarinta har sai ta cimma burinta kan Ukraine.

Mun duba abin da ke faruwa a yanzu da kuma inda wannan rikici zai iya kaiwa nan gaba.

Wane ne ke cin nasara?

Ana ci gaba da gwabza kazamin fada, wanda ya janyo hasarar rayuka daga bangarorin biyu.

Har yanzu ana ci gaba da gwabza fada a filin daga, inda dubban dakaru ke fafatawa tun 2022.

A cikin 'yan watanni da cikar mamayar shekara biyu da suka wuce, Ukraine ta kori sojojin Rasha daga arewaci da kewayen babban birnin kasar, Kyiv.

Ta sake ƙwace yankuna masu yawa a gabas da kudu daga baya a waccan shekarar.

Duk da haka, sojojin Rasha yanzu sun samu wurin zama sosai kuma suna da kariya mai ƙarfi. 'Yan Ukraine sun ba da rahoton fuskantar kalubale tare da raguwar kayan yaki.

A tsakiyar watan Fabrairu, sojojin Ukraine sun janye daga Avdiivka, wani gari da ke gabas da aka gwabza kazamin fada.

Dakarun Rasha sun yi bikin wannan janyewar a matsayin gagarumar nasara, domin wurin da Avdiivka ke da shi zai iya saukaka mamaya mai zurfi.

Kyiv ta bayyana cewa an yi janyewar ne domin kare rayukan sojojinta, tare da amincewa da cewa an fi ƙarfin dakarunta kuma an fi su yawa.

Wannan ja da baya ya nuna mafi girman ribar da Rasha ta samu tun bayan kame Bakhmut a watan Mayun da ya gabata.

Amma Avdiivka yana da nisan kilomita 20 daga arewa maso yammacin Donetsk, wani birni na Ukraine da Rasha ta mamaye tun shekara ta 2014.

Duk da haka, wannan ƙaramin ci gaba na Rasha a halin yanzu ya gaza cimma burinta na farko a watan Fabrairun 2022, wanda masu wallafa bayanai kan ayyukan sojoji a intanet, suka raba tare da sake maimaita farfagandar gwamnati da nufin ƙwace babban birnin kasar, Kyiv a cikin kwana uku.

A halin yanzu, kusan kashi 18 cikin 100 na yankin Ukraine ya kasance ƙarƙashin mamayar Rasha, ciki har da yankin Crimea da aka mamaye a watan Maris na 2014 da kuma manyan sassan yankunan Donetsk da Luhansk da ke gabas da Rasha ta kwace jim kadan bayan haka.

Shin tallafin Ukraine na raguwa?

Ukraine ta samu gagarumin tallafi daga kawayenta na Yamma ta hanyar ba ta tankokin yaƙi, da bindigogi, da manyan makaman atilari, wadanda suka ƙara karfin tsaronta.

Sai dai a 'yan watannin nan an samu raguwar kwararar kayan agaji, lamarin da ya haifar da fargaba game da dorewar tallafin daga abokan kawance.

A Amurka, shirin bayar da tallafin dala biliyan 60 ya tsaya cak a Majalisa saboda rikicin siyasar cikin gida.

Akwai kuma damuwa a tsakanin magoya bayan Ukraine cewa taimakon da Amurka ke bayarwa na iya raguwa idan aka sake zaɓen Donald Trump a zaben shugaban kasa mai zuwa.

A cikin Tarayyar Turai, a ƙarshe an amince da shirin tallafin dala biliyan 54 a watan Fabrairu bayan tattaunawa mai zurfi, musamman da Hungary, wanda Firaministan, Viktor Orban, ya fito fili yana adawa da goyon bayan Ukraine kuma yana da kusanci da Putin.

Bugu da kari, Tarayyar Turai ta ƙuduri aniyar isar da rabin makaman atilare miliyan daya da ta yi niyyar bai wa Kyiv a karshen Maris 2024.

Rasha na samun tallafi daga makwabciyarta Belarus, wadda ta yi amfani da yankinta da sararin samaniyarta wajen shiga ƙasar Ukraine.

Yayin da Amurka da Tarayyar Turai ke zargin Iran da bai wa Rasha jiragen yaƙin Shaheed, Iran ta musanta wannan ikirari, inda ta ce wasu tsirarun jirage ne kawai ta amince ta bai wa Rasha kafin rikicin.

Jiragen sama marasa matuki (UAVs) sun yi tasiri wajen kai hari a Ukraine - a yakin da ake neman jirage marasa matuka daga bangarorin biyu saboda karfin da suke da shi na gujewa kariya ta iska.

Duk da takunkumin da kasashen Yamma suka kakaba mata, Rasha na ci gaba da sayar da man fetur da kayayyakin aikin soji.

Ba a tunanin kasar China tana bai wa kowane bangare makamai ba, tare da tsayawa tsaka tsaki a rikicin, yayin da take ci gaba da sayen mai na Rasha tare da Indiya.

Duka Rasha da Ukraine sun himmatu da ƙasashe masu tasowa ta hanyar ziyarar diflomasiyya a Afirka da Latin Amurka.

Ko manufofin Rasha sun sauya?

An yi imanin cewa har yanzu shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yana son daukacin ƙasar Ukraine.

A cikin wata hira da ya yi da mai gabatar da shirin tattaunawa na Amurka Tucker Carlson, shugaban na Rasha - ba tare da kalubalantarsa ​​ba - ya sake bayyana gurguwar ra'ayinsa kan tarihi da rikicin.

Ya dade yana jayayya, ba tare da bayar da kwakkwarar shaida ba, cewa fararen hula a Ukraine - musamman a yankin Donbas na gabacin - na bukatar kariyar Rasha.

Kafin yaƙin, Putin ya rubuta wata doguwar kasida wadda ta musanta wanzuwar Ukraine a matsayin kasa mai cin gashin kanta, inda ya bayyana cewa 'yan kasar Rasha da na Ukraine al'umma daya ne.

A cikin Disamba 2023, ya sake nanata manufofinsa na "aikin soji na musamman" na Rasha, ciki har da "kawar da ɗan tsarin gurguzu".

Har ila yau, yana neman "karkatar da soja" da kuma nuna rashin son zuciya a Ukraine, kuma yana ci gaba da yin kakkausar suka kan kungiyar Nato da ke fadada tasirinta zuwa gabas.

Ukraine, a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta, ba ta cikin kowace irin kawancen soji, amma tana da burin shiga Tarayyar Turai da karfafa alaƙa da kungiyar tsaro ta NATO, muradun da a yanzu ake ganin sun fi dacewa idan aka yi la'akari da yanayin da ake ciki.

Wadannan manufofin na da nufin ƙarfafa matsayin kasar Ukraine da kuma hana yin tasiri a ƙoƙarin farfado da Tarayyar Soviet ta kowace fuska.

Ta ya ya za a kawo ƙarshen yakin?

Ganin cewa babu wani bangare da ake ganin zai iya mika wuya, kuma da alama Putin zai ci gaba da zama a kan karagar mulki, hasashen manazarta na nuna cewa yaƙin zai iya ci gaba.

Cibiyar nazarin tsaro ta duniya Globsec, wadda ke tattara bayanai daga masana da yawa, ta yi hasashen yanayin da zai dore bayan 2025.

Cibiyar nazarin tsaro ta duniya Globsec, na tattara bayanai daga masana da yawa don tantance yiwuwar sakamako daban-daban.

Sakamokon na farko sun yi hasashen yanayin yaƙin zai iya ɗorewa har zuwa shekarar 2025 tare da asarar rayuka masu yawa daga bangarorin biyu kuma Ukraine na ci gaba da dogaro da kayan makamai daga abokan kawance.

Wani sakamakon da zai yiwu ya hada da yiwuwar tashe-tashen hankula a wasu yankuna, kamar Gabas ta Tsakiya da China-Taiwan, da Balkans.

A cikin wannan yanayin, Rasha na iya neman ta'azzara tashin hankali a wadannan yankuna.

Wasu yanayi guda biyu masu yiwuwa, wadanda ake ganin sun yi daidai da juna, ko dai Ukraine ta samu wani ci gaba na soji amma ba a cimma matsayar kawo karshen yakin ba - ko kuma goyon bayan da kawancen Ukraine ke da shi ya ragu sannan suka tura shi don cimma matsaya.

Sai dai har yanzu akwai rashin tabbas game da tasirin zaɓen shugaban ƙasar Amurka, da kuma yadda sauran yaƙe-yaƙe, musamman rikicin Isra'ila da Hamas, zai shafi fifiko da kawancen magoya bayan Ukraine da Rasha.

Shin yaƙin zai iya ƙara ruruwa?

A tsakiyar watan Fabrairu, shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, ya yi gargadi game da sanya wa Ukraine rashin wadata da makamai, yana mai gargadin cewa hakan zai amfani Rasha.

Da yake magana a wani taron tsaro na kasashen duniya a birnin Munich, Zelensky ya buƙaci ƙasashen yammacin duniya da su tunkari Putin, yana mai cewa rashin yin hakan zai haifar da mummunan sakamako ga kasashe da dama a shekaru masu zuwa.

A cewar cibiyar bincike ta Royal United Services Institute (RUSI), Rasha ta sake fasalin tattalin arzikinta da masana'antar tsaro yadda ya kamata don ba da fifiko kan samar da soji kuma tana shirye-shiryen tsawaita rikicin.

Gargadin baya-bayan nan daga ministan harkokin wajen Jamus da hukumomin bayanan sirri Estonia ya nuna fargabar cewa Rasha za ta iya kai wa wata ƙasa ta ƙungiyar tsaron NATO hari cikin shekaru goma masu zuwa.

Sakamakon haka, duka NATO da Tarayyar Turai suna haɓaka ƙoƙarin tsara shirye-shiryen su na gaba, suna mai da hankali kan haɓaka ƙarfin soja da shirya al'ummomi don ingantaccen yanayin duniya.